❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(к'уαυтα ∂αgα Aℓℓαн)❄️*
💥 **ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє**
💥💥
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💞*
*WATPADD:HAFNANCY*
💥💥💥
_*°•gaιѕυwar вan gιrмa agareĸυ yan ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo,ѕoyayyarĸυ agarenι вazaтa ғaѕѕarυ вa нaĸa ĸυмa вazana ιya ĸwanтanтaѕнι вa,ιna gaιda anтy нaυwa zarιa мaмan υѕwan,anтy ѕaιna ĸeмa ιna gaιdaĸι,мy ѕaнιвa jaмeelaн janaғ ĸeтa daвance acιĸιn хυvιyaтa,ιna ѕonĸι мaтυĸa,мy najaтee ĸeмa ιna yιnĸι over тawar,мy najaн ιna тayaĸι мυrnar ғara lιттaғιnĸι мaι ѕυna 'yarιмa ѕυнaιl',allaн yaѕanya мaѕa alвarqa,real мaι daмвυ ĸeмa ιna gaιdaĸι мy нaвιвιya,υммυ aвιden,мoм aғra,qυeen мeenalι,aυғana,ѕιѕ lιмcy,ĸaι ĸυna da yawa wallaнι,ĸυмa ιna мιĸa gaιѕυwar вan gιrмa agareĸυ,nagode da ѕoyayyarĸυ agarenι*_
_*noтe:This novel is juz a fiction & not a true life story*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{σnwαrd tσgєthєr}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
_*вιѕмιllaнιr raнмanιr raнιм*_
*page 1⃣ тo 3⃣*
_*✨Hiranandani hospital,vashi -A fortis hospital,mini sea shore road,Navi Mumbai,India🏨✨*_
_**Room 09**_
°•°•°•°•°°•°Wani d'an k'yakk'yawan k'aramin yarone wanda akalla bazai haura shek'aru bakwai kacal adoron k'asa ba na gani kwance saman gado irin ta marasa lafiya.Kallo d'aya zaka masa kasan cewar wannan yaron jinin larabawa ne sak,babu ta inda ya baro kamanninsa dasu,kamawa daga hancin kares,tsantsin suma,tsukakken baki,uwa-uba hasken fata,da de sauran abubuwan yanayi dasu Arab din duk yaron nan ya mallakesu duka.Oxygen therapy ce saye ah d'an kares din hancinsa wacce take matuk'ar taka rawa wajen isar da oxygen gas agareshi don ya samu issasshiyar numfashi.
Xaune gefensa kan wata kujerar zama ta masu jinya,mahaifiyarsa ce,her majesty'GIMBIYA NAJMIYYAH UMAR FAROUQ BAHAGO'.Itama din kallo d'aya zaka mata ka tabbatar da cewar wannan din cikakkiyar balarabiyace,kamanninsu da d'anta sak! iri d'aya kamar an tsaga k'ara an k'arya.K'yakk'yawar macece meh ji da ajinta,mulkinta da kuma wadatacciyar ilimin arabi da boko daya gama ratsata.
Akallo na biyu da zaka sake mata,zaka lura da tsantsar tashin hankalin da yake tattare da ita wanda ba komai ne ya haifar mata da hakan ba illa na ganin mafi soyuwar d'anta akwance,yana cikin yanayin rayuwa za'ace ko mutuwa,he has been in a coma for good one year now.Yana fama ne da 'Medulloblastoma cancerous brain tumor' (ciwon cancer ta k'wak'walwa).
Hannayenta duka biyun sarke suke cikin nasa,kuka take rerawa ahankali kuma cikin k'aramin sauti wanda idan ba kasa kunnuwa kayi ba,toh tabbas bazaka iya jin shesshek'arta ba,duk idanuwanta sun gama rinewa,fararen idanuwan da aka Santa dasu ada toh ayanxu sun dade da komawa pure hot red.
Dubanta takai kan dan yaron akaro na barkatai wanda yake fidda numfashi awahalce tare da taimakon artificial gas(oxygen gas).
Tace _*"please Aryaan my son you juz have to stand on your feet again,Aryaan don Allah ka tashi ciwon ya isa haka nan,shekararka kusan daya kenan kana cikin coma,pls son wake up I don't wana loose you for the second time again Aryaan.........yah Allah na rokeka ka baiwa dana lfy don darajar fiyayyen halitta annabi Muhammad (SAW)...,idan kuma bazai tashi ba toh Allah ina rokanka da kayi gaggawan kawo masa k'arshen wahalar nan"*_
Kuka ne yaci k'arfinta.Ikon Allah! akace cuta ba mutuwa bace,ayau kuma at this very moment Allah ya k'arbi addu'ar wannan baiwar Allahn wanda akullum bakinta baya gajiya da rokarwa danta lafiya awurin ubangiji,sae gashi ayau Allah sarki meh duka ya k'arbi addu'arta.Kadan da kadan taga ya soma bud'e idanuwansa.
Da k'arfi ta furta"My prince.......... "
Ta matsa kusa dashi tana meh xubda hawayen farin ciki,shi kuwa kallonta yake amma ya kasa shaidata,can ya soma lumshe idanuwa,alokaci daya kuma numfashinsa ya soma yin sama da k'asa.Da sauri ta fice daga dakin tana ihun k'iran doctor agigice,iya karfinta take ambaton"Doctor! Doctor!! Pls cum and save my child,he's dieing pls help him......... "
Abakin kofar dakin kuwa wasu manya-manyan dogarawa ne ma'abota ingarman jikkuna su biyu tsaye suna gadi,ganinta sukai ta fito hankali tashe tana ambatan sunan likita.
Da sauri suka duka alamun girmamawa suna fadin"Allah ya taimaki gimbiya,meke faruwa? "
Kota kansu bata bi don ahalin yanxu bata nasu take ba,burinta kawai taga Dr.Bature ko kuma Dr.Ramu wa'enda sune likitocin dan nata.Babu b'ata lokaci kuwa sae gashi ta dawo da Dr.Bature wanda se faman fada yakewa Nurses din dake biye dashi,akan meyasa zasu dunga nesa da patients,especially irin condition din prince,at any time yana iya farkawa sannan yayi yunkurin komawa kuma.su kuwa sae haquri suke ta bashi tare da fada masa uzururrukansu.Yace next time idan hakan ta sake faruwa toh tabbas suna iya rasa ayyukansu akan prince don haka su kula.
Suna shiga dakin suka ga wa'ennan dogarawan sun tasa prince gaba suna kallonsa Cike da tausayinsa.
Da karfi gimbiya tace"Maza ku fice kubawa mutane wuri meh zaku iya masa da kuka tasashi gaba kuna kallo?Oya get loss immediately..... " (ba haka take ba but akan ciwon danta ta koma masifaffiya akan kowa).Da hanxari suka sake duka mata alamun girmamawa kana suka fice sunawa prince addu'ar samun lfy kamar koda yaushe.
Hankalinta ta maida ga Dr.Bature wanda ya dan duka tare da sanya kunninsa daya adaidai saitin xuciyar prince yana meh son tabbatarwa kansa da koh yana numfashi or not,don kafin su iso tuni numfashinsa dake tayin sama da kasa ya tsaya cak!.Ya kasa gane komai,don haka se yayi amfani da stethoscope dinsa dake rataye saman wuyarsa.
"Doctor ya mutu ko? " haka yaji ta fada cikin muryar kuka.Be bata amsa ba seda ya tabbatar ya sami kwakkwaran information daga jikin stethoscope din.
Saukar da ajiyar xuciya yayi kana yace"Ranki ya dade prince is still alive,I guess yayi yunkurin dawowa cikin rayuwa ne as usual,se kuma kwakwalwarsa ta gaza daukar wannan shock din da aka kasa ganota harwa yau,yanxu maganar da nake miki ya sake komawa cikin coma,don haka se mu sake zaman jiran farfadowarsa kuma akaro na ba adadi........ "
Wani uban kuka ne ya kubce mata,tace"No my son don Allah ka tashi,Aryaan I can't juz afford to loose u for the second time again,Aryaan kaine rayuwata,kaine wanda idan na kalla yake tuna min da Yah Aryaan dina,so pls stand up......... "
Dr.Bature ya runtse idanuwansa kam,sosae yake tausayin wa'ennan bayin Allahn yadda lokaci daya suka sukurkuce suka lalace akan lalurar dansu wanda shi karan kansa besan inda yake ba harna tsawon shekara guda daya kenan.
Ahankali ya bude idanuwansa yace"Gimbiya haquri zamuyi duka mu kuma dage da du'a'i,cuta sam ba mutuwa bace,insha Allahu prince ze tashi lafiya lau nan bada jimawa ba,wai ni ina meh martaba ya shige ne?kodai har ya tafi airport dinne? "
Murmushin takaici ta sakar kana tace"Eh wallahi ina jin mah yanxu basu isa airport din ba don basu wani jima da tafiya ba,ina aza ai ya fada maka ne kafin ya wuce? "
"Ya fada min amma dayake dazun ina dakin theatre ne shiyasa ban san lokacin daya wuce ba,amma kafin na shiga munyi sallama.... "
Cike da jimami ya sake cewa"Allah sarki hajiyarmu lokaci yayi,ta rigamu xuwa gidan gaskia,Allah ya rahamasheta,muma idan tamu cikawar tazo yah Allah kasa mu cika da k'yau da imani... "
"Ameen don darajar ma'aiki.... " ta fada tare da sanya bayan hannu tana share hawayen daya dan ziraro mata.
Yace"Idan mai martaba ya dawo akwai maganar da nakeson ganawa dashi relating to little prince health.... "
Gabanta ne taji ya bada rasss!,tace"Dr.Bature lafiya dai ko?"
Dan muskutawa yayi yace"No ba wani abu bane ranki ya dade,kai actually mah maganata ne dashi,so juz frgt Idan ya dawo mayi magana.. "
"Haba Doctor nima din fa parent ce,am his biological mother,so don meh zaka boyemin wani abin sannan kace seda mahaifinsa Zakayi maganar?kaga pls juz tell me duk abinda ke akasa,bazan iya jira har se ya dawo sannan ayita ba,juz tell me ko haka dan nawa ze k'arashe rayuwarsa cikin wannan yanayin becuz I guess abnda ke aranka kenan wanda kake shirin fadawa mai martaba.... "
Kuka yaci k'arfinta,juyin duniya yayi lallashin akan tayi haquri tayi shiru amma taki,akan dole ya haqura ya fice daga office din bayan ya gargadi nurses akan cewar kar Wanda ya kuskura ya sake nesa da prince because ko irin yanayin daya shiga adazu akwai taimakon gaggawa daya kamata su masa kafin akirashi,amma babu wanda ke wurin alokacin,ya tabbatar musu da cewar Idan suka kuskura koda wasa suka sake maimaita hakan,toh kuwa hadasu da ogansu zeyi and dey know wat dat means.
Don kanta tayi shiru,taja jiki zuwa inda wayarta yake,babu b'ata lokaci ta latso mai martaba don ta tabbata ko airport basu kai ba don basu wani jima da tafiya ba prince ya farka.Ai kuwa taci sa'a call din ya shiga,yana dagawa ta fashe masa da kuka tare da gaya masa cewar ai prince ya farka kuma ya sake komawa kamar koda yaushe,salati ya sakar,shima din wasu hawayen yaji sun tarun masa acikin kwarmin ido,wai yaushe prince Aryaan ze tashi ne? Hakan ya ayyana aransa.
Ta fada masa cewar gashi-gashi yadda sukai da Dr.Bature,ina ai baze iya haqura har se bayan ya dawo ba sannan suyi maganar,duk wani uzurinsa ze biyo bayan lalurar dansa ne,sam baya wasa da batun ciwon dan tilon dansa,duk da cewar mahaifiyarsa ce ta rasu shiyasa yake kokarin komawa Nigeria,amma hakan be hana masa bada umarnin juya kan mota xuwa asibitin ba.
Amintacciyar Jakadiyartace ce ta shigo dakin goye da wata 'yar two years baby,qanwar prince ce *'ZAITON'*,rigimammiyar 'ya kenan,bata yadda da kowa idan ba mamanta da babanta ba,se kuma ita jakadiyar wacce rainonta ahannunta yake shiyasa take dan yarda da ita.Yanxu mah haka kurum ta saka musu rigima sanda taga Mai martaba ze tafi,wai ita akan dole saita bishi,shine aka mata dabara akace jakadiya ta goyata su dan zazzaga cikin asibitin har tayi bacci,shine se yanxu suke shigowa dakin.
"Jakadiya har tayi baccin? "
"Eh ranki shi dade ta dan jima da yinta,kawai na cigaba da zagayar ne don baccin ya dada yin qarfi.... "
Tana gama fadar hakan ta isa ga wani extra bed ta kwantar da ita ahankali kamar wata kwan da ake tsoron fashewarta.su kadai ne adakin don sabida mukaminsu aka mallaka masu wannan dakin su daya,sannan kuma wai don lalurar prince baya son hayaniyar mutane,shiyasa aka keb'eshi daga sauran patients din.
Babu b'ata lokaci sai ga mai martaba ya iso tare da dogarawansa biyu biye dashi abaya,wani uban sauri suke ta zabgawa kamar zasu tashi sama ah sa'ilin da suka soma tattaki bayan sun sauko daga cikin mota,jama'a kuwa sai kallonsu ake musamman Mai martaba Wanda kusan zan iya cewa ba'a cikin hayyacinsa yake ba.Straight ofishin Dr.Bature suka nufa wanda yake acikin ward din da aka kwantar da Prince Aryaan.
*** "Ikon Allah! your highness ashe ba ance min ka dade da tsufa ah airport ba? azatona ma jirginku ya dan jima da flying,sai kuma gaka anan,lafiya ka dawo da baya kuma?" Dr.Bature ne yayi wannan maganar ah sa'ilin da kallonsa ya sauka kan Mai martaba wanda ya shigo cikin ofishin dauke da sallama abakinsa.
Saida mai martaba ya samu wuri ya zauna tare da cire hularsa ta sarauta ya ajje saman tebirin dake tsakaninsu da Dr.Bature,kana ya budi baki yace"Ance kana son magana dani akan rashin lafiyar d'ana dalilin daya saka na dawo da baya kenan.... "
"Kashhhh! yanzu saida gimbiya ta saka ka dawo da baya?seda fa nace mata ta bari harka dawo sannan ayi maganar amma....... "
Da sauri mai martaba ya tari numfashinsa"Look Bature rayuwar d'ana yana da matukar muhimmanci agareni wanda bana jin zan iya yin sakacin rasashi saidai idan rabbi ne yayi ikonsa akansa,amma da lafiyata da komaina,ina ji kuma ina gani bazanyi wasa da rayuwarsa da gangan ba,don haka Dr.Bature Abu sadiq bazan iya haqura har sai na dawo kafin ayi maganar ba,so now tell me wat's the deal?meh kakeson gaya min agame da ciwon prince?"
Saukar da ajiyar xuciya Dr.Bature yayi,kana ya soma bayani"wato your royal higness amatsayinmu na kwararrun likitocin kasar india, munyi iya bakin kokarinmu wajen yakice cutar _*'Medulloblastoma brain tumor'*_ da danka keda shi,kuma munyi nasara,ayanxu sam bashi da wannan cutar,sai dai kuma komfutocinmu sun kasa detecting shock din dake kai masa attack ah kwakwalwarsa,munyi iya bakin kokarinmu wajen gano wannan matsalar amma abu daya har yanxun yake nuna mana wato _*'NOT DETECTED'*_,wannan shock din itace ta saka yake cikin coma,aduk lokacin daya yi yunkurin dawowa cikin rayuwa se kaga shock dinnan ta kai masa hari wanda hakan ke saka kwakwalwarsa baze iya juran shock dinnan ba se kaga ya koma cikin coman,am sorry to say idan har shock dinnan ya cigaba dakai masa attack continuosly toh kuwa watarana yana iya loosing memory dinsa,yaji kawai ya manta wasu abubuwa da suka faru dashi na shekarun baya can,idan har ze warken kenan,or probably lead to mental madness,infact it can also lead to the dead of the victim......"
Cike da zafin rai Mai Martaba Umar faruq Bahago ya mik'e tare da kaiwa table din dake atsakaninsu mugun bugu bana wasa ba,kana ya daga yar yatsa yana nuna Dr.Bature dashi,yace"Dr.Bature kalamanka suna neman yin tsauri da yawa don haka kayi gaggawan kiyaye harshenka,ni dana baze tab'a haukacewa ba kamar yadda kake masa fatar hakan,prince Aryaan insha Allahu nan bada jimawa ba ze tashi,ze dawo ya cigaba da rayuwarsa kamar kowani dan'adam,na baku nan da sati biyu cur! idan har banga wani changes ba,toh kuwa zan dauke d'ana xuwa wata k'asar don ba ku kadai ne kwararrun likitoci anan doron k'asar ba,aikin banza kawai....... "
Yaja tsoki tare da daukar hularsa ta sarauta daya ajje saman table,ya kafata akai,kana ya fice daga office din,Dr.Bature kuwa sae binsa yake da kallo baki sake,mai martaba ma bai tsaya yaji shawarar da zai bashi ba kawai ya dau magana da zafi,girgiza kai kurum Dr.Bature yayi tare da ayyanawa aransa cewar sannu ahankali zai fahimtar dashi abinda yakeson gaya masa agame da ciwon d'an nasa.
Mai martaba na fita,straight ya nufi room din da aka kwantar da prince ayayin da dogaransa suka take masa baya.Yana shiga dakin ya tarar da Gimbiya zaune kusa da Prince,hannayenta sarke cikin nashi as usual,sam baya son ya kara mata wani damuwar akan wanda take ciki shiyasa yayi saurin shanye bakin cikin daya kunso awurin Dr.Bature.
Hawaye ne ya soma kwaranyowa asaman kuncinta ah sa'ilin data hada idanuwa dashi,kansa ya shiga girgiza mata yana fadin"A'ah my Najmiy karki soma,mu cigaba da yiwa Aryaan addu'a insha Allahu zaya tashi da izinin Allah ta'ala,oya maza wipe up ur tears and put a smile on ur face for ur dear King.... "
Wani irin pretty smile ne ya sub'uce mata wanda har hakan ya sanya ta dan manta da kuncin da take ciki na yan dakiku,ai kuwa da hanzari tayi kamar yadda yace.
Matsowa yayi kusa ya bata labarin yadda ta kaya tskaninsu da Dr.Bature,tasha kuka sosai ayayin da mai martaba ya dunga bata baki,akarshe ta saduda ta fawwalawa Allah komai,yayi mata sallama ya tafi akan cewa bayan anyi sadakar uku zai dawo sai susan nayi da prince,idan har babu wani changes tofa zasu daukeshi zuwa qasar Germany.
_*How far Hafnan's freaking fans? How was the first page?is it okay?and if yes should I move on?*_
_*will prince Aryaan survive at all?*_
_*sannan wannan wani irin shock ne da har kwararrun likitoci kamar na k'asar India suka kasa ganowa?*_
_*Sannan kuma ku biyoni don jin irin tsuntuwar da Mai martaba umar Faruq Bahago zaiyi akan hanyarsa bayan ya sauka qasar Nigeria*_
*I* *STILL*
*REMAIN*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(ƘվɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*
**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє 💏**
*MALLAKAR:HAFNAN* *WATPADD:HAFNANCY* ___________________________________
**ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,eмιr oғ nιger ѕтaтe,мιnna**
https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
{ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ} *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
_*°•gaιѕυwar вan gιrмa gareĸa мaι мarтaвa Dr.υмar ғarυq вaнago,нaqιqa ĸa cιĸa ѕнυgaвan ĸwaraι wanda вυrιnѕa aĸodayaυѕнe ѕнιne ya ĸyaυтaтawa тalaĸwanѕa,мυ'aмalarĸa da мυтane ιѕ jυz perғecтly oĸay,ιna neмar gaғararĸa,вanyι wannan lιттaғιn don тѕoĸacι agareĸa вa,ĸιrĸιnĸa ga al'υммa ya ѕanya nayι aмғanι da ѕυnanĸa dιrecт вa тare dana canza вa,υвangιjι Allah yaѕa ĸa wanye da dυnιya laғιya,can'т love yoυ leѕѕ мy ĸaĸυѕ😀•°*_
_*°•wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸι ne ĸe daya мy ѕaнιвa jaмeelaн janaғ,ĸιrĸιnĸι agarenι ιѕ jυz ĸιnda мaѕнa Allah,нaĸa мa ѕoyayyarĸι agarenι ι jυz нave тo alнaмdυlιllaнι ĸaѕeeran,ιna ѕon ĸι ѕanι cewar nι нaғnan ιna мιĸι ѕo мaι cιĸe da dυмвιn qaυna💕,don Allaн ѕaнιвa ĸι cιмιn υwarĸυ нaj. ĸarι da ѕaĸιna😂, мaĸe deм ѕυғғer & regreт ιn lιғe😁, ĸι ѕaѕѕaιтa мιn ĸawυnanѕυ dυĸ plѕ😊,ĸυ neмa ĸυ ĸaranтa lιттaғιn ѕaнιвa мaι ѕυna 'TA TAFKA KUSKURE•°'*_
💥
*Թɑցҽ4⃣*
_*SHIN WANENE MAI MARTABA UMAR FARUQ BAHAGO?*_
Mai Martaba Umar Faruq Bahago ∂a ne ga tsohon sarkin Minna wanda ake kira da _*'мaι мarтaвa мυнaммad ĸнaмιѕ вaнago'*_.Matan auran Mai martaba m.k bahago biyu,Gimbiya Khadeejah wacce aka fi sani da Haj.Babba itace uwargidansa,ita dinma 'ya ce ga sarkin gombe _*мaι мarтaвa мυнaммad υмar zayyan*_.Ya'yanta uku kacal aduniya, *'UMAR FARUQ'* (present emir) shine danta na fari,sauran biyun kuwa duk mata ne,*'ABIDA'* da kuma *'HIDAYA'*.
Bangaren ∂ayar matar tasa kuwa,sunanta gimbiya Maymunerh wacce ake kira da Haj.Karama,ita kuwa danta guda daya kacal data haifa adoron kasa,sunansa *HAYATUDDEEN'*,bayan haihuwarsa ko batan wata bata sake yi ba,haihuwar ta tsaya mata cak!,toh dayake ita din macece mai tawakkali da kuma haquri sai ta nuna godiyarta ga Allah madaukakin sarki da guda dayan daya azurtata dashi,wata tana nan mah ko barin wata bata taba yi ba,haihuwa take nema ido arufe amma Allah bai bata ba,toh ita wacece da har zata butulcewa ubangiji bayan mah ya azurtata da guda daya? Haka ta haqura ta rungumi dan tilon danta da kuma 'ya'yan kishiyarta,sosai suke zaman lafiya don itama Haj.Babban macece mai mutunci da kamala da kuma son ganin an zauna lafiya,haka mah 'ya'yansu akwai wata irin muguwar shaquwa ta yan'uwantaka mai karfin gaske atsakaninsu,kawunansu duka ahade yake,kai infact idan ba sanin gaske kayi musu ba,toh kuwa bazaka iya tantance dan dakin nan da dan dakin can ba komin kwakwarka kuwa.Hayatudden mah kwasar duka kayansa yayi ya koma bangaren Haj.Babba ah inda ya saje dasu ya zamana kamar itace ta haifeshi ba Haj.Karama ba.
Mai martaba M.K Bahago wani irin mutum ne mai saukin kai sosai,shi din mutumin jama'a ne don cewa suke ma yasan darajar mutane,amulkinsa mutane suka san kalmar *'Adalci da kuma kwatar yanci'* suna existing har yanxu azamaninmu,duk wanda ya zalunci waninsa,toh kuwa Mai martaba M.K bazai taba barinsa ya tafi ba har sai yasa an masa hukunci daidai da laifinsa da kuma yadda addininmu ya tsara,atakaice dai Mai martaba yana mugun kyautata mu'amalarsa da jama'a,ga taimakon talakawa da kuma jawosu ajiki,to make it short,kowa na bala'in sonsa kuma akullum fatar alheri suke masa da zuriarsa.
Mai martaba M.K bahago beyi karatun boko ba seta arabi,yayi karatun allo mai zurfi,duk da cewar beyi karatun boko ba amma yana bala'in sonta shiyasa yaci alwashin 'ya'yansa duka sai sunyi.
_*°•WASU SHEƙARUN BAYA CAN DA SUKA SHUDE•°*_
Wata tafiya ce mai martaba M.K bahago ya taba yi zuwa garin kano ta dabo tumbin giwa(sai mu nan munfi kowa😀)sarkin kano ne ya aika masa da katin gayyata ta bikin wata 'yarsa shine yaje,toh akan hanyarsa ta dawowa ne da masu tsaron lafiyarsa (dogarawa) suka gan wata 'yar karamar yarinya wacce bazata wuce sa'ar autarsa Hidaya mai shekaru bakwai aduniya ba tana ta kuka agefen titi,kuma abin mamaki duk cincirindon mutanen dake ta kai komo amma anki samun wanda yayi tunanin tsayawa ya magance mata damuwarta,kowa sabgar gabansa kawai yake.Mai martaba M.k shine ya umarce dogarawansa dasu tsaya yana son jin matsalar yarinyar sannan ya magance mata ita.
Shida kansa ya fita yaje har inda yarinyar take tsaye ya tsugunna yana tambayarta abinda ke damunta har take kuka,sannan kuma iyayenta suna Ina?
Ita kuwa yarinyar ko kadan bataji abinda ya fada ba don bata jin Hausa.Fashe masa da kuka tayi tace _*"'ana la'afham ma taqul.... "*_ ma'ana"Ban gane abinda ka fada ba"
Jikinsa ne yaji yayi sanyi qalau,atake anan ya gano dalilin daya sanya kowa yaki taimakonta,wato ita din balarabiyace don halittarta kadai ma ya nuna hakan,babu meh jin larabcin da take yi shiyasa kowa ya shareta ya cigaba da sabgar gabansa. Ya rasa abinda zece mata don shima din ba wani jin arabin yake sosai ba,can ya daure yace _*ayna abuki wa'umki?*_ ma'ana"Ina abbanki da ummanki suke?"
Jin yayi larabci ya saka wani pretty smile sub'uce Mata,atlast ta samu wanda ke jin larabci don ta dade tana zaga gari tana cigiyar dan'uwanta,tana yi tana hadawa da kuka,duk wa'enda tayi ta haduwa dasu ahanya suka kuma tambayeta dalilin kukanta?bata jin abinda suke fada,sai dai tayi musu bayani da larabci cewa dan'uwanta ne ya b'ata shine take nemansa,sai kaga mutum yaja tsoki yayi wucewarsa abinsa tunda bai gane abinda take fada ba balle yace bari ya taimaka mata.
Bayanin iyayenta ta shiga yi masa da kuma Akhee (my brother) kamar yadda take k'iran dan'uwanta daya b'ata.Tana yi tana hadawa da kuka da kuma kwatance da hannu,mutane kuwa tuni suka soma yi musu chaa! aka,da hanxari dogarai suka taka musu birki,suka hana musu samun kusanci da inda mai martaba M.K bahago yake.Don haka daga nesa kawai suka tsaya suna kallon ikon Allah!.Shi dai mai martaba M.K babu abinda ya tsinta acikin labarinta don iliminsa ta larabci bata kai girman wannan ba,haka mah dogarawansa babu abinda suka tsinta illa mah yarinyar birgesu tayi yadda take ta fidda larabci dakyau abin gwanin ban shaawa,yanayinta ne kadai zai sa kasan cewar labari me cike da tausayi ne take badawa.Abinda kawai mai martaba ya tsinta acikin labarinta shine, _*'Waldi*_ wanda yana nufin 'mahaifina',sai kuma _*'Ummii'*_ wanda yana nufin 'mahaifiyata',sai _*'Akhee'*_ wanda 'dan'uwana' yake nufi,se kuma _*'Ukhti'*_ wanda yake nufin 'yar'uwata'.Toh abubuwa ukun nan ne kurum ya tsinta acikin labarinta.
Ya dubi dogarawansa yace"Ina ganin kawai mu dauketa mu kaita gidan sarki tunda bamu tsinci komai acikin labarinta ba sannan kuma shi kadai yasan yadda zaiyi da ita tunda acikin garinsa ta fado,amma ni ina ji acikin jinin jikina cewar ba karamin zaluntar yarinyar nan akai ba..... "
Dukawa sukai alamun girmamawa,sukace"Hakan kuwa za'ayi ranka shi dade,kamata yayi kawai akaita gidan sarkin...... "
Ya kamo hannunta ta soma turjewa tana yakusarshi,tana hadawa da ihu da kuma kokarin son takai masa cizo,da hanxari dogarai suka fasa mata wani uban ihu wanda hakan ba karamin razanata yayi ba,at once ta shiga cikin taitayinta,dole tayi musu hakan don hakan ce ta faru da Akhee dinta,tana ji tana gani wasu sukai gaba dashi acikin mota,shiyasa take gani kamar itama din cutar da ita zasuyi.
Mai martaba yadan murmusa yace"Ku rabu da ita don Allah don ko waye ne mah zeyi tunanin cutar dashi ake shirin yi balle ita da take yarinya karama mah kuma wacce ko kadan bata jin yarenmu,dole ne tayi tunanin kila cutar da ita muke shirin yi.... "
Daya daga cikin dogaran ne yaji kawai yarinyar ta bashi tausayi,cikin harshen turanci yace"My dear relax! We mean no harm,we juz want to help..... " (dayake acikinsu duka shi kadai ne ya dan taba boko,amintaccen mai martaba kenan kuma shine ya rikeshi har ya sakashi aboko,iyakacinsa ss3,daga nan kuma ya zama dogarinsa,shine translator din sarki aduk lokacin da wani yayi wa sarki turancin da bai ji ba,Jabir ne mai translating😀😂).
Ita dai binsa kawai tayi da kallo don ko kadan ilimin turancinta bai kai nan ba,dake ita kanta batayi bokon ba,abinda kawai ta tsinta shine kalmar 'help' wanda hakan na nufin taimakonta zasuyi kenan.Shima kalmar 'Help' abakin mutane take jinta idan zaayi taimako kenan.
Wani ne acikin jama'ar da suka taru yace"Toh ina kuma zasu kaita?kar dai ace fa saceta suke shirin yi.... "
Da sauri Jabir ya waiga yana duban dukkan ilahirin jama'ar,axuciye ya juya ya soma takawa xuwa garesu yana fadin"Ina wanda yayi wannan maganar yake?maza ya fito nan..... "
"jabir rabu dasu kawai kazo mu tafi,idan mutum yace zai biye ta jama'a toh kuwa bazai taba tabuka abin kirki ba,gidan sarki zamu kaita tunda ku bakuyi tunanin kai baiwar Allahn nan can ba,ni ban san meyasa duniyar nan ta lalace ba,sam babu taimako kowa kansa kurum ya sani,Allah ya kyauta.
Haka suka bar wajen suka nufi gidan sarkin kano,mutane kuma suka soma watsewa kowanne cike da mataccen jiki don sosai maganganun mai martaba ya shigesu dakyau.
_*Note:pls don't b confused,shekarun baya fa muke tunawa ahalin yanxu,labarin tsohon emir muke badawa wato mahaifin mai martaba umar bahago,yana da matuqar muhimmanci kuji wannan labarin kafin mu koma kan ainihin labarin,wannan labarin shine mafarin komai*_
_*Idan har na gamsu da sharhi sosai da sosai toh ina iya baku update anjima,Nagode*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💞*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(ƙ'վɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*
**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💞*
*WATPADD:HAFNANCY*
**ՏɑժɑվƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα** ______________________________________
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
{օղաɑɾժ ԵօցҽԵнєɾ} *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
_*°•мy anтy нaυwa мarυвυcιyar 'laвarιn rayυwaтa' ĸιna ιna?тoн ιdan ĸιna ĸυѕa мaza ĸι мaтѕo don wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸι ne,na вaĸι ѕнι нalaĸ-мalaĸ,gιrмanĸι da мυтυncιnĸι aн ιdona ya wυce yadda ĸιĸe тѕaммanι cυz υ are really ιndeed a ѕιѕтer,aм very нappy тo нave υ ιn мy lιғe,Allah yaвar qaυna da хυмυncι,нaғnan тana мιĸι ѕon qaυna anтy нaυwa•°*_
💥
*Թɑցҽ 5⃣*
Acan gidan sarkin Kano kuwa,sosai yayi mamakin dawowar mai martaba M.K Bahago na ganin rabuwarsu kenan da nufin komawa garin Minna,don ana gama daurin aure,bai wani tsaya ba yace yana da wani uzuri dake jiransa ah minna,sukayi sallama ya taso tare da masu tsaron lafiyarsa,dalilin daya sanya sarkin Kano shiga tsananin mamakin kenan na ganin dawowarsa.Amma jin abinda ke tafe da Mai martaba M.K,ya sanya jikin sarkin kano yin sanyi qalau,gashi shima din ba wai yana jin larabcin bane haka mah jama'ar dake cikin fadarsa babu wanda harshensa ta larabci ya nuna,tunawa yayi da cewar akwai wani d'an abokinsa wanda yake jin larabci sosai,hasalima ah qasar eygyt yayi karatunsa ah inda ya karanci 'Islamic studies' zallah,Malami ne sosai wanda garuruwa da dama mah sukan gayyaceshi yin wa'azizzika.
Nan da nan kuwa ya aika hadimansa da suje su taho masa da Mal.Zubair (sunan malamin kenan).Wani aiki yake amma sai ya ture yabi bayansu don kiran sarki kira ce wacce bazaka iya ƙin xuwa ba.
Koda yazo aka masa bayanin wannan yarinyar,takawa yayi har xuwa gabanta ya tsugunna tare da tsura mata ido,ita kuwa baiwar Allah tun shigowarsu fadar take ta rawar dari gami da zazzare idanuwa lokaci xuwa lokaci don ko kadan ta rasa gane abinda ake ciki.Ahankali ya furta _*Alaisatirkha Hakaa kisswatu... " ma'ana"Ki nutsu ki bamu labarinki."
Kamar dama jira take abata umarnin hakan,sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da kuma ban tausayi,ta shiga yi masa bayani ayayin da shi kuma yake aikin gyada mata kai wanda hakan ke nuni da cewar sosai yake gane bayanun nata,sauran mutan fadar kuwa,babu abinda suke illa sharar hawaye duk da cewar basu jin abinda take fada,amma duk wani mai imani da kuma raunin xuciya idan ya kalleta sai ya tausaya mata sabida yanayin yadda take bada labarinta kadai mah ya isa kasan cewar labari ne mai cike da tausaya take badawa.
Bayan ta k'are labarin nata,Mal.Zubair ya juyo garesu,kwarmin idanuwansa cike suke da hawaye wanda dab suke da soma gangarowa saman kuncinsa,ta maza yayi ta hanyar kwafesu sannan ya soma fassara musu labarin data bashi cikin harshen hausa.
"Wato ita dai sunanta _*'Najmiyyah Gaddafi'*_,shekarunta na haihuwa bakwai,yar wani gari ne mai suna _*Baghdad*_ wanda shi din babban birni ne dake cikin ƙasar Iraq.Tana da yaya namiji mai suna *'Aryaan'* wanda take ƙira da 'Akhee',shekarunsa na haihuwa goma sha biyar,sai ƙanwarta mai suna *'Yumna'* wacce take ƙira da 'Ukhti',ita kuwa shekarunta na haihuwa biyar ne kacal.iyayensu talakawa ne liƙis wanda abincin da zasu ci mah sau uku arana daya gagararsu take,suma din sun tashi sun tsinci iyayen nasu ne acikin irin wannan rayuwar ta rashi,basu da kowa sai su ukun nan da suka haifa,Akhee shine kadai wanda aka saka amakaranta boko mai dan sassaucin kudi,su kuwa ba'a sakasu ba don iyayen basu da ƙarfin sakasu su duka,shima din don yana da namiji ne shiyasa aka sakashi dake yafi matan buqatar ƙaratun ko don gobe.makarantar islamiyya ce kurum suke zuwa.Wani abin birgewa wai shine,aduk sanda Akhee ya dawo daga makaranta toh duk wani abinda aka koya masa tofa zai hada kan kannen nasa ne suma ya koyar dasu,tofa anan ne suka soma tsintar kananu-kananun turanci.
Ah ƙasar Iraq suna zamansu lafiya qalau,fitintinu da kuma rigingimu awannan qasar da dan sauki musamman yankinsu Najmiy sam da wuya kaji ana tashin hankali anan.Kwatsam wata iftila'in ta kunno kai cikin wannan babban birnin,fada ta hada matasan Baghdad da kuma sojojinsu har takai ga kashe kashen rayuka,gida-gida ake bi ana kashe mutane,idan Allah yace da sauran kwananka agaba,sai kaga ka tsira,nasan kuna sane da wannan fadar da akayi awannan kasar don shekaranjiyan nan akayi news dashi,toh acikin rayukan da aka kashe,ciki kuwa hadda iyayen Najmiy da kuma 'yar qanwarta Yumna wato Ukhti.Cikin ikon Allah sai Najmiy da dan'uwanta Aryaan wato Akhee suka samu suka tsere,'yar karamar katangarsu suka haura suka sauka.Toh sai suka samu suka bi mutanen da suka tsere,tare da taimakon wani tsoho suka fad'o Nigeria kuma anan garin Kanon.Sunso bin wannan tsohon amma sai yace musu kowa yayi ta kansa,sauran ma haka sukace musu.
Tofa! Su Najmiy suka rasa madafa,gasu da kananun shekaru,shekarar Akhee goma sha hudu ayayin da ita kuma take da shekaru bakwai kacal aduniya,haka suka dunga yawo agari babu wanda ke son ya taimaka musu,wani gun ma wai korar kare ake musu,wasu kuma k'yamarsu ake balle anga farar fata (kun san dai yadda wasu ke k'yamar farar fata musamman irin fatar turawa ma wa'enda ba kabilarsu ba)😂.
Akarshe dai wasu samari dake cikin wata mota suka k'irawosu,toh turanci sukai da dan'uwan nata wanda ko kadan bata tsinci komai aciki ba,kalmar *'I will'* ne kawai ta gane,wanda hakan ke nuni da cewar wani abin suke son yayi musu shine yace zaiyi.
Can yayi mata bayanin cewar wani aiki zasu sakashi yi idan yaso sai su bashi abinci ya dawo suci tare,don haka ta zauna ak'arkashin gindin wata bishiya,bazai dade ba zai dawo.Tana ji tana gani akai gaba da Akhee dinta acikin mota,shi kuwa lek'owa yayi yana daga mata hannu yace _*"wada'an hataa naltaqi mujadadaan fi waqt lahiq Ya ukti😭"*_ ma'ana _*Goodbye till we meet again later my dear sister😭*_ (Ashe sallama ta har abada ne sukayi basu sani ba).
Shiru shiru 'Akhee zai dawo amma babu koda labarinsa,yinin ranar nemarsa take tayi tana kuka agari amma babu wanda yake jin yaren da take balle ya taimaka mata,akarshe awannan karkashin bishiyar ta koma ta shimfida siririn mayafin jallabiyarta anan,raguwar dan ruwan pure water data gani awurin bishiyar ce ta dauka tayi alwala da ita,gashi bata San lokaci ba don haka ta jera sallonlinta duka tayi,dan half sunna hijab ne kanta.haka ta kwana awurin da tsoro,ga yunwar da take ta addabarta,tun safe bata saka komai acikinta ba har dare,kuka take tana ambaton "'Akhee ina ka shige ne?" Allah ne dai kawai ya tsare baiwar Allahn nan daga fadawa hannun yan bata gari da kuma kidnappers har wayewar gari wanda kwana tayi zaune ko runtsawa batayi ba.
**** Washeqari ma haka ta tashi tana kuka tana neman Akhee dinta har bakin titi,shine fa har Allah ya kaddara haduwarta da mai martaba muhammad khamis Bahago.
Mal.Zubair ya karashe zancensa da"Allah ya taimaki mutumin talakawa,Allah yaja da ran sarkin sarakuna,haqiqa kayi tunani mai k'yau daka taimaki wannan baiwar Allahn har ka kawota nan gidan mai martaba sarkin kano,kayi namijin kokari wajen ceton wannan 'yar yarinyar daga fadawa cikin gararin rayuwa da kuma 'yan bata gari,ana yawan fada min cewar kana da taimako amma ban taba yadda ba sai yau,ubangiji Allah ya saka maka da mafificin alherinsa........ "
Gabaki daya kowa ya karba da "Allahumma amin..... "
Babu wanda bai zubdawa Najmiy kwalla ba na tsananin tausayinta.Sarkin kano shine ya sanya Mal.zubair tambayarta ko zata iya bada kwatancen halittar dan'uwan nata,da sauri ta gyad'a musu kai alamun zata iya din.Sarki ya bada umarnin aje anemo kwararran 'sketch artist' yazo ya zana musu fuskar Akhee dinta.
Kafin ah iso dashi,tuni sarkin kano ya sanya aka kawo mata abinci irin wanda aka san zata iya ci,kana ta biya sallar asubahinta don shine kadai ake binta.Bayan mai zanen ya iso,babu b'ata lokaci ya soma zanensa cike da kwarewarsa,tana kwatantawa Mal.Zubair yadda halittarsa take ayayin da shi kuma yake aikin fassarawa mai zanen,sharp sharp kuwa ya gama.
Tsab! Kuwa ya samoshi,tana ganin fuskar Akhee dinta kan farar takadda ta fashe da kuka tana fadin" Akhee kana ina?Don Allah ka dawo kai kadai ne ka rage min.... " da larabci ta fadi hakan.
Mal.Zubair ne ya shiga lallashinta akan cewa za'a ga dan'uwanta nan bada jimawa ba insha Allah.Sarakunan sukayi taking excuse suka fice waje sukayi shawarwari atsakaninsu,can suka dawo suka fadawa kowa shawarar da suka yanke.
Mal.zubair ya dubeta yace"Daya daga yace cikinsu yana son ya rikeki har zuwa lokacin da za'a ga dan'uwan naki,don haka wanne acikinsu kikeson ya rikekin?" ya fadi hakan tare da nuna sarakunan biyu.
Kallonsu ta shiga yi,itafa zuciyarta yafi kwantawa da wanda ya taimaketa afarko wato mai martaba M.k bahago.don haka nunashi tayi tace _*"Hadha*_, ma'ana"wannan "
Kowa yayi hamdala,aka damka amanar baiwar Allah 'Najmiyya Gaddafi' ahannun mai martaba M.K bahago har zuwa lokacin da za'a ga dan'uwan nata.Shima ya qarbi amanar da aka bashi da hannu bibbiyu tare da daukar alkawarin cewar tsakaninsa da Allah zai riketa kamar 'yar cikinsa.Aka rufe taro da addu'a.
Awannan ranar aka fidda wa'enda sune zasu je nemo Aryaan Gaddafi ah cikin garin kano tare da taimakon hoton fuskarsa da aka zana.
Sai goshin magrib Su mai martaba suka iso garin minna.
_*shigowar Najmiyya Gaddafi 'yar mutan Baghdad cikin wannan royal family din shine mafarin komai,muje zuwa my fiful😉*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(Ƙ'վɑմԵɑ ժɑցɑ Aℓℓαн)❄️*
**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN*
*WATTPAD:HAFNANCY* ____________________________________
**ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.մʍɑɾ fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα**
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
{օղաɑɾժ ԵօցҽԵhҽɾ} *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
_*°•wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸυ ne yaѕeera cool angel,нaғѕaт ĸanтy, мaмan ѕadιq,ғarιda тalвa,мoм ĸadιja, υммυlĸнυrѕooм,ѕιѕтer мaryaм,мy ғυlanι,мy janaғ,мy najaтee da ѕaυran wa'enda вan aмвaтo вa,нaqιqa coммenтѕ dιnĸυ yana ѕυмar danι,ιna мιĸa godιaтa agareĸυ allaн yaвar love da хυмυncι,aмeen•°*_
💥
*Թɑցҽ6⃣*
Koda mai martaba ya labartawa iyalansa labarin Najmiy,suma din sosai suka tausaya mata hadda zubda mata hawaye,ita kuwa sai binsu kawai take da kallo don ko kadan bata tsinci komai da suke fada ba amma dai tasan labarinta ne Mai martaba ya basu.lafiyayyar girki aka taresu dashi kuma ba laifi Najmiy ta cire kunya da bakunta taci sosai.Suna kammala cin abinci aka soma kiraye kirayen sallar magrib.
Kallon mai martaba tayi,akwai magana abakinta amma ta rasa yadda zata fadeshi har su gane abinda take nufi tunda ta lura suma din ba wai jin larabcin suke ba,gwara gwara mai martaba m.k.
Kowa yana lure da ita amma sai aka dake ana sauraron aji abinda zatace,idan ta bude baki zatayi magana sai kuma kaga tayi saurin rufewa,Hayat ne ya sanya hannu ya rufe bakinsa jin wani uban dariya na nemar kufce masa.Haj.Karama ce ta masa ido alamun maza ya kama kansa.
Duk da cewar tasan Najmiy ba lallai ne taji abinda zata fad'a ba,amma sai ta daure tace"Daughter what's wrong?"
Ai kuwa ta gane kalmar 'wrong',don haka da sauri tace"Ummii salat" murmushi sukai gaba dayansu wato dai tana nufin tana son tayi sallah ne,kowa awurin sai yaji kawai ta mugun birgesa,Mai martaba ya dubi su Abida yace"Maza Abida ku tashi kuja yar'uwarku kuje ku gabatar da sallah."
"Toh Abba mai martaba."haka suke kiransa,cike da farin ciki suka ja hannun Najmiy sukayi ciki.Hayat ya saukar da wata ajiyar zuciya wanda hakan ya janyo hankalin kowa zuwa gareshi,saurin saddar dakai kasa yayi yana dan murmusawa ganin an kura masa idanuwa.
Haj.Babba ce kawai ta dan murmusa tace"Kai Hayat akwai shiririta.... " daga haka kowa ya mike don gabatar da sallah.Mai martaba da samarin suka fice zuwa masallacin gidan.kowacce ta koma turakarta don dama ah turakar mai martaba duk suke.Bayan Najmiy tayi sallolinta hadda ta isha'i,su Abida suka bata kayan bacci ta saka tare da bata wata zumbuleliyar hijabi,suka tafi turakar mai martaba suka masa saida safe,shi kuma yayi masu fatar alheri,haka ma sunje sukayiwa haj.k'arama sallama,kana suka komo bangaren haj.babba,itama suka mata saida safe,kana suka wuce dakin baccinsu tare da Najmiy din.Al'adar royal family din kenan,Kafin su kwanta duk sai sun bi iyayen nasu sun masu gaisuwar k'arshe ta wannan ranar.
***** Washeqari Mai martaba ya tara duka iyalansa da kuma bayinsa,ya sake bada labarin 'Najmiyya Gaddafi' tare da nuna musu cewar ita din amana ce agareshi,don haka ya gaya musu cewar duk wanda ya bakanta mata toh kuwa kamar ya bakanta masa ne,don haka kowa ya kiyaye.kowa ya daukar masa alqawarin cewar insha Allah ze kiyaye kuma Allah ya bayyana dan'uwanta.Ita kuwa Najmiy sai bin mutane take da kallo don ta kasa gane wainar da ake toyawa,shi kuwa Hayat duk abinnan da akeyi hankalinsa baya garesu,gabaki daya hankalin nasa ya tafi ne ga Najmiy,sosai yarinyar ke birgeshi,ya rasa meyasa yanayin tsoronta da kuma yanayinta cikin danuwa yake bashi sha'awa.(Anya Hayat?I think you are alrdy inlove with balarabiya😀).
For the very first time,idanuwanta da nasa suka sarke cikin na juna,irin kallon da yake jifarta dashi yasa tayi saurin dauke kallonta daga gareshi,can kuma ta sake maida kallon nata gareshi,taga still ita din dai yake kallo hadda wani kashe masa ido daya.Tuni ta saddar da kanta kasa.
"Allah yaja da ran yarima karami,muje kayi shirin makaranta.... " haka yaji wani dogari ya fada,sai asannan ne ya lura ashe har an watse har Najmiy din,shi kadai ne ya rage acikin fadar sai kuma mai martaba da wasu dogarawan fada da kuma mai kula ko kuma nace mai hidima dashi Hayat din.
"Ai daka bari ya gama tunane-tunanen banzansa har yayi latti yaje yasha bugun tsiya amakaranta.... " mai martaba ne ya fadi hakan awasance.
Hayat yace"Tabdi! Abba mai martaba yanzu sai adoki the whole prince of sarkin minna?remember am Hayatudden freaking M.k bahago...... "
"Dallah can rufewa mutane baki anan,don kana d'an sarki shine zai hana ah hukuntaka?".....
Aka fashe da dariya,so yake yayi magana sai kuma wannan dogarin nasa ya sake magana"Allah ya taimaki Yarima karami,lokaci na kurewa kuma ina jiye maka fadar malaman makaranta..... "
Wani kallo ya watsa masa don shi sam arayuwarsa ya tsani ata nanata masa magana dai daya.bai sake cewa komai ba ya russuna ya sallami mahaifinsa,kana ya wuce ciki don yin breakfast cuz already yana saye cikin uniform dinsa ne.
Awannan ranar Mai martaba M.k ya sanya aka samo masa wani malamin larabci wanda kuma ya goge ab'angaren harshen hausa da kuma turanci,zai dunga zuwa ne akullum yana koyar da Najmiy hausa da turanci har zuwa sanda zata kware,sannan kuma idan tana da wata damuwa sai ya dunga fassara musu.Babu ranar da Najmiy baza tayi kukan rashin iyayenta da dan'uwanta ba,su mai martaba kuwa sai kaga suna rarrashinta,zuwa yanzu tasan meh kalmar 'haquri' yake nufi don malaminta ya fassara mata shi da larabci,yace 'asifa' yana nufin 'Haquri' ayaren Hausa.Toh idan taji ana cewa yi hakuri ko kuma sorry tasan lallashinta akeyi.
Aryaan Gaddafi kuwa babu labarinsa,duk wani lungu da sako na garin kano babu inda ba'aje ba amma ko mai Kama dashi ba'a gani ba,har gidajen radio aka bada cigiyarsa,infact harda gidajen radio na wasu garuruwa amma shiru kakeji babu labarinsa,Aryaan Gaddafi dan mutan Baghdad has gone,gone and gone forever😭.(Allah sarki Najmiy harna tausaya miki wallahi.)
Haka dai Najmiy ta haqura ta rungumi iyayen rikonta,amma akullum cikin addu'ar Allah ya bayyana mata Akhee dinta take da kuma yiwa iyayenta da kuma Ukhti dinta addu'ar samun rahamar ubangiji.
_*°•AFTER FIVE MONTHS•°*_
Acikin watanni biyar kacal Najmiy harta soma kwarewa da harshen Hausa da turanci,dake malamin jajirtacce ne kuma gwanin iya koyarwa,sosai mai martaba M.K ke yabawa da aikinsa,don zuwa yanzu Najmiy ta saki jikinta har tana zama tana hira dasu.Afari da 'Big Akhee' take kiran prince Faruq,wato 'Babban yaya',hayat kuma 'Small Akhee',Abida kuma 'big ukhti' wato 'babbar sister' sai kuma Hidaya 'small Ukhti',watanni biyar ne kacal ke tsakaninsu da Hidaya,don haka ita Najmiy dinne ta zama autar gida.
Toh ayanxu dake bakinta ya soma nuna da hausa,sai ta koma k'iran faruq da 'Yaya prince babba',Hayat kuma tace masa 'Yaya prince karami'.shine su Abida suma suka dauka suke kiransu da hakan.ita kuwa Abida da 'Yaya princess babba' take kiranta,ita kuwa Hidaya 'Yaya princess karama', duk kuwa sunayen yayi musu dadi sosai,shine ita kuma suka sanya mata sunan _*PRINCESS AUTA*_.
Kowa na qaunar Najmiy sosai don kallo daya ma zakawa yarinyar kaji kawai ta shiga ranka,yarinyace yar shekaru bakwai kacal amma kallo daya zaka mata ka rantse da cewar tayi sha biyu sabida ba laifi akwai girman jiki da kuma property😀.Malamanta biyu ayanxu,da malamin hausa da turanci,sai kuma malamin koyar da ita karatun boko da Mai martaba m.k ya samo mata wato 'lesson teacher',don anaso ta iya wasu abubuwan dakyau kafin asakata amakaranta.malamin dake koyar da ita hausa da turanci,shi din kuma ke koyar dasu duka karatun arabi harsu Faruq.
Bayan shekara daya kuwa,tuni hausar Najmiy ke fita dakyau kai kace jakar kano ce😀,turancinta shima ba laifi yana tafiya fluenty duk da cewar ba gama kama bakinta yayi ba,amma still tana kokartawa.Tuni aka sakata ah 'Al-amin International school' wanda makarantar dasu Faruq ke zuwa kenan,bayan an mata wasu gwaje-gwaje aka tabbatar da cewar lallai yarinyar akwai ilimi,shine suka bata Jss1 direct,yan'uwanta sunyi murna sosai,hidaya kuwa kuka ta saka wai ya za'ai princess auta ta wuceta ah aji,dake ita yanzu ne take pri5,toh shine mai martaba ya saka aka mata tsallake zuwa Jss1 din dake itama din akwai kwakwalwar daukar karatu irin _my janaf😉_ amma ya sanya aka raba musu aji don kada su hade suta wasa.Faruq shekarunsa ashirin kuma yana final year,Hayat kuwa shekarunsa 18 ah Ss2, Abida kuwa 13 ah Jss3,hidaya kuwa kamar yadda na fada afarko tsarar Najmiy ce.
Akullum idan ta dawo makaranta sai kaga ta hada kan yan'uwanta kamar yadda Akhee dinta ke musu ita da Yumna ukhti dinta,ta shiga koyar dasu abubuwan da aka koyar da ita aranar,su kuwa sai kaga suyi ta biye mata,hatta larabci tana koyar dasu,kuma ba laifi suna dan daukawa.Bayan ta gama dasu sai taje fada wajen Abba mai martaba,don ita dashi Five & six ne,yana mugun ji da ita haka ma yan fadar suna mugun sonta da kuma son sauraren hirarta da mai martaba.
Ita da Hayat kuwa wani irin muguwar shaquwace ta shiga tsakaninsu,tasu tazo daya,baya abu idan bata,kai ko abincine zaici tare suke ci ah plate daya,sai kaga yace azuba musu abincin ah plate daya da princess auta,karatu ma tare suke bitarsa,Mai martaba ya lura acikin ya'yansa Hayat da kuma Najmiy sunfi bada himma da kuma jajircewa wajen karatun boko da kuma arabi,shiyasa sukayi wa sauran fintikau acikin xuciyarsa.
_*°•вayan ѕнeĸarυ нυdυ•°*_
Bayan shekaru hudu,tuni Faruq ya kusa kammala karatunsa ah dan fodio University sokoto (Udus),ah inda yake karantar 'Political Science' don burinsa shine ace watarana ya zamo dan siyasa,shi kuwa Hayat yanzu yake level 3 dinsa ah federal university of technology minna,ah inda yake karantar 'Chemical engineering ',sabida Najmiy ne kawai yaki zuwa karatu awani gari.suma matan kowacce has been promoted to the next class.Najmiy da Hidaya an zama yan matan ss1,bama kamar Najmiy wacce tayi saurin girma kamar wacce ake baiwa taki kullum.She has become a woman with the full option😀,ga wani uban kyau data k'ara tatsowa,kai abin dai ba'a magana,sai dai kawai ace 'Tubarkallah masha Allah'
Watarana Hayat da kuma Najmiy na bitar karatunsu ta makarantar boko acikin filin shaqatawar gidan,bayan sun kammala ta masa sallama,harta juya zata tafi sai kawai taji Hayat ya rike mata gefen hijab.
Da sauri ta juyo tana dubansa,idanuwansa sun kada sun koma jajawur dasu,cike da tsoro tace"Yayah prince karami lafiya dai ko?ko wani laifin na maka?"
Dan murmusawa yayi kana yace"Yes Najmiy kin min laifi don zuciyata kika sace,tun farkon zuwanki nan gidan naji kawai ina jin wani abu agame dake amma ban gane cewar sonki nake ba sai da muka soma samun kusanci da juna,Najmiy nasan cewar ke din yarinyace kankanuwa har yanzu,You are juz 12 amma kina da girman jiki kamar yar 16years,naso boye abin acikin zuciyata har sai nan gaba wanda asannan kin kara wayau,amma I can't,ina tsoron kada wani yayi min shigar sauri shiyasa na gaya miki tun yanzu don kisan dani,wallahi tallahi Hayatudden M.K bahago loveѕ you alot,Najmiy ina sonki matuka,don Allah karki so wani bayan Hayat......... "
Bai gama maganarsa ba kawai ta fizge hannunta tayi cikin gida jikinta na kyarma,shi kuwa blow yakaiwa iska,kana ya lashe lips dinsa na kasa da harshensa,Faruq kuwa daya dawo hutun makaranta,ashe yana can tsaye yana hangosu daga nisa,hijabinta kawai da Hayat ya rike ne kawai ya tabbatar masa da zarginsa akan Hayat din ayau ya zamo gaskiya.
Azuciye ya soma takawa zuwa inda Hayat yake da sauri-sauri kamar zai tashi sama,duk inda ya gifta zubewa ake ana kwasar gaisuwa "Allah ya taimaki yarima mai jiran gado."
Shi kuwa Hayat ko kadan bai lura da tahowarsa ba don dukar da kai yayi kasa yana tunano abinda ya gudana ayanxu.Ji yayi Kawai an fizgi hannunsa aka mikar dashi ana jansa.
Idanuwansa ne suka sauka kan gefen fuskar Faruq wanda ko kallonsa baiyi ba sai jansa kawai yake.
"Yayah prince meye haka?idan wani laifin na maka ai kamata yayi kamin fada anutse bawai ka fizgi hannuna kana ja haka ba kamar wani dabba,haba wannan cin mutuncin da meh yayi Kama?wani irin shit kega agaban bayi ma?pls get ur filthy hands off me Yaya prince.... "
Ko ci kanka Faruq baice masa ba illa cigaba da jansa da yakeyi da karfi,shi kuma Hayat din na biye dashi da sauri-sauri ayayin da yake zuba masa surutu akunne.............
_*тoғa нayaтυ ĸa deвo rυwan daғa ĸanĸa😁*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
💥 ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*❄️(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)❄️*
**ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑**
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*°ՏɑժɑմƘɑɾաɑ ցɑ Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα°* __________________________________
_*°•wannan ѕнaғιn naĸυ ne мoмy zιl,υммυl мeenal da ĸυмa мaмan ĸнaυѕar,ιna ѕo ĸυ ѕanι cewar нaғnan тana мυĸυ ѕo мaι cιĸe da dυмвιn qaυna❤•°*_
💥
*Թɑցҽ 7* Faruq bai saurarawa Hayat ba har saida ya sadasu da dakin baccinsu,suna shiga ya jefar dashi ayayin da shi kuma ya juya ya sanyawa kofar dakin nasu key.shi kuwa Hayat tangal tangal yayi zai fadi,toh dayake shi din jarumin jarumai ne,sai yayi kokari ya rike kansa.
Ya juya yana duban wan nasa xuciyarsa na tafarfasa kamar danyar ganda,yace"Wai Yayah prince meye hakan?what's the meaning of all diz bullshits?wani laifi nayi da har yakai girman wannan cin fuskar daka min?iyyeh tambayarka nake...... "
Ji kake tassss! Faruq ya kwasheshi da wani wawan mari wanda har saida yaga wasu shining stars⭐ na blinking.
"Kayi gaggawan kiyaye harshenka da irin kalaman rainin da kake jifana dasu,that slap was simply a reminder to tell you dat am ur elder one and not ur junior neither ur mate...... "
Murmushi Hayat yayi tare da shafa fuskarsa inda aka watsa masa marin,yace"Wow rana ta farko da Yayah prince ya taba daga hannu ya mari k'aninsa wanda yafi so duk duniya,ban san dalilin wannan rashin mutuncin da kake shirga min ba amma kuma bai kamata hakan takai ga mari ba,anyway am grateful buh seriously the slap was kinda hot Prince Faruq Bahago...... " Ya sakar masa wani killer smile amma axuciyarsa shi kadai yasan irin takaicin dake cinsa.Shi kuwa Faruq jikinsa ne yayi sanyi qalau,meyasa yayi hakan?meyasa zai daga hannu ya mari dan'uwansa akan abinda bai tabbatar ba?
Kallon kwayar idanuwan Hayat yayi daya tsura masa ido yana jifarsa da kallo mai cike da ma'anoni iri iri.Duk da hakan kuma yana iya hango true 'love & affection' kwance cikin k'wayar idanuwan Hayatun wanda babu tantama it's for Najmiy Gaddafi.
"Meye dalilinka na rik'ewa Najmiy hijab dazu sannan kuma meye ka fada mata wanda har ya sanya ta fincike hijabinta tayi cikin gida da gudu?"
Wani irin malalacin dariya ya fashe dashi wanda yafi kuka ciwo,yama maida Faruq wawa wanda hakan ya sake fusata Faruq din. "stop laughing like a mad man and answer my question....... "
Wayyo!haqiqa kalmar 'mad man' yayi nasarar soya xuciyar Hayat,amma baice komai ba illa tamke fuska da yayi kamar ba wanda shine ya gama k'yak'yatar dariyar ban haushi ba.
Yace"Ohh! now I see,was dat the reason why you treated me like a coward in the presence of those servants out there?well na fada tarkon so ne,prince Hayatudden freaking m.k Bahago is inlove with Princess auta Najmiyya Gaddafi.... " Ya fadi hakan ne with full confidence babu alamun tsoro atattare dashi.
"Shut the hell up! Hayatudden Bahago,ain't you ashame of urself?kai baka ji kunya ba?yarinya kankanuwa kamar Najmiy wacce ko gama sanin kanta batayi ba itace kake furtawa kalmar so?ta gane meh acikin soyayyar?look,tun ba yau ba na dade da gano take-takenka akanta ta hanyar shisshige mata da kake yawan yi which is earnestly out of bound,amma naki amincewa da zargin da xuciyata take akanka agame da hakan,nace kila kawai ba sonta kake ba,shaquwace kawai ta yan'uwantaka,amma ayau zargina akanka ya tabbata gaskiya,ni ban hanaka sonta ba amma meyasa baka bari harsai ta dan kara girma da wayau ba kafin ka furta mata wannan kalmar?kai infact! Kai dinma har guda nawa kake da harka soma tunanin soyayya in banda iskanci irinta 'ya'yan zamani?You are juz 22 fa Hayat?ko ni da nake da shekaru 24 wallahi yan mata ma basa gabana for now,burina ayanzu na samu na kammala karatuna lafiya qalau,naje service dina,na kuma samu aikin yi kafin na nemi matar aure,donni wlhy babu ruwana da wata yarinya ayanzu tazo ta yaudareni ko ni kuma na yaudareta,arabu ana dibar albarkar juna.......... "
Hayat ya tari numfashinsa"Wannan kuma kai kakesowa kanka wannan tsarin,da kake jifana da maganganu,toh ni din ba dan'iska bane da nake shirin lalatata ba,nadai furta mata ne don tasan da zamana amatsayin mai sonta kafin wani yayi min shigar sauri harya sami wani gurbi acikin xuciyarta............... "
"Rufemin dirty mouth dinka anan,idan har da gaske din sonta kake tsakaninka da Allah toh ai kamata yayi ka sami Abba mai martaba wanda shine uban rikonta kace masa _*KA GANI KUMA KANA SO*_,don haka amaka kamun kafanta,amma furta mata kai tsaye da kayi sam bai dace ba,kai look daga yau sai yau,ina son ka fita aharkarta kabar yarinya ta maida hankali kan karatu,karka sake ka raba mata hankali gida biyu........ "
Azuciye Hayat yace"Ban gane yaren wai in fita harkarta ba,ni da qanwata kuma shine ake kokarin yimin iyaka da ita?"
"Toh ai gani nayi kamar baka dauketa kamar qanwartaka ba,tunda har zaka iya tsayawa ka kalli cikin kwayar idanuwanta sannan ka furta mata kalmar 'so' awannan yan kankantar shekarun nata,In banda girman jiki ma da Najmiy take dashi ai tsarar Hidaya ce,Hidayar ma ai tama dan girmeta,don dai kawai ita bata girma ne shiyasa ake ganin kamar Najmiy ce babba,yanzu idan wani yayiwa Hidaya hakan zakaji dadi?I am very pretty sure dat saika kusan ganin bayansa......... "
"Yayah Prince kalamanka suna nemar wuce limit dinsu..... "
Da sauri Faruq yace"Amma hannuna yafisu sauri..... "😂 (Hayat kabi ahankali kada Faruq din sahiba ya mazgeka anan😁)
Murmushi Hayat yayi kana yace"Kada ka kuskura ka kaini bango.... "
"Inma na kaika zaka dawo da baya da kanka ne,na dai gaya maka ka fitar ahanyar Najmiy,karka batawa yarinya rayuwa,Najmiy amanar Allah ce agaremu,karka kuskura ka yaudareta da soyayyar k'aryarka Hayatu,ina baka shawara ne don wallahi hannuna yafi kalamaina saurin aiki,na barka lafiya Yarima karami..... "
Ya juya ya bude kofa yasa kai ya fice fuuuu! Kamar kububuwa,Hayat kuwa wani dunkulen bakin ciki ne ya tokare masa qahon xuciya,meya shiga cikin kwakwalwar dan'uwan nasa ne da har yake jifarsa da zazzafar kalamai haka?Ayau shi Faruq ke yiwa kallon dan'iska kuma mayaudari?har yake ce masa kada ya kuskura ya b'ata rayuwar yarinya?
Tuni hawayen bakin ciki suka soma shatato masa saman kunci don shi harga Allah ne yake son Najmiyya Gaddafi,sonta har cikin jinin jikinsa yake jinsa,shi kawai yayi saurin fad'a mata ne sabida kada wani can daban ya dauke mata hankali.zubewa yayi saman wata two seater tare da dafe kansa da hannayensa bibbiyu,yama rasa tantance abinda ke masa dadi acikin duniyarsa.
**** Faruq kuwa yana fita fadar mai martaba ya nufa zuciyarsa ah dagule,yana shiga kuwa ya tarar babu kowa acikin fadar sai dogarai biyu da kuma mai martaba wanda ke hakimce kan kujerar sarautarsa.
Samun wuri yayi ya zauna tare da rike Kansa da hannayensa bibbiyu,hankalin mai martaba ne ya daga ganin yanayin dan nasa wanda kana gani kasan yana cikin damuwa ne. Ahankali yace"Umari meya faru na ganka cikin damuwa?wani abin aka maka acikin gidan?
Dakyar ya iya cewa"A'ah babu abinda aka min" ya fada ba tare da ya kalli inda mai martaba yake ba.
Murmushi mai martaba yayi kana yace"A'ah Faruq ba haka yanayin d'an nawa yake ba,duk da cewar kai din miskili ne amma kana da faram-faram da mutane,yanxu Umari ashe har akwai ranar da zatazo da har zaka iya boyemin damuwarka ka barwa cikinka kai daya?iyyeh Umari tambayarka nake?"
Ahankali ya furta"A'ah Abba mai martaba ka gafarceni..... ",Faruq ya dubisu Jabir(dogari)yace"Ku dan bamu wuri jabir zamuyi magana."
Zubewa sukai akasa sukace"Allah ya taimaki Yarima mai jiran gado,agama lafiya..... " suka fice,asannan ne ya juyo ga mahaifin nasa ya kora masa bayani.
Jikin mai martaba ne yayi sanyi qalau,kuma haqiqa zancen yayi mugun girgizashi,duk da cewar shi karan kansa ya dade yana zargin Hayat akan cewar kamar son Najmiy yake sabida irin muguwar sabon da sukayi,amma still bai taba tsammanin cewar irin wannan ranar zata zo ba,shifa tun zuwan Najmiy gidan ya kudurta aransa cewar insha Allahu Faruq zai baiwa aurenta don ya tabbatar da cewar zai rike masa amanarta kuma bazai taba barinta tayi kukan maraici dede da minti daya ba,don Faruq mutum ne mai sanyi hali,haquri da kuma tausayi,uwa-uba kyautatawa,sab'anin Hayat yana da zafi sosai kuma ga saurin fushi,sam bashi da haquri kamar zawo yake,tun yana karaminsa ya taso da wani irin mugun hali,idan har ka masa wani abinda ransa baiso ba toh kuwa saiya rama,haka kuma idan har yana son abu toh kuwa kota halin ƙaƙa ne saiya sameshi,ahalin yanzu kuwa rikici babba ne ke shirin kunno kai cikin royal family din don agaskiya mai martaba baya jin zai iya baiwa Hayat auren Najmiy sabida ko kadan basu dace ba,Najmiy zata cutu sosai idan ta auri Hayat,yana hango mata kukan maraicin da zata sha bayan ta aureshi,shi kuma bazai taba so hakan ta faru ba don Najmiy amanar Allah ce agaresu shiyasa yakeson aurar da ita ga nagartaccen namiji wanda zai kula da ita kamar Faruq.
Daga murya yayi ya kira sunan Jabir,nan da nan kuwa sai gashi ya iso ya zube akasa"Allah yaja da ran mutumin talakawa gani gareka ya shugabana...... "
"Maza kuje ku taho min da Yarima Karami,ace masa ina nemansa da gaggawa yanxun nan kuwa..... "
"An gama ranka shi dade...... " ya Mike ya fice don isar da sakon mai martaba.
_*Tofa my fiful yau ake yinta,wayyo Hayat😭 wallahi harna tausaya maka*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
{Onward together} *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
💥
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαи¢тι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY:*
*°ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα*° ____________________________________
💥
*Թɑցҽ 8⃣*
Najmiy kuwa tana shiga b'angaren Haj.Babba taji wani uban kuka ya taho mata,sam bata lura da Haj.Babba da kuma Haj.karama dake zaune afalo ba,sai kuma ƙuyangun dake durkushe agabansu suna musu hidima,masu firfita sunayi,haka kuma masu tausa nayi.ko lura dasu batayi ba dake makeken falo ne,ta nufi dakin baccinsu da gudu tana 'yar shessheƙa.
Haj.karama ce ta soma hango bayanta tana wucewa zuwa daki da dan gudu-gudu.Cike da tashin hankali ta dubi Haj.Babba wacce bata masan abinda ke faruwa ba sai aikin baiwa wata ƙuyangi order take dake mata tausa.Tace"Yaya kalli auta can ta shigo da gudu kuma kamar ma kuka take... " Agigice Haj.Babba ta dubeta tace"Ina autar take?"
"ta shige daki.. "acewar Haj.Karama
"maza Maymunerh tashi muje mu dubota nidai Allah yasa lfy dai... " Haj.Babba ta fadi hakan tare da mik'ewa at once,suka sallami kuyangu,kana suka nufi hanyar dakin da Najmiy ta shige da sauri saurinsu.
*** Bawan Allah kuwa Hayat yana nan zaune dai inda Faruq ya barshi,zuwa yanzu hawayen ya daina zubo masa,sai saukar da numfashin da yake tayi da karfi,acikin wannan halin ne su Jabir suka shigo suka riskesa,acikinsu babu wanda ma ya lura da yanayin da yake ciki don suna shigowa ko hada idanuwa dashi basuyi ba suka zube ak'asa,kafin Jabir yakai ga magana tuni yaji Hayat yayi saurin katse masa hanxari"Jabir wai sau nawa ne zan gaya muku cewar ku dena zub'e min ak'asa?karfa ku manta dani daku duk daya muke awajen Allah,wanda kawai yafi wani matsayi awajensa shine wanda yafi tsoronsa,kuma ko ba komai ai ni din k'anin bayanka ne na nesa ba kusa bama,don Allah ku daina bana so,pls get up immediately.... "
Allah sarki!ta inda kuma suke son Hayat kenan,sam bashi da ganin kansa azuwan shi din wani ne,infact yama daukesu kamar yan'uwansa ne.
Jabir yace"Allah ya taimaki jarumin jarumai,amatsayinka na dan sarki ya zama dole kaima mu girmamaka,don haka kayi haquri bazamu iya dainawa ba...... "
Bai tankashi ba,ya dauki ruwan faron dake gabansa,ya balle marfinta,sai daya furta"Meke tafe daku yakai amintaccen Abba mai martaba?" kafin yakai bottle din bakinsa.
Jabir yace"Allah yaja da ran Yarima Karami,ga sako zuwa gareka daga mai martaba,yace yana nemarka da gaggawa..... " Da sauri ya cire bottle din daga bakinsa,ruwan kuwa ya kwareshi sosai wanda ya janyo masa wani mugun tari har idanuwansa sukai jajawur,duk kuma adalilin tashin hankalin daya shiga ne,hakan na nufin Faruq yakai kararsa ne koko menene?don fitarsa kenan baa wani jima ba sai ga dogarai wai mai martaba na nemarsa da gaggawa kuma yanxun nan.
Dogarawan kuwa sai sannu suke ta masa ayayin da yake ta aikin gyad'a musu kai alamun amsawarsa kenan.Can ya dubesu cike da faduwar gaba bayan tarin ya sakeshi yace"Jabir kuje gani nan tahowa... "
"A'ah Yarima karami mai martaba yace kafarmu kafarka. " Gabansa ne ya tsananta faduwa jin furucin Jabir,atake anan ya sake tabbatarwa kansa da cewar lallai kararsa Faruq yakai.
Mik'ewa yayi ya shige gaba yace"ku muje... " suka take masa baya da sauri sauri.
** Gabansa ne ya karashe tsinkewa ah sa'ilin da sukayi ido hudu da mai martaba wanda se faman jifarsa yake da wani irin mugun kallo,kana iya cewa ma kashe masa wani Hayatun yayi.Shi kuwa Faruq kansa ya saddar kasa alokacin daya jiyo takun tafiyar Hayat,ko kadan baya son su hada idanuwa.
"Barka da warhaka Abba mai martaba,sakonka ya riskeni don haka gani gareka Allah dai yasa lafiya.... "
"Ba lafiya ba..... "acewar mai martaba cikin hargowa.Hayat baiyi mamakin jin furucinsa ba don dama can jikinsa ya bashi cewar Faruq ne ya kawo kararsa,watakil k'arya da gaskiya ne ya fad'a masa.
Mai martaba ya sake cewa"kana jina ko?nace ba lafiya ba,meh ka gayawa Najmiy dazun?"
Murmushin takaici Hayat yayi kana yace"Abba mai martaba cewa nayi ina sonta ko kuwa yanzu ya zama laifi ne mutum yace yana son wani?"
"Rufemin baki anan mutumin banza da wofi,ita ya kamata ka gayawa hakan ko ni?meyasa baka sameni ka nemi izinin tunkarenta ba ko kuwa zamanka take agidan ne?"
Hayat na kokarin magana tuni mai martaba ya rigashi"Shhhhhhh! yi min shiru anan bana son jin komai daga gareka,ka bude kunnuwanka ka saurareni dakyau,daga yau sai yau bana son ka sake keb'ancewa da ita don Najmiy amanar Allah ce agareni,idan na kuskura nayi sakaci har rayuwarta ya gurbata toh kuwa Allah bazai tab'a yafemin ba,Hayatudden Bahago bazan tab'a baka auren 'yata Najmiyya Gaddafi ba,Najmiy marainiyace don haka yasa nakeson na aurar da ita ga namiji nagartacce wanda nasan zai kula min da ita,wanda kuma nasan bazai taba bari tayi kukan maraici ba dede da minti daya,amma bakai ba Hayat,kaje na yarje maka ka zab'o duk wacce ta maka afadin duniyar nan,muddin dai tana kai kanta k'asa tofa zan aura maka ita,amma ba Najmiy ba,kuma daga yau sai yau na haramta maka k'ebancewa da ita,wannan shaquwar kuma arageta bana so,idan kuma aka kuskura aka sab'a umarnina tofa zanyi hukunci da kuma daukar kwakkwarar mataki,don haka kayi gaggawan yakiceta daga cikin xuciyarka... "
Gabaki daya network din jikin Hayat ya tsaya cak! ya daina aiki,haka ma dukkan jijiyoyin jikinsa sun tsinke da kalaman mai martaba,gwiwowinsa sun sake,gaba daya kawai yaji duniyar tana juya masa,dakyar ya budi baki yace"Abba mai martaba don Allah karka sa na soma tunanin cewa bakai ne ka haifeni ba,don aganina da kuma iya sanina babu mahaifin da zaiso ganin ya salwantar da farin cikin dansa da gangan,fisabilillahi! Menene aibuna don kawai nace ina son Najmiy?don Allah ba abin farin ciki bane ma don ina son na taimaka mata ita da bata da asali ma?kuma wanene yace ni din bazan iya share mata kukan maraicinta ba?haba Abbana meyasa?
Fashewa yayi da wani kuka mai tsuma xuciya,da sauri ya isa ga Mai martaba ya zub'e agabansa tare da kamo kafafuwansa,yace"Don Allah Abba mai martaba idan wani laifi na maka wanda ni ban sani ba,toh don Allah ina rokanka daka yafemin dan'adam ajizine,amma pls karka hanamin samin farin cikina,wallahi ina son Najmiy,she really captured my heart starting from day one,kuma itama nasan tana sona,wallahi ku k'irata ku tambayeta nasan zata fad'a muku gaskiya...... "
"Hey! Young man karkayi tunanin cewar shaquwar dake atsakaninku so ce,sam abin ba haka bane,shaquwa daban haka kuma so daban yake,don haka bana tsammani Najmiy sonka take kamar yadda kai kace kana sonta.... "Faruq ne ya fadi hakan.
Hayat ya dago yana dubansa,cike da tsanarsa yace"Ai dama nasan kaine ka hada komai,ka shimfidawa Abba mai martaba k'arya da kuma gaskiya,waya sani ma ko kaima son Najmiy din kake shiyasa kake son ka hada bomb?"
"Allah ya kiyaye,tirr da wannan negative thinking din naka,Najmiy kallon qanwar da muka fito ciki daya nake mata,kallon Hidaya da kuma Abida nake mata,kai ko zan nemi budurwa ma ni bazan taba nemar yar kankanuwa kamar Najmiy ba,haba brother wat You are trying to do is simply child abuse.... "
Haqiqa kalmar 'child abuse' ta daki Xuciyar Hayat don har runtse idanuwansa yayi gam,kuma agaskiya Umar ba wai son Najmiy yake ba,shi kawai gani yake Najmiy bata kai matsayin da har zata soma soyayya ba (waya gaya maka?)
Mai martaba kuwa saddar dakai yayi kasa yana saurarensu,yama rasa ta cewa,shidai gaskiya acikin 'ya'yansa yafi qaunar Hayat amma bazai iya bashi Najmiy ba don sosai zata cutu da halayyarsa bayan aure,wanda ko kadan bazai taba so hakan ta faru ba.
* Acan daki kuwa,su gimbiyoyin ne suka tasa Najmiy agaba akan tayi musu bayanin abinda ya sakata kuka,dakyar ta hadiye kukanta kana tace"Wai ya za'ayi ace Yaya Prince karami ya kalli cikin k'wayar idanuwana yace yana sona?shin ya manta cewar ni din k'anwarsa ce?ko kuwa haka kukeyi anan?ko kuma nace shin haka kukeyi ah al'adarku wa yace yana son k'anwarsa da soyayya?"
Jikin Haj.karama ne yayi sanyi qalau da jin wannan zance na Najmiy,ita kuwa Haj.Babba sosai abin yayi mata dadi na ganin za'ayi 'yar gida gida ne,haka ma su Abida abin yayi musu siga sosai.
"Abinda ya sakaki zubda hawaye kenan?" haka haj.karama ta furta sam babu ko digon annuri akan fuskarta,kai kawai Najmiy ta daga mata alamun eh. "Toh share hawayenki yarinya don nima ko kadan bana qaunar wannan hadin.... "
Cike da mamaki Haj.Babba tace"Haba Maymunerh lafiyarki kuwa?wannan wani irin zancen banza kenan?Najmiy ce fa?shine kike ambaton cewar bakya qaunar hadin nan?toh gaskia ki sake tunani Maymunerh don nidai banga dalilin dazai saka kiyi irin wannan furucin ba.... "
"Yaya akwai dalili... "acewarta
Haj.babba tace"Wani dalili kenan?"
"ki bari anjima zamuyi magana... "
Ta maida kallonta ga Najmiy tace"Ke ina Hayatun yake?"
Da rawar murya Najmiy tace"Na barosa ah inda muka saba bitar karatunmu..... "
Fuuu! ta mike tayi hanyar kofa,Haj.Babba na mata magana ko waigowa batayi ba balle asa ran zata tankata,da hanzari Najmiy tabi bayanta tasha gabanta,kamo hannayenta tayi tace cikin muryar kuka"Ummi khuddha basat (take it easy),don Allah na rokeki karki masa fada,kedai ki sake tunatar dashi cewar Najmiy qanwarsa ce,don haka bai kamata ace ya furta Kalmar so agareta ba...... " kala bata ce mata ba ta rab'a ta gefenta ta wuce.
Haj.Babba wacce fitowarta daga daki kenan tace"Ke kuwa Najmiy in banda abinki ai akwai aure atsakaninki da Hayat,Hayat ba shaqiqinki bane,ba ciki daya kuka fito dashi ba,don haka akwai aure tsakaninku..... " she was suprised sabida ita bata taba sanin cewa ana iya auran gida gida bama,kuma ita ta dauki su faruq kamar 'Akhee dinta ne wanda suka fito ciki daya.
Haj.karama ta janyo hannunta suka zauna saman kujera,kana ta shiga warware mata komai dalla dalla harta fahimta,sai dai har yanzu mamakin bai bar fuskarta ba.
_*Toh yanzu bari mu koma fada mu dubo wainar da ake toyawa,sannan kuma meh Gimbiya Maymunerh take nufi ne?kuma meh take shirin aikatawa?ku biyoni*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°* *°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATPADD:HAFNANCY*
*•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•*
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo🖊•°* ___________________________________
💥
*Թɑցҽ 9⃣*
Acan fada kuwa,rigima ce ko kuwa nace cin musu ce ta kaure sosai tsakanin Faruq da Hayat,shi Hayat cewa yayi sai Faruq din ya gaya masa hadisi ko kuma ya kawo masa ayar da akace nemar mace kamar Najmiy child abuse ne,shi kuwa Faruq ya kuke sai masa bayani yake akan tsarin bayahude.
Mai martaba wanda keta sauraransu tun dazu ne ya doka musu wani uban tsawa,yace"Ku min shiru mutanen banza da wofi,kunbi kun cika min kunne da shashancinku na banza.... "
Ya dubi Hayat yace"Kai kuma Hayat ko kadan banji dadin furucinka dakace wai Najmiy bata da asali ba,haqiqa kayi daƙiƙanci anan,toh ina son ka sani cewar ni awurina kallon 'yar cikina nake mata,Najmiy tana da cikakkiyar asali,kuma zan tsaya kan tsayin daka koda kuwa kowa ya gujeta ne,toh ni zanyi kokari naga na zame mata gatanta wanda zatayi alfahari dashi fid-dunya-walakhira,kuma koda wasa ka sake ka sake maimaita wannan kalmar,toh wallahi sai nayi mugun sassab'a maka,da fatar kaji abinda na fada?"
Cike da nadama Hayat yace"Eh duk naji abinda ka fada Abba mai martaba,don Allah ka gafarceni subutar baki ne... "
** Haj.Karama kuwa tana fitowa ta aiki wani dogari da yaje ya k'irawo mata Hayat ah inda Najmiy tace yake,da sauri dogarin ya zub'e agabanta yace"Ranki shi dade,Yarima Karami yana fada.... "
Bata bari ta k'arashe jin zancensa ba ta nufi hanyar fadar,har ƙuyangu sun soma take mata baya sai kuma tayi saurin dakatar dasu.Tana shiga cikin fadar kuwa ta hango Hayat durƙushe gaban mai martaba yana kara rokansa akan yayi haquri ya bashi auran Najmiy,shima Faruq din ya saka baki don bai tab'a tunanin hakan ne zai kasance ba da kuwa bai kawo kararsa ba,shi kansa bai san dalilin daya sanya mahaifin nasu yace bazai baiwa Hayat auren Najmiy ba,shifa kawai yazo ne yace masa ya kirawo Hayat ya masa fada kan ya fita hanyar Najmiy don bata kai matsayin da har zata tsaya tayi soyayya ba ayanxu,ya bari sai ta dan kara wayau da kuma girma,sai kuma gashi mahaifinsu yace kwata kwata ma wai bazai bashi auranta ba.
Babu b'ata lokaci ta isa ga Hayat fuskarta babu ko digon annuri akansa,dagoshi tayi ta mikar dashi tsaye,shi kuwa mutumin naku yana hada idanuwa da ita,ya soma sakin murmushin jindadi,don atunaninsa itama zancen ya isketa ne shine tazo ta tayashi roƙan mai martaba akan yayi haquri ya bashi Najmiy.
Babu zato babu tsammani kawai Hayat yaji saukar wani lafiyayyan mari saman kuncinsa,bai gama shanye mamakinsa ba kuma yaji saukar wani adayan gefen kuncinsa,har ta daga hannu zata k'ara masa wani,sai kawai taji an rike mata hannun,Faruq ne,Yace"Haba Haj.karama meh kuma yayi zafi haka da har yakai ga mari?"
"Cikan hannu... " shine kawai abinda ta iya furtawa da k'arfi,da sauri Faruq yayi kamar yadda ta bukata tare da jaa da baya da sauri sabida irin tsantsar bala'in daya hango shimfid'e acikin ƙwayar idanuwanta.Juyawa tayi ga Hayat wanda tsananin mamakinta ma ya hanashi furta komai,nunashi tayi da 'yar yatsa tace"Don qaniyarka ni Maymunerh ni zaka janyowa abin ƙunya da kuma abin fada agari?ka rasa wacce zakace kanaso sai wacce ba'a san asalinta ba?toh wallahi da sakel,bada yawuna ba kuma ba'a cikin wannan masarautar ba,don haka maza ka gaggauta binne wannan zancen nadai gaya maka tun wuri don kada matakin da zan dauka agareka yazo bai maka dadi ba.... "
Har ta juya zata wuce,da sauri mai martaba yace"Maymunatu maza dawo nan.... " cak! ta tsaya ah inda take,sai data kwashi kusan daƙiƙu goma kafin ta juyo ta soma dawowa da baya zuwa gareshi.Rissinawa tayi har k'asa tace"Gani ranka ya dade... "
Zuba mata idanuwa mai martaba yayi ba tare da ya furta komai ba,sai girgiza kansa yake cike da tsananin mamakin jin furucin daya fito daga bakinta,gani yake kamar ba maymunarsa bace mace mai tsananin son mutane da daukar kowa nata ne,koda yake ai ba abin mamaki bane don dama can ance mutum tara yake bai gama cika goma ba,dama duk ƙyawun halayyarka tofa dole za'a samu wani b'angare naga mai muni.Toh ayau kuwa other side dinta Gimbiya Maymunerh ta gwada masa.
Gyaran muryarsa yayi daidai da shigowar Haj.Babba cikin fadar,shiru shiru taga haj.karama bata dawo ba shiyasa ta biyo sahunta.samun wuri tayi ta zauna ganin kamar magana muhimmiyace akeyi acikin fadar.
Yace"Maymunerh yanzu na gama yiwa danki fadar wannan furucin da kikayi,sai gashi kema kin maimaitashi,maymunerh yau meya shiga cikin kwakwalarki ne da har ya sanya kikayi irin wannan furucin?Ayau Najmiy ce ta zamo mara asali?azatona kin dauketa ne tamkar 'yar data fito daga cikin cikinki,ashe tunanina akan hakan ba gaskiya bane,tunda gashi ayau kin fito kin nuna min cewar baki haifi Najmiy ba,baki dauketa kamar yadda kika dauki Hayatu ba,Najmiyya bata da gata,haka kuma bata da cikakkiyar usulin da har zaki iya bari danki ya hada jini da ita,toh ina son kisha kuruminki,ni Muhammadu bazan ma taba baiwa Hayatu auren Najmiyya ba sabida ko kadan bai cancanci abashi ita ba,don haka ki rubuta ki ajje cewa nina fadi hakan,maza kowa ya tashi ya bani wuri.... "
Haka kowa ya tashi ya fice jiki ah sabule,bayan sun fita kuwa haj.babba ta hau yi mata fada akan meyasa zatayi irin wannan furucin?meya shiga cikin kwakwalwarta ne?
Ko kala bata ce mata ba tayi b'angarenta.shi kuwa Faruq so yake ya baiwa Hayat haquri amma ko kadan bai samu damar hakan ba.
*** *°•Ah gurguje pls•°*
Mai martaba M.k bahago ya saka su dogarawa sanya ido sosai akan Hayat da Najmiy,har umarni ya bada akan cewa muddin aka ga sun keb'e toh ahukunta masa Hayat,don ya riga ya gargad'eshi akan kada ya kuskura ya sake keb'ancewa da ita,karatu ma yanzu idan har zasuyi tofa sanya dogarawa ake atsakaninsu,kwata-kwata babu maganar da take shiga tsakaninsu bayan na karatu.Hayat duk yabi ya rame ya kuma lalace,sam bashi da wani sukuni da walwala,kullum cikin kuka yake,gashi mahaifiyarsa ta juya masa baya don kawai yace yana son mara asali,Faruq ma tuni ya koma makaranta,haj.babba ce kawai take dan jansa ajiki sai kuma kannensa,itama tayi tayi da mai martaba akan ya gaya mata dalilinsa daya sanya yace bazai baiwa Hayat auran Najmiy ba amma fir! yaki don yasan zasuce ba wani dalili mai karfi bane,amma shi kadai yasan abinda yake hangowa nan gaba.itama Najmiy zuwa yanzu ta soma tausayin Hayat,gashi babu damar keb'ancewa dashi,kuma ita bata masan wainar da ake tauyawa ba acikin gidan,ko kadan bata san cewa mai martaba yace bazai taba baiwa Hayatun auranta bane,itafa duk wannan mutanen da aka sanya su dunga tsaronsu ita azatonta kawai bai dace suyi soyayya bane ashekarunsu,shiyasa aka sanya masu gadin da zasu dunga lura dasu aduk sanda suka k'ebance don karatu ko wani abin can daban.
_*jan нanĸalι na ғarĸo agareĸυ ιyayen yanzυ da ĸυмa ιyayen goвe,ĸυ daιna ѕanya dogon вυrι aranĸυ don вaĸυ ѕan мaι goвe zaтa нaιғar вa,gaѕнι yanzυ мaι мarтaвa мĸ yana neмar тaғĸa вaввan ĸυѕĸυre,da'ace yaвι ѕon zυcιyar danѕa ne da ĸυwa ĸoмaι dazaι ғarυ вaι ғarυ вa,waтaĸιla мa вayan aυre yana ιya canzawa тυnda нar yana ѕon najмιy dιn da gaѕĸe,aммa dogon вυrιn da yaĸe daѕнι aĸan ғaranтawa najмιy ѕнι ya нaιғar da ĸoмaι*_ мυje zυwa🏃
_*idan har na gamsu da comments toh kuwa kuna iya ganin update anjima kadan*_
*TAKU* *ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*°ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα°*
_*°•wannan page dιn naĸι ne ĸe daya мy najaтee мarυвυcιyar 'yarιмa ѕυнaιl',нaqιqa lιттaғιn na nιѕнadanтar daмυ,υвangιjι Allaн ya ĸara вaѕιra da kuma zaĸιn нand,ιna ѕo ĸι ѕanι cewar нaғnan dιnĸι тana мιĸι ѕan ѕo💕💕💕•°*_
*°•Intelligent writers Asso🖊•°* __________________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣0⃣*
_*вayan waтannι υĸυ*_
Zuwa yanzu Hayat ya soma fusata da gadin da ake musu,ba dama su zauna waje daya da Najmiy,sai gaka dogarawa nayiwa junansu signal alamun maza su matso kusa dasu,zancen soyayyar nan ne dai ba'a son suyita,shi yama fita harkan mahaifin nasa tunda harwa yau yaki sauraron maqigarsa(Mai martaba m.k Bahago wani irin mutum ne mai tsassauran ra'ayi,idan har yace haka yakeson abu,tofa babu wanda ya isa ya canza masa wannan tsarin,yana da kafiya akan abu sosai,Allah sarki duk fa akan baiwar Allah Najmiy yake kuntatawa dan cikinsa,don kawai ita ya faranta mata,ta samu tayi rayuwar farin ciki da kuma jindadi,(irinku sunyi karanci mai martaba m.k,Allah yaja da ran mutumin talakawa,amma ranka shi dade daka jaraba Hayat kila ya sauya halin saurin fushinsa dinnan da sauransu dai,dama ance sai kaga ta sanadin wani mutum ke canzawa daga wani halin da aka sanshi dashi.)
Haka ma mahaifiyarsa Haj.karama tace babu ruwanta dashi muddin bai fita ahanyar Najmiy ba.kannensa Abida da kuma Hidaya suma sun dan ja baya da Najmiy don aganinsu itace ke nemar tarwatsa family dinsu.zuwa yanzu Najmiy tasan wainar da ake toyawa wanda ko kadan bata ji dadin hakan ba,tausayin Hayat da take ji ya sanya har ta soma developing sonsa acikin xuciyarta,amma babu damar gaya masa,kuma ko ta gaya masan ma tasan mai martaba ba yadda zaiyi ba. Shi kuwa Faruq koda ya koma makaranta ya kasa samun kwanciyar hankali,gashi alokacin wani da wani ne ke rik'e wayar salula balle yace zai k'ira Hayat ya sake nemar gafararsa ko zaa dace wannan karon ya sauraresa.Allah-Allah yake semester tayi ta kare ya dawo gida.
Watarana Hayat da Najmiy suna bitar karatunsu as usual,gefen haqunsu da kuma damarsu masu gadinsu ne,bayan sun kare karatun,hayat ya dubesu yace"Wallahi yau fa sai dai ku min duk abinda zakumin amma agaskiya sai na gana da Najmiy.... "
Kan suyi magana ya kalli Najmiy yace _*"NAJMIYYA INA SONKI,SHIN KEMA KINA SONA?"*_
Kan tayi magana kawai yaji saukar dorina agadon bayansa,wani dogari ne wanda dama ya dade yana jin haushin Hayatu,yanzu gani yake its an opportunity ya koyawa Hayat hankali,Hayat bai damu ba,Hawaye cike fal da idanuwansa yace da d'an k'arfi"Najmiy kiyi magana karki ji tsoro,shin kema kina sona?"
Tuni Najmiy ta fashe da kuka ganin bulalar da aka sake tsula masa,wani dogari ne yayi mata alamu da ido wai ta tashi ta shige ciki,da sauri ta kwashi books dinta tayi ciki tana kuka.Hayat shima fashewa yayi da kuka mai tsuma xuciya bayan tafiyarta,ashe yanzu idan kace kana son wani ya zamo laifi?
Awannan ranar saida aka kaiwa mai martaba kararsa,ya kirashi ya tsassage masa yace ya fita aharkar Najmiy don ya riga da yayi mata miji ma amma bai fada masa cewar Faruq bane,ashe tun da dadewa suka kulla wannan zancen da sarkin kano,kan cewa Faruq zai baiwa auran Najmiy,toh shi ko kadan baya son canza magana arayuwarsa,shiyasa ya tsaya kan tsayin daka akan lallai fa Faruq zai baiwa ita.babu wanda yasan wannan kudirin nasa sai sarkin Kano.
Yanzu ma sam sam an hanasu zama wuri daya suyi karatu,azahiri Hayat yayi kamar ya haqura ne amma shi kadai yasan famar da yakeyi da xuciyarsa akan soyayyar Najmiy,kullum kamar k'ara masa sonta ake acikin zuciyarsa.Rayuwar Hayat na tafiya ne ba yabo ba fallasa,idan kuna hira dashi kaji can yayi shiru,tofa tunanin Najmiy yake,idan ka tambayeshi abinda ke damunsa,toh kuwa next thing hawaye ne zai biyo baya,yanzu Ma ya daina concentrating kan karatunsa,CGPA dinsa ma yayi kasa da yawa,wanda har ya sanya saida level adviser dinsu ya kirashi yake tambayarsa abinda ke damunsa da har yayi sakaci CGPA dinsa yayi low da yawa.
"Babu komai sir" shine kawai abinda ya iya furtawa.Zuwa yanzu ya soma hulda da abokan banza,don sosai suke mantar dashi rayuwar kuncin da yake ciki,sigarin nan ma Hayat har ya soma d'an tabawa da kuma codein,idan yasha shi yakan jishi ontop of the whole world ne,yakan mantar dashi damuwar da yake aciki.sai dai wani abin birgewa,sam baya hulda da mata,mace daya yakeso kuma itace 'Najmiy Gaddafi'.Mutum na farko daya soma noticing canjin halayyar Hayatun shine wannan dogarin daya fi tsanarsa wato mamman.
Watarana Hayat na dakinsa don zuwa yanzu ah boysquarters suke,tare yake da abokansa su hudu,'Spanzy', 'Roughcoin', 'Na babies','MD smart',sannan shi Hayat shine na cikon biyarsu wanda ake k'ira ayanzu da *'BADMAN'*😅.(chubby don't cry pls)
Sun baje ak'asa suna buga chachaa wanda su Roughcoin ne suka kawoshi aboye.Mamman dogari wanda yazo yin fitsari ah boysquarters ya jiyo yar hayaniya adakin Hayat,cikin sanda yaje kusa da kofar dakin,lekawa ne yayi ta window ahankali,warin sigari ne ya daki hancinsa,ai kuwa da sauri ya fice yaje yakai rahoto wajen sarki,akunne ya gaya masa.cike da tashin hankali mai martaba ya nufi boysquarters,ai kuwa yana tura kofar dakin ta kuwa budu,ya afka ciki,dukkanninsu babu wanda yayi tunanin cewar akwai wanda zai iya shigowa har ya riskesu acikin wannan halin musamman ma mutum kamar mai martaba.
Arud'e Hayat ya dubi roughcoin don shine ya shigo ak'arshe,yace"Kai banza dama baka rufe kofar bane?"
"Allah ne dai ya shirya tona asirinku ayau... "acewar Mai martaba cike da dacin rai.
Can ya sake cewa _*HAYATUDDEN*"_ nan da nan kuma sai ga hawaye ya zubo masa shaa! asaman kunci.Ya cigaba"Hayatu kaci amanata kuma kaci amanar tarbiyyyar dana baka,ashe haka abin yake?dan daka fiso shine ke sanyaka zubda hawaye?hayatu irin wannan kazamar rayuwar ne ka jefa kanka aciki?chacha acikin gidana?shan sigari?jibi sumar kanka ka canza masa Kala,haba shiyasa kodayaushe kake cikin saka hula,baka yadda ka fito waje ba tare da hula akanka ba,ashe dai kasan abinda ka aikata..... "
Ya tsagaita jin numfashinsa dake haurawa sama sama sabida tsananin b'acin ran da bai taba experiencing irinsa ba.Shi kuwa Hayat fashewa da kuka yayi cike da nadamar irin sabuwar rayuwar daya jefa kansa wanda hakan ya sanya mahaifinsa zubda hawaye akansa ayau.Abokansa kuwa kowa jiki ba kwari suka kashe sauran karan sigarinsu tare da jefawa cikin aljihun wandunansu,Spanzy ne ya karbi ta hannun Hayat ya kashe don shi yama kasa motsawa daga inda yake tsaye.wannan wani style ne irin tasu da suka sabayi,idan har wani babba ya kamasu suna shanta,ko kuma wani yana musu fadar Shanta,sai suyi saurin kashewa atare kana su jefar da karan ah aljihun wandunansu.
Roughcoin ya duka ya dauki kwalbar codein dake kasa,kana yayi wa sauran signal,ai kuwa da gudu suka rab'a gefen mai martaba,suna fita sukaci karo da dogarawan dake tsaye abakin kofa,wani irin dodging sukai musu suka arta aguje tamkar wasu karnuka.harsu dogarawan na shirin kwasa aguje su kamosu,suka ji mai martaba yayi sauri katse musu hanxari,yace"A'ah ku kyalesu sun tsira,yau ranarsu ce don haka babu hukunci,amma idan suka bari suka sake maimaita hakan acikin gidana tofa saina hukuntasu fiye da tsammaninsu,kai karma ku sake ku kara barin koda daya daga cikinsu ne ya tako cikin gidan nan,da fatar duk kunji abinda na fada ko?"
Zub'ewa sukai akasa sukace"Allah ya taimaki mutumin talakawa insha Allahu hakan bazata sake faruwa ba."
Yace"Dakyau kuma ina musu fatar shiriya.... "
Ya juyo ga Hayat wanda jikinsa ke aikin k'arkarwa non-stop kuwa,da sauri Mai martaba ya runtse idanuwansa don sosai tausayin Hayat ke dakar xuciyarsa na ganin irin kazamar rayuwar daya jefa kansa.
Da k'arfi yace"Jabir maza ku shigo ku dauki Hayat akaishi dakin horo,ayi masa bulala 20 masu ƙyau adalilin kawo abokan banza susha kayan maye acikin gidana,kaine zaka amshi hukuncinsu,sumar kansa dinnan kuma ah aske masa shi,ayi masa ƙwaryar molo,maza nace..... "
Da hanzari suka shigo su wajen biyar suka kamo Hayat yana dan turtujewa,yace"Abba mai martaba please please kayi haquri banason bulala,walhy na tuba Abbana,bazan sake binsu ba,nabar halaye don Allah kaban Najmiy ina sonta..... "
Tasss! Kakeji mai martaba ya kwasheshi da wani mahaukacin Mari,yace"Ahakan ne kakeson na baka 'yata bayan ka jefa kanka cikin wannan kazamar rayuwar?ada nayi tunanin sauya ra'ayi na baka ita amma halin dana riskeka aciki shi yasa zan fasa,bazan iya baka auran Najmiy ba,watarana idan kasha kayi tatul kazo ka jibgi 'yar mutane ko kama kasheta ba..... "
Cikin muryar kuka yace"Abba mai martaba waya jawomin fadawa cikin wannan kazamar rayuwar?ka tuna fa daga kai har Hajiya Karama kun bada taku gudummawar...... "
"Nace ku wuce dashi ko?kuma bayan kun gama ku kawoshi fada ..... " mai martaba ya fadi hakan da k'arfin gaske,da hanxari sukayi waje dashi amma still bakinsa bai mutu ba.
Cewa yake yana kuma nanatawa"Abba mai martaba kaine silar faruwar komai,kuma na tabbata gobe kiyama sai Allah ya tambayeka yaya ka rike amanar 'ya'yanka daya baka aduniya?meh kuma yasa ka salwantar da farin cikin Hayat da gangan?"😭😭.
Jikin mai martaba ne yayi sanyi qalau don yasan tabbas gaskiya ne Hayat ya fada,shima ya bada tasa gudummawar wajen jefa rayuwar dansa acikin wannan rayuwar.Mai martaba M.K mutum ne mai kafiya sosai kan abu,shifa xuciyarsa tafi kwantawa da auran Faruq da Najmiy.
Ko kadan bai yadda iyayen Hayat mata susan halin da ake ciki ba don sosai zasu daga hankulansu,komawa Fada yayi ya zauna jiran isowar Hayat cikin fadar.
_*wayyo нayaтυ ι don'т ĸnow тнe ĸιnd oғ eмpaтнy ι нave ғor yoυ😭😭,laвarιnĸa aĸwaι тaυѕayι ѕoѕaι,Allah ya ĸawo мaĸa мaғιтa cυz ι don'т lιĸe тнe ĸιnd oғ lιғeѕтyle daĸa jeғa ĸanĸa*_
_*мυje daĸιn нoro🏃*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°* *°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATPADD:HAFNANCY*
_*°•wannan page dιn мallaĸιnĸυ ne нιввaтυllaн ғanѕ groυp,janaғ ғanѕ groυp,yarιмa ѕυнaιl ғanѕ groυp & ιnтellιgenт wrιтer'ѕ ғanѕ groυp,нaqιqa coммenтѕ dιnĸυ yana ѕυмar danι,ιna ѕon ĸυ ѕanι cewar нaғnan тana мυĸυ тѕaғтaтaccιyar ѕoyayya,acιgaвa da gaѕнι ѕυya ѕaι ranar ѕallaн😉•°*_
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo🖊•°* ____________________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣1⃣*
Acan dakin horo kuwa,tuni aka isar da saƙon xuwar prince Hayat,akacewa malamin horo cewar ga Yarima Karami nan tafe ai ga laifin da mai martaba ya kamashi dumu-dumu yana aikatawa,malamin horo wato Idrisu duk yaji jikinsa ba dadi don tabbas Hayat mutuminsa ne,sosai suke dasawa da juna.Babu yadda ya iya illa mik'ewa ya dauki dorinarsa kakkaura mai baki biyu,ya shiga gyarata kafin zuwansa,don hukunci ya zama dole,don ma wai yana d'an sarki kenan shiyasa aka dan masa sassauci,wannan hukuncin da mai martaba m.k ya sanya ayiwa Hayat ba karamin dadi yayiwa mutane da yawa ba,don hakan da yayi shine daidai,ya kwatanta adalci,ya nunawa duniya cewa sam baya da son kai ko kadan,baiyi tunanin cewar ai Hayat dansa ne ba don haka bazai hukuntashi bisa laifin daya aikata ba,a'ah ya kwatanta adalci anan.
Mamman dogari shine gaba gaba,ayayin da sauran hudun ke rik'e da Hayat,shifa Mamman sosai abin ke masa dadi,ji yake tamkar ya xuba ruwa ak'asa yasha don murnar ganin za'a hukunta Hayat (Kunsan haka abin yake,kowa zaka ga da wanda jininsa ya hadu da,haka zalika akwai wanda jininsa bai hadu dana wani ba,toh hakan take ga Prince Hayat da kuma Mamman dogari.)
Suna shiga cikin dakin Jabir ya nufi Idrisu wanda ke tsaye yake jiran isowar Hayat.Sauran dogarawan kuwa ahankali suka zaunar da Hayat ak'asa wanda sai faman basu haquri yake tayi akan kada su bugeshi,abin dai gwanin ban tausayi.
Jabir ne ya danyiwa sauran dogarawan clapping 👏 sau biyu,duk suka dubi inda yake ah kusa da Idrisu,yace"Duk ku matso kusa.... "
Da hanxari suka isa gareshi don shine oganninsu gabaki daya,He has the final saying kuma dolene subi duk abinda yace,idan har ya kafa wata doka toh kuwa babu dogarin dake tsallakewa koda kuwa kana jin kai din wani shegen ne irinsu Mamman tofa dole ka lafar don Jabir ko kadan baya daukar ƙaniya.
Yace"Meh zai hana mu hade kawunanmu mu taimaki Yarima Karami?kowa anan yasan Yarima karima dai mutumin kirki ne kuma sosai yake k'yautata mu'amalarsa da mutane kamar dai mahaifinsa,shidai abarshi da saurin fushi,mugun zuciyar tsiya wanda har hakan ke sanya ko kadan bashi da yafiya idan aka masa wani abin da ransa bai so ba,amma apart from dat,sam sam Yarima Karami bashi da matsala,kowa nasa ne,don haka abinda nakeso daku shine,kar abugeshi,mu dan bada lokaci sai awuce dashi Fada,sai yayi acting kamar an bugeshin,koya kuka ce?"
Kowannensu ya gyad'a kai har Idrisu mai horo alamun amincewa,Cike da rashin jindadi Mamman yace"Amma dai kunsan Mai martaba yana iya gane cewar ba'a dakeshi bako?don haka nidai babu ruwana,haba ko bulala goma ne dai ayi masa gudun shiga cikin matsala..... "
Axuciye Jabir yace"Wato kai Mamman na lura kai hassadarka mai lasisi ne akan Yarima Karami,sannan kuma hassadarka bama akansa kadai ta tsaya ba,akan kowa take,toh bari kaji babu wanda zai dakesa acikinmu,idan kuma kai zakayi bismillah ina kallonka,idan kuma a'ah kai ƙararmu zakayi,toh shima bismillah kayi sauri kaje kafin iska ta rigaka... "
Bai ce kala ba illa gungunin da yake tayi,da sauri Jabir ya matsa kusa dashi yace"Dan uwarka idan ba tsoro ba fada inji in ban k'akkarya banza anan gun ba... " "Master ayi masa haquri... " haka sauran suka fada,shi kuwa Hayat sai binsu yake da kallo cike da qaunar Jabir aransa.Jabir ya sanya wani dogari tsayawa abakin kofa sabida at anytime Mai martaba yana iya zuwa.Kai Jabir akwai wayau,samun wani abu sukayi wanda ni kaina bansan ko menene ba,kasa kasa ne kuma dan jaja amma ba ja can sosai ba,suka goggogawa Hayat ajikinsa,dake shi din farin mutum ne,sai nan da nan fatarsa ta canza Kala,kai kace ko da gaske bugunsa din akayi.Kowa sai yabawa aikin Jabir yake banda Mamman wanda yayi fuska kamar na shanu😀.
Hayat ya fashe da kuka tare da kamo hannun Jabir,yace"Jabir thank u so much,haqiqa kai din mutumin kirki ne kuma ka cika masoyina na gaske,yadda kuka taimakeni dinnan kuma ina muku addu'ar samun taimako mafiyin nawa wataran,ubangiji Allah ya saka muku da mafificin alherinsa.
Dan muskutawa Jabir yayi kana yace"Allah ya taimaki Yarima karami ai ka cancanci ataimaka makan ne,shawararmu dai agareka yanzu shine don Allah ka dawo kan hanya,zunubi babba ne kake kokarin daurawa akanka sannan kuma kana kokarin b'atawa mahaifinka da kuma wannan masarautar suna,don Allah kabar shaye-shaye,buga chacha da kuma bin abokan banza,duk nan munsan abinda ke damunka kuma insha Allah zamu tayaka da du'a'i don mahaifinka mutum ne mai tsassauran ra'ayi,idan yace 'A' toh baka isa kace 'B' ba,kayi kokari ka karbi kaddararka ayadda tazo maka kuma na tabbata nan gaba zakaci ribar haquri,kazamar rayuwar daka jefa kanka ciki ya sanya ka zamo tamkar ragon namiji sabida ka kasa yin tawakkali,har ka biyewa rudin abokanan banza,don Allah abokina ka dawo kan hanya kaji ko?"
Murmushi Hayat yayi yace"Nagode Jabir insha Allahu daga yau nabar shaye shaye da kuma bin abokanan banza... "
Jabir ya sake duƙawa yace"Alhamdulillahi naji dadin hakan,My little prince ka mana afuwa zamu maka askin kai don wannan ya zama dole ayishi... "
"Ba damuwa... " Nan da nan kwalla ya sake taruwa acikin ramin idon Hayat don arayuwarsa ya tsani ƙwaryar molo😀,amma toh yaya ya iya?
Haka yana ji kuma yana gani akai masa correct tantali😂,bayan an gama Jabir yace"My little prince yanzu sai kayi acting kamar wanda yasha bugun tsiya har xuwa fada.... " Jabir ya mik'e ya soma tafiya yana dan d'ingisawa da kuma babbanƙaro baya tamkar wanda dai aka dakan.
Sauran suka fashe da dariya,Idrisu yace"Dakyau Yarima Karami,agaskia zaka fa iya yin wasar ƙwaiƙwayo,jinjina mai tarin yawa gareka jarumin jarumai.... " (Jarumin dake tsoron bulala?😂).
Jabir ne yaje ya soma dubawa ko babu kowa acikin fadar don baya son gimbiyoyi da kuma baƙin Mai martaba susan abinda ake ciki,yana zuwa kuwa ya tarar da Haj.Babba aciki suna fira da mai martaba,gaban mai martaba ne ya fadi na ganin Jabir don atunaninsa tare suke da Hayatun.Gaisar dasu kawai yayi kana ya juya ya fice,mai martaba hadda sauke ajiyar xuciya ganin ba'a taho da Hayatun ba.
Haj.Babba ta mik'e tace"Ranka shi dade ni na shige ciki bacci nakeji,yau kwata-kwata ban sanya d'ana Hayat ah ido ba,don Allah idan ya shigo yazo ina nemansa."
Murmushi kawai Mai martaba yayi tare da d'aga mata kai alamun yaji,ta fice abinta,Jabir nanan tsaye hatta zo ta wuceshi,sai daya tabbatar da ta shige turakarta kana ya wuce da gudu yaje ya taho da Hayat xuwa Fada.
Mai martaba na had'a idanuwa dashi yayi saurin k'awar da kansa gefe tare da runtse idanuwansa,ko kadan baya son ganin yanayin Hayat don yasan kalar fatarsa tabbas ta canza,sosai tausayinsa ke dukan xuciyarsa.Shi kuwa Hayat ganin mahaifin nasa ya dauke kallonsa daga gareshi,hakan yasa ya fashe da kuka tare da rugawa aguje xuwa gareshi,zubewa yayi agabansa ya rirrik'e kafafuwansa,Jabir kuwa ficewa yayi don ya baiwa d'a da mahaifi damar ganawa dakyau.
Yace"Abbana don Allah kayi hakuri wallahi nabar shaye shaye da kuma bin abokan banza,kuma itama Najmiy din na haqura da ita.... "
Girgiza kai Mai martaba yayi,kana yace"A'ah Hayat nifa nasan halin d'ana,duk fa abinda yace yana so toh kuwa kota halin ƙaƙa ne sai yasan yadda zaiyi ya sameshi,Hayatudden zan iya bugar k'irji ince baka haqura da Najmiy ba,kadai fada ne kawai don naji dadi,Hayatu bawai bazan iya baka auran Najmiy bane,a'ah so nake kawai na nuna maka cewar ba komai ne mutum idan ya nema kuma yake samu ba arayuwarsa,ina son na koya maka daukar haquri da kuma dangana don duk baka sansu ba."
"Abba mai martaba da gaske nake na haqura... " ya fadi hakan tare da d'agowa yana kallon mai martaba.
Murmushi mai martaba yayi kana yace"Toh Allah yasa,maganar da kayi dazu kuma bakayi k'arya ba,ni da mahaifiyarka mun bada tamu gudummawar wajen jefa rayuwarka acikin garari,amma kuma ina son ka sani cewar hadda son xuciyarka acikin,don da'ace kayi haquri kayi tawakkali ga ubangiji toh kuwa da hakan bata faru ba,kuma nasan tabbas zakaci ribar haquri da biyayya nan gaba,amma sai ka biyewa son zuciya,ita kuma xuciyar ta biyewa rudin abokanan banza,Hayat ina baka shawara daka gyara ko don lahirarka,sannan kuma ka dauki haquri da dangana don Najmiy ta riga ta maka nisa,maza ka tashi kaje kayi wanka sannan kaje ga mahaifiyarka Haj.Babba tana nemarka. "
Zancen Mai martaba be wani daga masa hankali ba kamar yadda yace wai Haj.Babba na nemansa,mai martaba ya lura da tashin hankalin daya shiga don haka yace"Bayan ni dasu Jabir babu wanda yasan halin da muka riskeka dazu... "
Saukar da ajiyar xuciya yayi,kana yayiwa mai martaba godia sannan ya mik'e ya fice ayayin da Mai martaba ya bishi da kallon tausayi,ahankali ya furta"Allah ya shirya abinsa... "
_*тoн мy ғιғυl ĸυna ganιn da gaѕĸe нayaт ya нaqυra da 'yar вalaraвιyar nan ĸυwa???*_
_*ĸυdaι ĸυ вιyo🏃*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
_*wow ιna тayaĸυ мυrnar ĸaммala lιттaттaғanĸυ мy janaғ(NA TAFKA KUSKURE) and мy leeмaн (BABBAN KUSKURE) wow the name's has something in common,haqiqa kun ilimantar,fadakar,wa'azantar da kuma nishadantar,sai mun jiku asabbin litattafanku,I want u all to know dat,dat chemistry of love between us will forever last & dat bond will forever be strong insha Allah•°*_
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo✍•°* _____________________________________
💥
*Թɑցҽ1⃣2⃣*
Ai kuwa zancen Hayat ya tabbata gaskiya,don tun daga wannan ranar yabar shaye shayen kayan maye,dama ba wai ya wani dulmiya ciki bane sosai,a'ah kawai sigari yake dan tab'awa sai kuma codein,shiyasa abin yazo masa da d'an saukin dainawa,wa'ennan abokanan nasa wa'enda sune suka dorasa kan wannan hanyar,suma tuni yayi watsi da lamuransu,Najmiy itama yayi kokarin yakiceta acikin xuciyarsa,kuma Alhamdulillah sonta yayi mugun raguwa acikin xuciyar tasa,dake ma yanxu ba wani cika haduwa suke har su zauna wuri guda ba shiyasa son nata yayi mugun raguwa acikin xuciyar tasa,itama hakan yake gareta,wannan dan birbishin sonsa da har ta soma jinsa aranta,tuni ya goge,sam babu shi don shaquwar tasu tayi mugun raguwa ne to the lowest level wanda hakan kuwa ba karamin dadi yai wa Mai martaba da Haj.Karama ba,ita kuwa Haj.Babba taso wannan hadin,amma tunda wanda yafita iko akansa yace sam bayaso sannan ita karan kanta mahaifiyar yaron itama bataso,toh ita din har wacece da zata goyi da bayan hakan?
Zuwa yanxu Hayat ya ware ya koma Hayatunsa nada da aka sani,wasa da dariya da kuma jawo mutane ajiki,amma wannan bakar xuciyar nan dai tana nan har yanxu ya kasa barinta,baka isa ka takashi ka wuce lafiya ba wallahi kuwa ko waye ubanka agarin bai damu ba sai ya daddaƙaƙa,shi dai bazai toneka ba amma muddin ka sake ka shiga gonarsa toh kuwa baya amsar kalmar 'hakuri' koda kuwa awasance ne ka masa abin,toh kuwa sai ya koya maka hankali wanda atake anan zakayi danasanin yi masa wasar.
Abin nasa ma yanzu ya k'ara worst don har dambe yake amakaranta da mutane,sau biyu ana bashi warning akan hakan,kuma akace idan ya sake next time ya kuma maimaita hakan akaro na uku,toh kuwa za'a koreshi ne daga makarantar,wannan abin nasa kuwa sosai ya bakanta ran mai martaba har yadau fushi dashi mai munin gaske,dakyar ya sakko bayan mutane da yawa sun saka baki akan yayi haquri,shima Hayatun yadau alqawarin cewar hakan bazata kuma faruwa ba.
Wani abin mamaki shine,harwa yau tsanar Faruq nanan makale acikin xuciyarsa,ya kullaceshi sosai aransa amma babu wanda ya gane hakan har shi Faruq din,don azahiri zaiyi faram faram dashi amma acikin xuciyarsa kuwa he has a story to tell,shi aganinsa k'arya da gaskiya ne ya shimfid'awa mai martaba agame da zancensa da Najmiy shiyasa mai martaban yadau alqawarin cewar bazai taba bashi auren Najmiy ba,aganinsa watakila Faruq din sharri ne ya kulla masa akan cewa lalata Najmiy kawai zaiyi ba wani sonta da yake,shiyasa yake jin tsanar Faruq din aransa sosai.Karatu kuwa tuni ya maida hankalinsa ya bada himma sosai,dake Hayat akwai ilimi awannan ƙwanyar tasa😂,don haka tuni CGPA dinsa yadan soma haurowa sama kadan da kadan.
_*•°вayan ѕнeĸarυ υĸυ•°*_
Acikin sheƙaru ukun nan kuwa abubuwa da dama sun faru,ciki kuwa hadda gama bautar ƙasar Faruq wanda yayi shi agarin Kaduna,bayan ya gama kuma mai martaba ya shige masa gaba ya samu aikin jarida don yace sam baya son fadawa harkar siyasa kuma,toh dake ba lallai sai field din da kayi studying kake samun aiki ba,now adays you can work anyway as far as u have that certified result,toh aikin jarida yake shaawa ayanxu becuz duk yana cikin job career na 'political science',prince Faruq Bahago is now a well known popular journalist.
Coming to our prince Hayat kuma,yana can Lagos yana bautar qasarshi,ah garin kaduna yayi camp training dinsa,daga baya kuma akayi relocating dinsa xuwa 'Akwa Ibom'wani abin ikon Allah kuma tare aka turasu can da Roughcoin wanda cikakken sunansa shine 'Abraham Sunday'.Roughcoin asalinsa bayeraben Ibadan ne,Karatu ne kurum ya kawoshi garin Minna (Dama bayerabun nan sune ke cika mana makarantun garinmu dinnan musamman ma FUTmin,lol only the futmites can relate😁).
Toh kunsan sha'anin 'ya'yan yanxu,ka haifesu ne amma baka haifi halinsu ba,wasu idan suka ga basa gaban iyayensu toh kuwa babu abinda basayi musamman idan suka hade da abokanan banza,idan kuwa kaci sa'a,Allah ya kiyaye,sai kaga ya shiryar da abinsa.(Allah yasa mu dace).
Toh hakan take ga Roughcoin,farkon zuwansa garin minna ya hade dasu spanzy wa'enda su din yan garin ne kuma agaban iyayensu suke,toh tare da taimakonsu ya fada kazamar rayuwa,shaye shaye kuwa babu wanda basayi,chacha ne da kuma zuwa party da clubs duk baya wucesu,kuma duk sunyi kaurin suna anan.Gashi sun soma rudan Hayat don kam Hayat ayanxu sai ta Allah,Roughcoin ya sake wura masa kunne ya koma kan shaye shayensa,don tun xuwansu Camp training ya soma.
_*°•ѕaι ĸυмa мeн?•°*_
Alokacin dasu Hayat suka soma zuwa camp training for three good weeks kafin zuwansu service kenan,da ya dawo gida ya sake kyalla ido akan Najmiy,sai kawai yaji gyamb'on sonta ya fama,yaji kawai wannan karon idan bai sameta ba toh kuwa yana iya mutuwa,tuni ya tada bala'i acikin gidan akan lallai fa sai an aura masa ita ko anki ko anso idan ba haka ba kuwa zaiyi kidnapping dinta idan yaso kowa ma ya rasata.(lallai na yadda da maganar mutane da sukace Shaye shaye yana sanya mutum rashin kunya,zakaga idanuwan mashayan nan atsasstsaye suke,basa tsoron kowa kuma).
Toh hakan take ga Hayat,sam sam yama manta cewar Abba mai martaba ne yake gayawa hakan,shi kuwa mai martaba sosai abin Hayat din ya bashi mamaki da kuma haushi,wannan Karon abinda mai martaba bai taba yi ba yayi,wato dukan mutum da hannunsa,illai kuwa Hayat yasha bugun tsiya ahannun Mai martaba,dakyar aka kwaceshi ahannunsa,cike da tsananin fushi mai martaba ya sake daukar alqawarin cewar bazai taba baiwa Hayat auran Najmiy ba,ko bayan ransa aka sake hakan ta faru,toh kuwa bai yafewa malamin daya daura wannan auran ba.wannan maganar ta sake girgiza kowa bama Hayat din kadai ba,Haj.karama ita kanta tayi nadama kuma ta sakko yanxu kuma tana son hadin amma kuma ga abinda mai martaba yace.
Mai martaba so yake Faruq yadanyi steady kafin ya bullo da maganar hadashi da Najmiy don bai wani jima da soma aikinsa ba,yafi son komai yayi masa chaschas kafin ya kunno da batun auren.
Najmiy da Hidaya kuwa tuni suka sami gurbin kayatu ah 'School of midwifery minna',suna matakin farko kenan.Ita kuwa Abida sheƙaranta daya da rabi kenan da aure,dake tana gama sec.school dinta ba'a wani dau tsawon lokaci ba tayi auran don dama ita batason karatu acikinsu duka,tana son aure sosai kuma wani matashin saurayine ya aureta,ƙanin wani former mataimakin gwamnar jihar minna ne,wanda dama suka dade suna soyayya aboye.
Wani abin mamaki da al'ajabi shine,kafin Hayat ya tafi service yanata maimaita kalmar "inna tafi bazan dawo ba,wallahi bazaku sake ganina ba,tunda har aka hana min Najmiy." toh kowa bai bi takan maganarsa ba don atunaninsu duk iya shegensa bazai taba yin hakan ba,azatonsu rashin hankalinsa bai kai nan ba.
Wasa wasa bayan ya tafi,har 'yan first batch na service sun soma daddawowa gida amma ba labarin Hayat,dake shima din dan 'batch A' ne.magana karama har ta zama babba,har aka shafe shekara daya da rabi babu zancen dawowar Hayat,dake yanxu yana da wata 'yar karamar waya,idan aka nemeshi sam ba'a samunsa,har ankai report ah Youth service centre minna,suma suka sanya ayi cigiyarsa acan Akwa Ibom din,amma babu labarinsa.
Daga baya mai martaba yayi fushi yace"Kar wanda ya sake neman Hayat,na tabbata ya cika alqawarin daya daukar mana ne,ku bari duniya ta koya masa hankali tukun,nasan tabbas zai dawo don bazai iya da rayuwar babu ba,kar wanda ya sake ya sake saka kafa waje da niyyar nemansa,idan har hakan ta faru kuwa,toh ban yafe ba.... " shi kansa yadai fada ne amma sosai abin ke damunsa.
_*°•Ina labarin Hayat?•°*_
Tun kafin su kammala service dinsu ya gayawa roughcoin damuwarsa,ai gashi gashi wacce yakeso agidansu amma mahaifinsa ya rantse da cewar bazai bashi ita ba,yanzu ina mafita?
Dake ya kawo kuka gidan mutuwa ne,ko kuma ince yazo neman shawara gun mahaukaci😂,sai roughcoin ya bashi shawarar cewar tunda ai har ya gaya musu cewa idan yazo bazai dawo ba,toh ya cika wannan alqawarin,ya bari sai bayan kamar shekara daya ko biyu sai ya koma,zai dunga kula da cinsa da shansa,infact zai samo masa aikin yi dake iyayen roughcoin din nada dan kudi,yace masa ya tabbata bayan ya koma za'ayi saurin bashi auranta don bazaa so ya sake guduwa ba.
Allah dai ya tsaremu da hulda da abokan banza,tuni karatun da roughcoin ya karanto masa ya shiga cikin kwakwalwarsa ya zauna daram,ya biye masa suka lula sai can Lagos,acan suka kama haya,Hayat ya kakkarya sim dinsa don kada asameshi,sannan ya sauya da wani.makuden kudaden dake hannun roughcoin kuwa tuni ya samo musu second hand bus suka soma kasuwancin kai da kuma dauko mutane agari,dake Hayat bai iya tukin mota ba,sai ya zamana roughcoin ne direba ayayin da Hayat ne conductor😭,(imagine the whole son of an emir,Hayatudden freaking m.k Bahago is now a conductor,kai such is life! Hayat kayi mugun bin son xuciyarka).
Toh da wannan kasuwancin ne suka dogara suke samun naci aciki,Hayat sam sam baya ma tunanin gida,so yake da zarar yayi shekaru uku anan saiya koma,kuma yadau alqawarin cewa muddin Najmiy tayi aure tofa saiya fitar da ita idan ya koma.Toh shima din Roughcoin iyayensa basu san duniyar daya shige ba,suma sunyi neman har sun gaji don har minna suka zo amma babu labarinsa.
Akalla yanxu yayi shekara daya kenan acan,zuwa yanzu an soma fama da mahaifiyarsa Haj.karama,ta kamu da ciwon zuciya chronic one kuwa,don lokaci daya yayi mata mugun kamu,toh itane kullum cikin kukan zuci take kan b'atan danta,kunsan ance uwa-uwa ce,koda kuwa kowa ya manta da batun Hayat toh kuwa yana makale ita aranta.
Gimbiya maymunerh is suffering from congestive heart failure,General hospital abin yafi karfinsu shine sukace "wannan fa sai an fita da ita waje,if not kuna iya rasata"
Bayan kamar kwana biyar tuni mai martaba ya gama hada kudaden da zaa fita da ita,dake ba laifi shima yana da kudi kuma babban mutum kamarsa ai dole ne ya samu taimako daga hannun mutane da yawa.
Gimbiya Maymunerh dai tace baza'a sha wani wahala akanta ba,don ana gobe za'a fita da ita kasar India tace ga garinku nan,kuma ta mutu ne da sunan _*Hayatudden*_ abaki.
_*Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un*_, haqiqa wannan mutuwar ta girgiza iyalan mai martaba M.k Bahago,kaiconsu ma akan Hayat ne wanda bai samu ganawa da mahaifiyarsa ba har ta tafi,ta sanadiyyarsa kuma ta kamu da wannan ciwon xuciyar har ya zamo ajalinta........Allah sarki Gimbiya Maymunerh Allah yaji kanki,amin😭
_*Zan dan dakata don nima zan kai ta'aziyya,idan akwai wa'enda zasuje toh akwai free bus sai sumin magana*_
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
_*°•don Aℓℓαн ιna ѕon ĸυ ғaнιмcι dalιlιna na rυвυтa wannan laвarιn,вawaι nayιѕнι don ajι dadιnѕa ne вa ĸawaι,ĸaмar yadda naga waѕυ нar ѕυn ѕoмa мιn ĸoraғι ĸan ya ĸaмaтa na ѕaѕѕaυтawa rayυwar нayaт,don Allaн ĸυ daιna вanaѕo,nιna тѕaro laвarιna don ιna ѕon ne na ιѕar da waтa мυнιммιyar ѕaĸo хυwa gareĸυ,ѕo naĸe ĸυ тѕιncι darυѕѕa da yawa acιĸιn rayυwar wa'ennan вayιn Allaнn мυѕaммan мa нιввaтυllaн wacce don ιтa мa nayι wannan lιттaғιn,тa ĸυѕan ѕнιgowa cιĸιn laвarιn nan вada jιмawa вa,ιdan ĸυwa ĸυĸace ѕaι anyι yadda ĸυĸeѕo,тoн ĸυwa вazaĸυ вanι daмar ιѕar da aвιnda naĸeѕon ιѕarwa вa,don нaĸa ιnaѕon don Allah ĸυ вanι нadιn ĸaι ĸυмa ιna ѕonĸυ dυĸa мy ғanѕ,ιna godιa da coммenтѕ dιnĸυ•°*_
_*•••wannan ѕнaғιn мallaĸιnĸι ne ĸe daya мy вlood ѕιѕ anтιna ѕaιnaн,ιnaѕo ĸι ѕanι cewar qaυnarĸι araιna ya wυce yadda ĸιĸe zaтo da ĸυмa тѕaммanι,ѕaιnaн нaғnan dιnĸι тana мιĸι тrυe love вaвυ yaυdara acιĸι❤️💕°°°*_
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo✍•°* ______________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣3⃣*
"Hajiyata yanxu shikenan Haj.Karama ta tafi ta barmu da ƙewarta kenan?yanxu shikenan bazamu sake ganinta har abada ba kenan?lallai yau na ƙara tabbatar da cewar ita duniya makarantace,kamar yadda ka shigo cikinta,tofa haka watarana zaka barta,acan kuma zaka soma wata rayuwa kai kadai ah inda ayyukanka na alkhairi ne kadai kawai zasu iya tseratar dakai daga azabar Allah, _*'RAYUWAR KABARI KENAN'*_ ..... "
Fashewa da wani irin kuka yayi mai ban tausayi,kana ya cigaba"Hajiyata wallahi babu abinda yake sakani cikin tsananin firgici da kuma tsoro face inna tuna da zango-zango na tashin ƙiyama,Bahasi na farko shine *'MUTUWA DA KUMA TSANANINTA'*,mutuwa itace masauƙin farko na isa ga ƙiyama,sannan kuma zangon farko ta tayarwar lahira,manzon Allah (S.A.W) yana cewa *"mutuwa ƙofa ce ta lahira,haka kuma mutuwa ƙiyama ce,idan dayanku ya mutu tofa ƙiyamarsa ta tashi,Inda anan ne zaiga sakamakonsa na ayyukan daya aikata asanda yake duniya,wato khairan ko kuwa sharran..."*
Bahasi na biyu shine, *'BARZAHU DA KUMA AZABAR DAKE CIKINTA'*,wato ita dai barzahu wata duniyace dake tsakanin mutuwa da kuma ƙiyama,ana ni'imta mamacine idan yazo ne da ayyukansa na alheri,ko kuwa ah azabtar dashi idan har yazo ne da munanan ayyuka,za'a cigaba ne da azabtar dashi har xuwa gobe ƙiyama."
Bahasi na uku shine *'SHARUDDAN ƙiyama'* ,wannan kuma alamomi ne dake nuni da samuwar Aljannah ko kuma wuta.."
Bahasi na hudu shine *'ABUBUWAN DA ZASU FARU RANAR ƙIYAMA'*,Ranar tayarwa kenan,ranar da halittu zasu tsaya gaban ubangiji don hisabi. "
Bahasin ƙarshe shine *'YAN ALJANNAH DA YAN WUTA'* wato anan ne zakasan makomarka,wato wuta ko aljannah?"
Sake rushewa yayi da wani sabon kuka yace"Toh meh zaisa mu 'yan adam mu dauki duniya da zafi?itafa gidan wuta da kudinka zaka siyeta,sabida chachar nan idan zaka bugata tofa tabbas zaika biya kudi,haka ma giya da sauran kayan maye idan zaka shasu suma tabbas saika biya kudi,kwanciya ma idan zakayi da karuwa(Zina) shima saika biyata kudi,da sauransu dai,amma itafa aljannah k'yauta za'a baka ita,zakayi sallah k'yauta babu ko sisinka da za'a k'arba,haka ma azumi k'yauta zakayi,da sauransu dai,toh fisabilillahi! Meh zaisa muyi wasa da damar da Allah ya bamu?"
"Iyaye!iyaye!!iyaye!!! Manzon Allah da kansa ya k'ira sunayen iyaye sau uku kafin yace *"Iyayenku suna da matukar muhimmanci arayuwarku musamman kai d'a namiji,iyayenka sune hanyar samun aljannarka idan harka k'yautata musu kenan,samun aljannar ma dakyau yana tafin kafar mahaifiyarka ne,in taso ta daga ka samu,in taki kuma shikenan... "
Ya k'arashe zancensa da"Why Hayatu?meyasa ka biyewa son xuciya da kuma rudin abokanan banza har suka kaika suka baro?ta sanadiyyarka mahaifiyarka ta rasu adalilin rashin haqurinka da Kuma daukar dangana,uwa fa ba'a bar wasa bace..... "
Cikin muryar kuka Haj.Babba ta katseshi"A'ah Faruq dena fadin hakan?ko kadan karka ga laifin Hayat acikin wannan al'amarin,a'ah lokacin Maymunerh ne yayi shiyasa ta amsa k'iran mahaliccinta,Kuma muna fatar Allah yakai rahama kabarinta,Maymunerh Allah yasa kinje asa'a,Maymunerh ubangiji Allah ya gafarta miki kurakurenki duka,na yafe miki duk wani laifi da kika min,da wanda na sani da wanda ban sani ba,duk na hada na yafe miki duk da cewar ni dai baki taba min komai ba,amma ance zaman tare dole watarana za'a dan samu 'yar sab'ani,amma wallahi harga Allah ni Hadizatouh na yafe miki...... "
Kuka yaci k'arfinta,babu wanda kalamanta bai shigesa ba da har ya sanyasu kuka,Hidaya,Abida,Najmiy da kuma Faruq din duk kuka sukeyi mai tab'a xuciya.
Mai martaba wanda ya dade abakin kofar dakin tsaye yana sauraronsu ne ya shigo ciki,idanuwansa sunyi jawur dasu,sun kankace sabida kukan dayasha,yace"Hadizatouh sam Umari beyi k'arya ba,ta sandiyyar Hayatu maymunerh tabar duniya,kuma insha Allahu kamar yadda yasanya muka xubar da hawaye akansa toh kuwa........ "
Da hanzari Faruq ya isa gareshi tare da sanya hannu ya rufe masa baki,alokaci daya kuma ya shiga girgiza masa Kai"A'ah Abba mai martaba don Allah na rokeka kar zuciya ta sanya ka tsinewa d'anka don hakan zai iya karasa tab'arb'arewar rayuwarsa,na rokeka Abbana karka debewa Hayatu albarqarka.... "
Zubewa yayi akasa gami da rirrike masa kafafuwa yace"Abba Mai martaba ina rokarwa Hayat wata alfarma,ba donni ba,ba kuma donna isa ba,amma don Allah zakayi,ina son ayau ka sanyawa rayuwar Hayatudden albarqa aduk inda yake afadin duniyar nan..... "
Haj.Babba ma dasu Abida duk suka taso suka zube agabansa suna rokonsa,Mai martaba kuwa rintse idanuwansa yayi jin yadda xuciyarsa ke aikin soyuwa,can ya budesu,fes ya sauke kallonsa akansu,murmushin takaici yayi kana yace"wani albarka ne kuma yayi saura da zan sanyawa Hayatu?ai ina aza ko yana da wasu iyayen ne can wa'enda suka fimu shiyasa ya gujemu?kuyi haquri amma wannan bakin nawa bazai iya furta kalmar 'Albarka' akan Hayatu ba,ni nama riga da na cireshi acikin 'ya'yana,na sallamawa duniya shi......."
Cike da tashin hankali Faruq ya mik'e yana kuka,yace"No!No!No!! Abba Mai martaba don't say dat,don Allah na rokeka karka tsinewa dan'uwana,Abba mai martaba idan bazaka iya sanya masa albarqa ba,toh idan ana iya debewa akan wani d'an,toh inason ka kwashe nawa idan yaso shi azuba masa,ni kuma atsine min.... " agigice Faruq ke fadin wannan maganar😢
Da sauri Najmiy ta mik'e ta rufe masa baki,tace"No Yayah prince Babba daina fadin hakan,babu wanda za'a tsinewa acikinku saima dumbin albarkarsa da zaku samu...... "
Zubewa ta sakeyi akasa ta shiga rokan Mai martaba,shi kuwa Faruq hannu yakai yana taba bakinsa inda tafin hannunta ya taba,lumshe idanuwa yayi yana mai jin wani sabon al'amarin da bai taba ji ba yana shigar xuciyarsa,wato *'SHAUKIN SO'*
"Najmiy naji ya isa amma da sharadi idan har kun yadda.... " haka suka ji mai martaba ya fada cikin wata kakkausar murya.Babu wanda baiji gabansa ya fadi agame da hakan ba.
Dakyar Hayat yace"Wani sharadi kenan Abba mai martaba?"
With full confidence yace"Idan an gama zaman makoki zan daura auran *'NAJMIYYA GADDAFI'* da kuma *'YARIMA UMAR FARUQ BAHAGO'* "
Gabaki daya dakin yayi tsit kamar babu wasu halittun dake ciki,gaban kowa sai harbawa yake da sauri da sauri musamman ga wa'enda abin ya shafa,wato 'Faruq' da kuma 'Najmiy'.
"Ya naji duk kunyi shiru?idan kuma baku yadda ba shikenan bazan sanyawa Hayatun albarka ba... " acewar mai martaba.Har ya juya zai fita,da sauri Faruq ya riko rigarsa yace"A'ah Abba mai martaba don Allah karka tafi wallahi duk mun amince,zamu maka biyayya idan har hakan ne zaisa ka sanyawa dan'uwana albarqa.... "
Mai martaba yace ba tare da ya juyo ba"Dakyau Umar Faruq,kefa Najmiy yaya kin amince ko kuwa a'ah?"
Kafeta da idanuwa Faruq yayi,ai kuwa anci sa'a itama shi din take kallo,signal yayi mata alamun itama tace ta amince.Da sauri tace"Abba mai martaba harni na isa naja da hukuncin da mahaifina ya yanke akaina?akullum fatarmu shine mu wanye daku lafiya kuna masu alfahari da kuma shi mana albarka,don haka ni Najmiyya nayi na'am da zab'inka na auren Yarima umar Faruq.."
Murmushin jindadi Mai martaba yayi tare da juyowa yana fuskantarsu,yace"Alhamdulillah! Najmiy ina godia kwarai da gaske da daukata da kikayi tamkar wanda ya haifeki,kaima Faruq ayau ka nuna min cewar lallai na haifa,kuma na isa na bada umarni har abi,sannan kuma ka nuna min cewar na isa na zartar da hukunci har ah amsheshi da hannu bibbiyu ba tare da anmin korafi ba,nagode kwarai da gaske Umaru da biyayyarka agareni kuma ina rokan Allah kaima ya baka 'ya'yan da zasu maka hakan daga kai har Najmiy,kuma yanxu zan muku abinda kukeso... "
Hawaye na gangarowa saman kuncinsa yace _*"d'ana Hayatudden ubangiji Allah yayiwa rayuwarka albarqa aduk inda kake,Allah ya karkato da hankalinka gida ka dawo cikin zuri'arka"*_
Duk suka amsa da "Ameen Yah Allah" suna masu kuka,mai martaba yana gama fadar hakan ya juya ya fice don har xuwa yanzu suna kan karbar gaisuwar ta'aziyyar mutane ne,yau kwana bakwai da rasuwarta amma idan kaga yadda mutane keta tururun zuwa kai kace ko yau ne akayi rasuwar.
_*υp!υp υp υмar ғarυq вaнago,wallaнι ĸayι мυgυn вιrgenι awannan page dιn,ѕaмυn dan'υwa ĸaмarĸa ѕaι an тona,мaĸιyιn υмarι people lιĸe мaryaм cнυввy нope yaυ ғarυq ya ѕoмa вιrgeĸυ????*_
_*ιѕ lιĸe ĸaмar ғarυq ya ѕoмa ĸaмυwa da ѕon najмιy ĸo?wнaт???aĸwaι rιĸιcι ĸenan?нaнaнa!can'т ѕay,ĸυ daι ĸυ cιgaвa da вιвιyaтa*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
*°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтerѕ aѕѕo✍•°* _____________________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣4⃣*
"Hajiyata amma kina ganin....... "
Da sauri Haj.Babba ta tari numfashinsa"A'ah Faruq kul kada naji ka furta komai,mahaifinku ya riga da ya gama magana,yanxu ya rage gareku ne kuyi biyayya tunda har kun riga da kun amince,ya rage gareku ku kara fahimtar juna kafin lokacin biki,ubangiji Allah ya shi muku albarqa da biyayyar da zaku mana bawai don kunso ba,kuma ina mai tabbatar muku da cewar insha Allahu bazaku taba tab'ewa ba don d'a meh biyayya ga iyayensa,Allah kan saka yaga daidai acikin lamuran rayuwarsa,Umar Faruq,Najmiy Allah ya shi muku albarqa,shi kuma Hayatudden Allah yasaka hannu cikin lamarinsa ya karkato da hankalinsa xuwa gida.... "
Gabaki daya suka amsa da "Ameen Ameen Hajiyarmu... " Faruq ya mik'e ya fice zuwa fadar mai martaba don tayashi ƙarban gaisuwa kamar kodayaushe,don tunda akayi rasuwar kullum makale yake da mai martaba,tare suke ƙarbar gaisuwar mazaje,Haj.Babba kuma su karbi na mata,wasu matan ma da biyu suke xuwa kawo gaisuwa don kawai suyi tsegumi,dake kuwa maganar b'atar Hayat ya gama zaga gari,da yawa cewa suke ta dalilinsa mahaifiyarsa tabar duniya.
*WANNAN KENAN* _______________•°•___________________
Bawan Allah Hayat kuwa,duk wani information na gidansu yana samu tare da taimakon abokinsu Ibrahim Spanzy wanda shine ke basu labarin komai awaya.Spanzy ne ya samu mai gadin gidansu mai martaba,dake shi din yaro ne mai wayon tsiya sai da yasan yadda yayi suka saba da tsohon,kusan kullum sai yazo kofar gidan sai su zauna abenci awaje,spanzy sai yayi ta bugar ruwan cikinsa,shi kuwa Mal.Madu mai gadi sai kaga ya shagalta yana kora masa bayanin komai dake faruwa tun daga batar Hayat har xuwa rasuwar mahaifiyarsa,idan Spanzy zai tafi sai kaga yadan zaro naira dari ko dari biyu ya bashi,shi kuma tsohon ya karba yana mai washe baki tare da shi masa albarqa,Mal.Madu bai taba kawo komai aransa agame da zuwan Spanzy wurinsa akodayaushe ba,ya dauki hakan ne kawai akan haduwar jini ne.
Alokacin da rasuwar Haj.Karama ya riski Hayat,ranar sadakar uku ne ma aka gaya masa,har suma sai da yayi,bayan ya farfado kuwa kamar zai haukacewa Roughcoin,cewa yake yana dada nanatawa"wayyo kaicona Hayat na cuci kaina,nayi sanadin barin mahaifiyata duniya,ta tafi da tsananin fushina adalilin biyewa son xuciyata,babu makawa makomata gidan wuta ce... " Ya fashe da wani irin wahalallan kuka mai ban tausayi,Roughcoin kuwa fashewa da dariyar iskancinsu yayi,sai daya dan zuƙi tabarsa kana yace"See diz idiot ooo,u don already judge urself,hahaha thank God da kasan cewa gidan wuta straight zaka shiga.... " Ya sake zuƙar tabarsa ya fesar akan fuskar Hayat,azuciye Hayat ya mik'e ya yankawa Roughcoin mari yace"Mahaifiyata ta rasu shine kake shan taba agabana?atleast she need a sign of respect and a sympathetic face from you,kodayake ita din uwatace ba uwarka ba shiyasa baka damu ba,toh bari kaji ni gida zanyi yanxun nan kuwa. " ya juya ya soma hada kayansa yana kuka yana ambaton "Hajiyata pls ki yafemin wallahi na tuba,ubangiji Allah yayi miki rahama. "
Kai ya rabbi Allah ka mana tsari da shedanun Abokai (Ameen),wato na takaice muku labari sai da Roughcoin yasan yadda yayi ya sake hurewa Hayat kunne akan yayi haquri ya cika mission dinsa,yayi kokari koda shekara dayace ya kara,Haj.karama ko ya koma ba dawo da ita zaiyi ba,don haka ya haqura kawai.
Yana hawaye yana fadin"Abraham uwa-uwace fa bai kamata ace na banzarta da ita ba,ya kamata naje nima ayi zaman makokinta dani,don haka na rokeka ka bari na tafi." Rokansa yake tayi amma don mugunta Roughcoin ya cigaba da zugashi har sai daya ga ya samu nasara,ya hada Hayat da wiwi,tuni Hayat ya shiga duniyar dake mantar dashi damuwarsa.
Haka ya kasance akullum sai yayi kukan Hajiyarsa tare da rokar mata samun rahamar ubangiji da kuma nemar gafararta,wani abin birgewa ga Hayat shine sallolin nan na farilla guda biyar arana daya baya taba wuceshi,kai infact har nafilfili yana yi,lokacin shiriyarsa ce dai bata yi ba.(Shifa shiriya sai wanda Allah yaso yake yiwa,don haka let's thank God for every situation we found ourselves in,Allah ya shiryar da al'ummarsa,ameen😭).
*** Magana karama harta zama babba,wata ranar Juma'a bayan an sakko sallar juma'a aka daura auran *'YARIMA UMAR FARUQ BAHAGO'* da kuma *'NAJMIYYA GADDAFI'* akan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.Manya manyan mutane sun samu damar halartar wannan daurin auren,hadda sarakuna,sarkin gombe mahaifin Haj.Babba ma saida yazo da tawagarsa.Abin dai yayi tsari sosai,kuma sun masa addu'ar Allah ya bayyana dansa Hayat duk da cewar babu wanda yasan dalilin batarsa,gaskiya agaida masu yiwa mai martaba Mk Bahago hidima,akwaisu da amana da kuma rike sirri,Mal.Madu ne dai ya fita zakka acikinsu,amma hatta Mamman dai akwaishi da rufe magana wasu lokuttan.Shi kansa batar Hayat na damunsa ayanxu.
Dama akwai flat biyu da Mai martaba ya sanya aka ginawa 'ya'yansa maza don xuwan irin wannan ranar,toh daya daga ciki aka baiwa Faruq ya zauna da amaryarsa anan.Faruq bai taba mafarkin cewa wai akwai ranar da zai auri yarinya yar kankanuwa ba cuz he never liked it,Najmiyya shekarunta ayanxu goma sha shidda,shi kuma yana da 28,amma kuma toh yanzu ya ya iya dole ce tasa,biyayya kurum yayi,amma tsoronsa daya duk ranar da Hayat ya dawo tofa akwai rikici.
*°•BAYAN WATANNI BIYU•°*
Toh dayake ance tsakanin mata da miji sai Allah,tuni Faruq da Najmiy suka ijje wani nauyin juna da sukeji,suka rungumi kaddararsu suka hau zaman lafiya,ga wata soyayyar junansu data samu matsugunni acikin xukatansu,uwa uba mutunta juna da kuma girmamawa.Najmiy da Hidaya na shekararsu ta biyu kenan ah midwifery,sauran musu 1year is kare,don haka tare suke tafiya makaranta kullum.
Xuwa yanxu dangin mahaifiyar Hayat sun tasa mai martaba Mk agaba,wai ya manta da yaron yar'uwarsu ya cigaba da rayuwarsa bai damu da batar Hayatun ba,don haka dole ne afita aje anemo masu shi idan ba haka ba kuwa zasu dauki mummunan mataki,damuwa yabi yayiwa mai martaba yawa,kusan kullum sai sunzo sun fitineshi,Hawan jinin mai martaba ya tashi sosai wanda hakan ya janyo watarana ya yanke jiki ya fadi,stroke ta kamashi,yanzu mai martaba Mk.Bahago sai dai atayar sannan kuma adaga,baya iya magana sai dai kwatance da hannu da kuma hawaye,duk kuma so yake yace aje anemo masa Hayat amma ya kasa😭.
Watarana Faruq da kuka ya sami Haj.Babba yace"Hajiyata na nemi inda Ibrahim Spanzy abokin Hayat yake zaune,kuma ya gayamin komai,Hayatudden dai yana garin Lagos yana aikin conductor tare da abokinsa Roughcoin wanda shine ya zugashi suka gudu... "
Da karfi Haj.Babba takaiwa k'irjinta mugun bugu tace"Ni Hadizatouh conductor fa kace Faruq?"
"Eh hajiyata sana'ar da Hayat keyi kenan acan,da wannan aikin suka dogara har suke samu su saka abu acikinsu,wai don sun nemi aikin gwamnati harwa yau basu samu ba,fisabilillahi Hajiyata taya kuwa zasu samu aikin bayan suna rataye da hakkin mutane da yawa awuyansu?kadan ma suka gani kenan,na yanke shawarar tafiya garin lagos agobe don tahowa da Hayatu don bazan taba bari wannan karon ya sake zamowa sanadiyyar mutuwar wani nawa ba.... "
Da sauri Hajiya tace"Kai yanzu idan ka shiga garin lagos ka soma nemansu daga ina?koka manta cewar Lagos babban birni ne?
"Hajiya Spanzy ya gayan komai hadda kwatancen unguwar da suke zaune.. "
Tace"Toh addu'ata shine Allah yasa dai gaskiya ya gaya maka. "
"Amin,amma don Allah kar afadiwa Abba mai martaba gaskiyar lamari,don kawai ce masa nayi wani gidan radio ne agarin lagos suke nemana da gaggawa,yadai amsa min da kai ne kawai.. "
Ahankali tace"Toh Faruq Allah yasa ayi nasara,Allah ya jagoranceka awannan tafiyar da zakayi,Allah yayiwa rayuwarka albarqa.... "
"Amin Hajiyata,bari naje na kwanta don gobe sammako zanyi.. " tace"Toh"
Koda ya fita bangaren mai martaba ya nufa don anan yake kwana yanxu tunda ya kwanta rashin lafiya,gobe ne kawai zai danyi nesa dashi,Najmiy kuwa adakin Hidaya take kwana don acewarta bazata iya kwana ita daya awannan makeken flat din ba.
_*тoғa мy people ĸυna ganιn ғarυq zaιyι naѕarar dawowa da нayaт gιda ĸυwa?*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍* https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ ____________________________________
💥 *Թɑցҽ 1⃣5⃣*
Misalin karfe biyar ta asuba alokacin tuni har an soma kiraye-kirayen assalatu,Faruq ya mike,mai martaba ma tuni shima ya farka,don yama riga Faruq din farkawa.
"Abbana harka farka?toya jikin naka?" acewar Faruq.Kai kawai ya daga masa alamun da sauki,gashi babu damar tashiwa don gabatar da sallah,dama Faruq din yaketa jira ya tashi yayi masa alwala,tunda ya kwanta rashin lafiya Faruq ko kuma Haj.Babba ko kuwa Najmiy sune ke masa alwala idan yaso sai yayi sallar acikin xuciyarsa.Mai martaba Mk Bahago kenan akwai son ibada.
Yanxu ma haka Faruq dinne ya shiga bathroom ya soma dauro alwalarsa,kana ya debi wani ruwan acikin buta sannan ya dauki wani bawo mara girma sosai,yaje ya daurawa Abbansa alwala,ahankali yaketa bi dashi harya kammala.Mai martaba ya shiga gabatar da sallarsa acikin xuciyarsa ayayin da Faruq kuma ya shimfida dadduma don sauke nasa faralin.
Bayan ya kammala ya juyo yana duban Mai martaba,lazimi yaga yakeyi da hannunsa mai lafiyar.ahankali yace"Abba mai martaba bara naje na shirya donna samu na isa da wuri." Binsa kawai yayi da ido harya bacewa ganinsa.
Misalin shidda saura Faruq ya gama shirinsa tsaf cikin kananan kaya wanda sukayi matukar karbar jikinsa,kaya kala daya kurum ya zuba acikin laptop bag dinsa irin na school bag dinnan,kana ya ratayoshi,ya fito tsab dashi kuwa,komawa turakar mai martaba yayi ah inda ya tarar da Haj.Babba dasu Najmiy har sun fito sallamarsa.(Idan zaku tuna awani page nace tunda mai martaba ya kwanta rashin lafiya Faruq ya tare awurinsa,toh shine ita kuma Najmiy ta koma kwana tare da Hidaya sabida tsoron kwana take ita kadai).
"Faruq har an fito?"acewar Haj.babba.
"Eh Hajiyata gwara na daka sammako donna samu na gama abinda yakaini yau dinnan,gobe kuma na juyo idan har naci nasara kenan."
"Insha Allah zama aci nasara... " acewar Haj.Babba,ya russuna ya gaida ita da kyau,bayan sun gama gaisawar,Najmiy da Hidaya suma suka russuna suka gaidashi,ya amsa musu cikin sakin fuska.Can ya nufi inda mai martaba yake zaune asaman gado,yayi matashi da kansa akan wani pillow.Zuba masa idanuwa yayi tun kanma ya karaso gareshi.
Tsugunnawa yayi tare da kamo hannunsa mai lafiyar,ya shiga dan murzasu kana yace"Abbana barka da safiya,ya karfin jikin naka?" ya fadi hakan tare da sakar masa murmushin karfin hali,shima mai martaban sakar masa murmushin yayi gami da daga masa kai alamun amsawarsa kenan.
Sannu ahankali wasu hawaye masu dumi suka sakko saman kuncin Faruq,da rawar murya yace"Abbana don Allah ka sanya min albarqarka acikin wannan tafiyar da zanyi bawai donna so bane,a'ah sai don kawai ya zamar min dole na fita naje na samo maka maganin lalurar nan taka,idan har naci nasara toh kuwa insha Allahu zan komo gobe Abbana,Abba bazan dawo ba har sai....... "
"Kai Faruq meye haka?so kake ne ka tada masa hankali kuma?" acewar Haj.Babba cikin hargowa.Ai da sauri ya shanye sauran maganar tasa don shi baima san ya sake layi haka ba sai datayi saurin ankarar dashi.Shi kuwa mai martaba tsura masa ido yayi cike da rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa,dake Faruq din yace masa wani gidan redio ne suke nemansa ah garin lagos da gaggawa(ku tuna shi din dan jarida ne),yanxu kuma yana ce masa wai zaije samo masa maganin lalurarsa,shiyasa ya rud'e.
Faruq ya lura da tsananin mamakin dake shimfid'e saman fuskarsa don haka murmusawa yayi yace"Abba mai martaba don Allah karka daga hankalinka ba wani abin bane kawai alheri ne ke ƙirana,nidai kawai albarqarka nake nema kafin na tafi... "
Ahankali ya zare hannunsa dake sarke cikin na Faruq din,ya dora hannun asaman kansa,yadan bubbuga kan alamun ya sanya masa albarqan kenan.
"Nagode Abbana." Faruq ya fada da murmushi sannan ya nufi Haj.Babba itama ta sanya masa albarqa da kuma yi masa fatar alheri.
Agurguje suka fito suka masa rakiya zuwa wurin mota,Haj.Babba na kara jaddada masa kan ya rike addu'a abaki kuma Allah yasa yayi nasara.
Babu bata lokaci direba yaja motar suka bar gidan sai *'N.S.T.A GARAGE MINNA'*, sam bayason xuwa amotar gida shiyasa ya zabi xuwa amotar gwamnati.Acikin motar ne ya fito da system dinsa daga cikin jaka,ya shiga sarrafata cike da kwarewa,so yake yayi booking hotel kafin ya isa don bayason abata masa lokaci idan yakai, wani hotel ne yaga ya bashi shaawa don haka babu bata lokaci ya shiga booking *'GRANDBEE SUITES HOTEl IKEJAH,LAGOS'*.
Adaya bangaren kuma yayi connecting wayarsa da Bluetooth speaker din dake kunnensa,kana yayi dialing layin Spanzy ya sanar dashi cewa yana kan hanyarsa ta xuwa gareji ne don haka idan wani abin ya shige masa duhu toh zai nemeshi kuma karya kuskura ya sanarwa su Hayat da tafiyarsa.Spanzy yace masa tuntuni ma ya sauya layi donsu.
Isarsu garejin yayi daidai da gama abinda yakeyi,dake akwai network mai karfi shiyasa nan da nan ya gama harma yayi musu transfer din kudi ayayin da su kuma suka aiko masa da room number.Bai wani sha wahala ba ya samu ya siye ticket,bakwai saura bus dinsu ta tashi.Sai da direba yaga tashiwarsu kafin ya tada mota ya tafi.
___________________________________
_*°•IKEJAH,LAGOS STATE•°*_
Hayat da Roughcoin kuwa tunda garin Allah ya waye suga shiga gari,suka shiga tallar motarsu suna nemar wanda zai siyeta,don Sam yanzu basu wani samun kasuwa kamar da,gashi duk wani kudaden hannunsu sun gama karewa,kuma adaren jiya Hayat yayi mafarki da mahaifinsa yana rokansa kan ya dawo gida,tofa shine hankalinsa ya daga,da safe ya labartawa Roughcoin mafarkin nasa,kuma yace shifa washeqari zai koma gida abinsa,sosai yayi nadamar irin wannan rayuwar daya jefa kansa hadda kukanshi,shima Roughcoin bawai ya saba da irin wannan rayuwar babun bane,bai saba da rayuwar buga buga ba amma kawai don Hayat yake kokartawa,gasu da result dinsu mai kyau amma sun kasa samun aikin kwarai ta gwamnati,toh da Hayat ya kawo masa wannan zancen,ai da sauri shima yace ya gaji zai koma gida gaban iyayensa amma yau su fita suje su siyar da wannan bus din tasu idan yaso su biya basussukan da ake binsu,sauran kudin kuma su samu na komawa gida.
Wannan karon Spanzy bai nemi Hayat ya gaya masa cewa ai mahaifinsa na kwance babu lafiya ba,don shima abinna Hayat ya soma bashi haushi,yace shifa koman iskancinsa bazai iya guduwa yabar gaban iyayensa kamar yadda Hayat yayi ba,ya biyewa wani katon Arne suka lula wata uwa duniya.Akansu ya sauya layi don kada suma sake samunshi.Ai kuwa idan sun nemeshi basa samunshi,Hayat ya daina samun duk wani information na gidansu,watannin mahaifinsa biyar kwance babu lafiya amma duk bashi da masaniya akan hakan.
*****
Toh! awannan ranar har karfe biyu na rana babu kanta,basu sami mai siyar bus din ba,ga wani irin yunwar dake addabarsu,gashi basu da ko sisi,akarshe yanke shawarar xuwa gidan wani abinci sukai inda anan ne suke cin bashi akodayaushe idan basu da kudi,idan sun samu kuma sai sukai daga baya dake sun riga sun zama customer,toh dayake kasuwarsu ta kwanan nan sai ahankali,ba wani samun kudin suke sosai ba,shiyasa matar ta dena basu abinci akan bashi,acewarta akwai kudaden da take binsu sosai akasa,don haka sai sun biya wannan kafin ta basu wani.Sun kwana biyu basa xuwa amma dake yau basu da wani option shiyasa sukaje.
Matar tana ganinsu tayi wani irin Zabura daga inda take zaune,da karfinta tace"Badman,Roughcoin you again in my shop?hope say no be food issue bring u here again?I hope say na my money u bring?" ta rike kunnenta daya tana ja don susan cewa da gaske take.
Roughcoin yace"Madam Becky pls help us jus for today,we promise to bring all ur money if we sell our bus today.... "
"Madam pls.... " Hayat ya fadi hakan kamar zai saki kuka,hannunsa daya rike da cikinsa wanda ke masa ciwo sosai don yunwa,dake komai yau basu saka aciki ba idan ka cire ruwa.Toh dayake Allah yayi madam Becky mace mai tausayi,sai ta amince zata basu amma wannan karon idan har kudinta ya dade basu kawo ba toh kuwa police ne zai rabasu don tabbas tasan inda suke zaune sai dai idan ba guduwa ne sukai daga nan ba.Babu bata lokaci kowa ya fadi abinda yakeso yaci ita kuma tayi serving nasu.Hayat ne ya soma gamawa,yacewa Roughcoin bari yaje yayi sallar azuhur amasallacin dake kusa kafin ya gama.Akullum idan sukazo cin abinci anan,idan har lokacin sallah ne tofa sai Hayat yaje masallaci kafin yaci ko kuma bayan yaci,kuma duk madam Becky na lure dashi da hakan.bayan wucewarsa ta dubi Roughcoin wanda sai kai loma yake bakinsa tace"Rough diz ur frnd bad buh him no dey play with prayer at all... ".
Dariya sosai Roughcoin yayi kana yace"Kinsan Waye shi?he's the son of the Niger state emir...... "
"What????" ta fada with a suprised face. "Son of the Niger state emir?then wetin bring him into diz useless life?"
Roughcoin ya gajerta mata labarin Hayatudden Bahago.
Cike da tausayi tace"Eyya I pity the guy,Roughcoin kai ba abokin kirki bane wallahi,gamuwarka da Yesu Sam bazaiyi kyau ba,how I wish him no follow ur advice at all,Rough biko let the child go back home pls,eya his mum died becuz of him.... " tuni hawaye ya soma shatato mata saman kunci na tausayinsa.Ana haka nefa sai ga Hayat ya dawo alokacin Roughcoin ya kammala cin abincinsa.Hayat yace masa ya tashi su tafi su kokarta su siyar da bus din sannan suzo su biyata kudinta don shifa ya rantse gobe goben nan zai koma gida.
Da sauri madam Becky tace"No! Leave the money,wallahi nina yafe harga Allah... " ta fada cikin hausarta da baya fita sosai.
Da mamaki Hayat yace"Because of wat ma?"
Cike da tausayinsa tace"Nothing! Just go back home my child cuz diz life dosnt fit you at all,accept ur destiny and go back to your family cuz they nid you,go go goooo my child..... "
Wani uban kuka ya subuce mata,da gudu ta shige cikin shagonta gudun kada ta tara musu jama'a.Hayat kuwa duk jikinsa ne yayi sanyi qalau da maganganunta,atake anan ya gano cewa Roughcoin ne ya bata labarinsa.Da sauri ya sanya 'yar yatsa ya dauke hawayen daya dan zubo masa.ahankali yace"Abraham let's go.... " yayi gaba abinsa don sosai maganganunta sukayi tasiri akansa,ya kudura aransa cewa koda kuwa zai kwana yana bara ne toh kuwa zaiyi don insha Allahu gobe garin minna yayi.
_*weldon мadaм вecĸy ĸeмa ĸιn тaĸa rawa awannan page dιn,jιnjιna agareĸι*_
_*ιna laвarιn prιnce ғarυq?*_ мυ вιѕнι🏃*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍* https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*°•yaυ ranarĸι ce dala,don нaĸa ĸι мaтѕo ĸυѕa ĸιyι нonoυrιng wannan ѕнaғιn,na мallaĸa мιĸι ѕнι нalaĸ мalaĸ,тanĸѕ ғor тнe тrυe love💑•°* ____________________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣6⃣*
Faruq bawan Allah kuwa sai misalin biyar saura kwata suka iso garejin Ikeja,ya gaji sosai don tunda yake arayuwarsa har ya girma haka bai taba yin doguwar tafiya irinta yau ba,awanninsu dai daya har goma sha daya akan hanya,kuma duk tsayuwar da ake tayi akan hanya don sanya abu aciki,toh shi babu abinda ya siya sai ruwan gora don ahalin yanxu burinsa kawai ya ganshi agarin lagos,sallace kawai yake fita yayi,ruwa kuwa lokaci xuwa lokaci yake dan kurba.Bayan kowanni awanni bibbiyu Haj.Babba ke ƙiransa taji yaya hanya?ko sun kai?sai shi kuma yace mata a'ah da saura.Abin har yazo ya soma isarta dake itama din bata taba xuwa lagos din ba,tace"Wai Faruq dama haka Lagos din keda uban nisa?sai kace zaku bangon duniya ganin yajuj da majuj?"
Murmushi kawai yayi yace"Hajiyata idan nakai zan kiraki.. " Toh tun asannan sun kwashi kusan awanni hudu basu sake waya ba,yanxu saukarsa kenan ah mota.Jan jikinsa yayi xuwa wani wurin zama inda aka tanadar domin matafiya,zamarsa keda wuya ya zaro hankicinsa daga aljihun wandonsa ya shiga goge zufar data tsassafo masa asaman goshi.Babu abinda yake buqata ahalin yanxu kamar ya samu lafiyayyiyar abinci yaci,bayan ya gama kuma ya nemi lafiyar gado,amma inaa! ayau dinnan yakeson ya soma yin abinda ya kawoshi kafin ma ya tafi hotel din da yayi booking online.Wani mai saida lemukan gora ya yafito da hannu,ya taho tare da ƙanwarsa dake dauke da tika tikan famke acikin roba.Saida ya siya yaci yayi kat dashi kafin ya latso Haj.Babba don gaya mata cewa yakai sabida hankulansu duk ya kwanta musamman na Abbansa.
Bayan sun gama gaisawa da Haj.Babba,sai data sake masa tsiya akan ita azatonta bangon duniya zasu ganin yajuj da majuj,dariya kawai yayi abinsa kana yace"Ina Abbana yake?Ya jikin nasa?da sauki ko?" ya jero mata tambayoyin nan alokaci guda.
"Da sauki sosai don yanxu likitocinsa suka zo dubashi kuma sun tabbatar mana da cewa akwai improvement.... "
Cike da farin ciki yace"Alhamdulillah! Wallahi harna ji dadi sosai,don Allah hajiyata taimaka kisa masa wayar akunne naji saukar numfashinsa kawai.... "
Murmushi tayi tare da jinjina irin kaunar da Faruq kewa mahaifinsa,sakala wayar tayi akunnen Mai martaba wanda yaketa sauraron hirarsu tun dazu,sai dai bata bari sunyi hirar Hayat agabansa ba,tace"Ranka shi dade Faruq ne keson yayi maka magana..... "
Daga can bangaren kuma Faruq yaji saukar numfashin Abbansa,wasu hawaye ne yaji sun tarun masa acikin ramin ido na tausayin mahaifinsa,cike da rauni yace"Abbana ubangiji Allah ya nuna mana ranar da zaka tashi tsaye akan kafafunka,Allah ya nuna mana ranar da magana zata sake fitowa daga baki mai kwatanta adalci da kuma fadin alheri,Abbana dama so nake na gaya maka cewa na isa garin Lagos kuma insha Allahu zanyi nasara kan abinda ya kawoni don ina tsananin son naga ka tashi daga wannan ciwon..... "
Bey kai ga karashe zancensa ba yaji ance"Faruq zaka soma ko?so kake kasa ya gane cewa Hayat kaje nema salon hankalinsa ya kara dagawa ko?" acewar Haj.Babba wacce itace ta wufce wayar daga kunnen mai martaba sabida speaker din aloud take shiyasa take iya jiyo duk abinda yake fada.
"Hajiyata don Allah kiyi haquri na kasa controlling kaina ne... "
Tace"Maza ka kama jiki kaje ka dubo mana inda kace yana zaune,duk yadda ake ciki ka kira ka sanar dani komai... "
"Naji Ummin Najmiy... " haka yake kiranta most of the time.
Ya sake cewa"Ammm.... Hajiya nace ba?... "
"Kace meh?" acewarta,shiru yayi mata,ya shiga sosa ƙeyarsa tamkar mara gaskiya.Ta gane nufinsa don haka daga murya tayi ta ƙirawo sunan Najmiy don ta tabbata muryarta yakeson yaji amma kunya ta hanashi fada.
Dake waje ta fito yin wayar,ta baro su Najmiy din awajen mai martaba,ai kuwa da gudu Najmiy ta fito don kiran Hajiyar ya daki dodon kunnenta dakyau.
"Ummii gani.... " mika mata wayar tayi tace mata Faruq keson magana da ita,cike da kunya ta soma ja da baya,Hajiya tace"Yauga iskanci ruwa-ruwa meye haka kikeyi?karbi man?"
Dakyar ta karbi wayar ta sakala akunne,ita kuwa Hajiya komawa wajen mai martaba tayi tana murmushin yarinta irinna Najmiy.
Ahankali ta furta"Assalamu alaykum_*Ya Hayati*_ (my life)"
Saukar da ajiyar xuciya yayi kana yace"Amin wa'alaikis salam _*Habib Albi*_ (Love of my heart).
Kuka ta fashe masa dashi tace"Ya Hayati don Allah ka yafemin,duk nice na sakaku cikin ƙalubalen da kuke ta fuskanta arayuwa,nice sanadiyyar barin Yaya prince karami gida,kuma nice..... "
"Ke wai meye haka?zaki soma haukarki ko?" ya katseta cikin tsananin fushin jin irin furucin daya fito daga bakinta.
Ahankali tace"Yayana kayi haquri karkayi fushi dani wallahi bazan kuma ba.. "
Murmushi yayi kawai,cike da qaunarta yace"Yauwa dats my gal,kiyi kokari ki kunna wayar dana baki kan na taho,idan na gama abinda nakeyi zan kiraki anjima.. "
"Okay,Ana bahibbak Ya Hayati (I love you my life). " ta fadi masa hakan ahankali.
Shima yace"wa'ana ahbuk ' aydaan Habib Albi (I love you too love of my heart)" hahaha duk itafa ta koya masa hakan.
Daga haka sukai sallama.Agogo ya duba yaga shidda saura,da hanzari ya mike ya fice daga garejin,abakin titi ya tare wani dan acab'a.Kiran spanzy yayi,kana ya baiwa dan acab'a wayar,ya gaya masa sunan unguwar da za'a kaishi donshi bai rike sunanta ba.Ai kuwa dan acaban ya gane unguwar,don haka babu wani b'ata lokaci sai gashi sun iso *'OJODU STREET'* inda anan ne su Hayat ke zaune.
Tun shigowarsu unguwar Faruq yaji kawai area din beyi masa bane becuz it's somehow crowdy kuma unguwar ya tara 'yan shaye-shaye ne sosai.Atake anan ya kara jinjinawa kokarin Hayat na iya rayuwa acikin irin wannan untidy environment din,acewarѕa.Wani dandalin samari ne ya hango zaune saman wani dogon benci kusa da wani shago,kowannensu rike yake da karan sigari yana zuƙa cike da kwarewa,hayaki na fita ta hanci da kuma baki.Har sun wucesu,sai kuma ya umarci dan acab'a daya dawo da baya.Adaidai wajensu ya dakatar dashi,yace masa yana xuwa.
Wani cikinsu ne ya ankarar da sauran ah sa'ilin da yaga Faruq ya nufosu,cewa yayi"Oboi! See one hot classic man... " sauran ne suka maida hankulansu ga Faruq suma suka shiga yaba haduwarsa.Gaisar dasu yayi sanda ya karaso inda suke,duk suka amsa.
Wani yace"Bros how may we help you?" yace"Am looking for a guy named Hayatudden and his friend Abraham,sana'arsu itace tukin bus,a Danfo driver & conductor.... "
Gaba daya sukace"Oh!You mean Badman & Roughcoin?mun sansu,nawa zaka ban na kaika gidansu?"
Wani aciki yayi masa wannan tambayar,shi kuwa Faruq wuta ne ya dauke masa na dan wani lokaci jin irin banzan sunan da Hayat ke amfani dashi anan,ji yayi wani uban kuka na neman taho masa,da sauri yayi ta maza ta hanyar danneshi yace"Money isn't my problem Mr.man,juz take me there... "
Su biyu aciki ne suka taso don masa rakiya,yaje ya sallami dan acab'a,cike da kasaita da jan'aji yabi bayansu,duk inda suka gifta sai an bi Faruq da kallo har ya bacewa ganinsu,don Faruq karshe ne akyau da kuma iya daukar wanka,Sam Sam basa kama ko kadan da Hayat,kowanne kamanninsa daban,haka kuma k'yawunsa daban,idan ka gansu tare ma kana iya rantsewa da cewa basu hada jini ba,sabida basa kama,haka kuma bazaka iya cewa ai wannan yafi wancan kyau ba,kowa naji da kyan da Allah yayi masa ne,haske kawai Hayat zai nunawa Faruq.Tafiyar mintuna biyar kawai sukayi sannan suka iso wani gida wanda kofarsa an garkameta da k'aton kwado,nan akace masa gidan da suke zaune kenan,amma sai gab da sallar magrib suke dawowa.Yayi musu godia tare da fitar da dubu biyu ya basu,cike da murna suka karba suna godia,kana sukayi gaba.Shi kuwa ya bisu da kallon Allah ya shirya.samin wuri yayi ya zauna akan wani dakali dake kofar gidan.
Akalla ya share kusan mintuna goma zaune anan,can yaga wata matashiyar budurwa wacce tasha dogon hijabinta har kasa da kuma niƙabinta,da alamu ma daga islamiya take sabida Qur'anin dake rike ahannunta ta fitar dashi daga cikin hannun hijabin.Dan madaidaicin gidan dake kusa danasu Hayat yaga zata shige,da sauri ya mike yana fadin "Malama assalamu alaykum don Allah tambaya nake... "
Dakatawa tayi,ta kallo inda yake tace"Amin wa'alaykas salam ina jinka" ta fadi hakan cikin wani irin zazzakar muryarta.Shi kansa Faruq saida ya yabawa zakin muryarta kafin yace"Don Allah ko kinsan wani abu agame da wa'enda suke zaune acikin wannan gidan?" ya fadi hakan tare da yin nuni da gidansu Hayat.
Sai data kwashi kusan dakiku biyar kafin tace"Da fari dai meye alakarka dasu kafin na gaya maka komai?"
"Tambaya kan tambaya halin dan Nigeria Kenan,wallahi ni abinda na tsana kenan arayuwata wai kayiwa mutum tambaya amaimakon ya maido maka da amsar tambayarka,a'ah sai dai....."
Bai karashe fadarsa ba kawai yaga tasa kai tayi shigewarta cikin gidan ba tare da ta tankashi ba.Dogon tsaki yaja tare da furta"I wonder why some people behave like animals,yanxu mena fada anan da har ya bata mata rai?" (hahaha! A rhetorical question without an answer dear Prince Faruq).
Komawa wajen zamansa yayi,time to time yake duba agogon dake makale ah tsintsiyar hannun hagunsa,it's exactly 6:25pm.
Ita kuwa tana shiga cikin gida tsananin b'acin rai ma ya hanata gaida wanta da kuma mahaifinta wanda ake kira da 'Tsoho',wucesu tayi zata shige daki,da karfi Yah Rilwan yace"Ke! Maryam lafiyarki kuwa zaki shigo cikin gida babu ko sallama balle musa ran zaki gaidamu?iyyeh tambayarki nake?"
Daga nikabinta sama tayi,anan naga fuskarta,babu laifi tana da dan kyanta,ashagwab'ance tace "Yayah kayi haquri wallahi wani ne ya bata min rai awaje,wai tambaya yake akan samarin dake zaune acikin gidan can shine nace sai ya gayamin alakarsa dasu kafin na gaya masa komai akansu,shine ya hauni da fada ni kuma abin yaban haushi na shigo abina.. "
Tsoho yace"Maryam kina da gajen hakuri wallahi,wato dayake ke din bakison ayi miki fada arayuwarki shiyasa kika wulakantasнι kikayi shigowarkι,toh Allah ya shiryeki,kai Rilwanu tashi kaje ka dubo ko wanene ke nemansu?kuma meyasa yake nemansu din?don tunda yaran nan suka soma zama ah gidan nan ban taba ji ko kuma ganin wani mutumin kirkin yazo nemansu ba... "
"Toh tsoho bara na dubo... " ya mike ya fice,ita kuwa Maryam dan guntun tsaki ta saki kana tayi shigewarta daki don ita arayuwarta ta tsani aci mata fuska kamar yadda Faruq yayi mata.
_*тoғa! wacece мaryaм dιnnan?*_
_*ιna ĸυмa laвarιn нayaт da roυgнcoιn?*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕* ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°* https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ ____________________________________ 💥
_*°•dιz page ιѕ dedιcaтed тo all тнe нaғѕaт's all over тнe gloвe,ιғ υr naмe ιѕ нaғѕaт,нaғѕυ,нanѕaι & waтever den dιz page ιѕ υrх,ιna yιnĸυ мy naмcιeѕ,'тнe вeaυтιғυl вaвy lιoneѕѕ' daтѕ тнe мeanιng oғ oυr naмe•°*_
*Թɑցҽ 1⃣7⃣*
Mal.Sani Falalu wanda akafi sani da 'Baba Tsoho' haifaffen 'Dumawa' ne wanda karamar hukumar 'Minjibir' ne dake jihar Kano.Su biyu ne kawai iyayensu suka haifa,dashi da kuma ƙanwarsa wacce ake ƙira da Inna Ladidi,ya taso yaga mahaifinsa yana noma,wato dai manomi ne,toh dayake shi kadai ne namiji agabansa,sai ya dorashi akan wannan sana'ar,doya ne,masara ne,shinkafa dadai sauransu duk suna nomawa,bayan sun girbe,sai sukai cikin garin kano su siyar,ana haka ne fa har Allah ya habbaka kasuwancinsu suna samun kudi dakyau yadda ya kamata,ita kuwa Ladidi tuni akai mata aure da wani dan makobcinsu wanda ya nuna yana sonta,as time goes on da aka ga kokarinsu na siyar da kayan masarufi,sai gwamnati ta basu wani dan filli akasuwar kano,sai suka kafa rumfa anan,shi Sani aka bari anan ya dunga saidawa,ayayin da mahaifinsa ke kawo kayan ya jibge masa.Ba'a wani jima da dawowarsa garin kanon ba yayi aurensa,ya aure wata 'yar fillo mai kawo musu fura da nono na sayarwa.
Wasa wasa saida suka kwashi kusan shekaru goma kafin Fatoumata matarsa ta haifi danta na farko wanda aka sanya masa suna 'Rilwanu',alokacin kuwa mahaifinsa mal.falalu ya rasu,sai ya zamana shi ke komai na bangaren kasuwancinsa ayanxu,Rilwan kuwa an sakashi amarantar boko har zuwa matakin diploma,ah inda ya karanci electrical engineering,Shima ya soma sana'ar saye da siyarwa ta kayan wuta ta lantarki,abu har lagos yana zuwa sarowa,daga baya kuma yazo ya koma Lagos da sana'arsa dindindin, acan ya amshi hayar shago,ya shaketa da iri irin kayan electronics,sosai arzikinsa ya bunkasa wanda har ginin wani madaidaicin gida yayi inda da zarar yayi aure zasu zauna anan da iyalinsa,ya sake ginin wani dan karamin gida akusa da nashi,gidan zaman mutum daya ne,wato daki daya ne sai kuma kitchen da bayi awaje,bayan ya komo kano yayi auransa kana ya dauki matarsa Ummi Aisha suka koma can garin Lagos.
Wani abin ikon Allah kuma sai alokacin Fatoumata ta sake haihuwa,wanda har sun cire rai da sake haihuwar don daga ita har Mal.Sani sun soma dan manyanta.aka sanyawa yarinya suna *'Maryama'*,maryam ta taso cikin gata ta kowanni bangare,iyayenta da kuma yayanta wanda ahaife ya haifeta duk suna ji da ita,tana ss1 asecondary mahaifiyarta Fatoumota ta rasu bayan tayi yar karamar jinya.
Mutuwarta ta girgiza tsoho sosai don yana bala'in son matarsa sosai,bayan wani dan lokaci da rasuwarta,Rilwan yazo ya dauke tsoho da Maryam ya maidasu Lagos.Yadda akai Sani tsoho ya ijje sana'arsa ta kayan masarufi Kenan. Acikin gidan da Rilwan ke zaune da matarsa,dama akwai extra dakuna biyu,sai aka baiwa tsoho daya,dayan kuma aka baiwa maryam.alokacin tana ss2 dinta ne sanda suka komo Lagos da zama,shine aka samo mata wata makarantar private mai dan saukin kudi aka sakata da kuma islamiyyar da aka samo mata dake kusa da unguwar.
Maryam yarinyace nutsasstsiya,Sam bata da rawar kai kamar na 'yan matanmu na zamanin nan,babu ruwanta da kowa ne idan ba tsoho da wanta Rilwan ba wanda ya zame mata tamkar uba,tsoho kuma ta maidashi kakanta ba uba kuma ba,Akodayaushe idan har zata makarantar islamiya ko kuma idan an aiketa bata taba fita ba tare da dogon hijab da nikabi ba,haka ma idan har zata boko,tofa tun daga gida take sanyawa,da zarar ta kusa da makarantar kuma sai ta cire ta saka cikin School bag dinta,idan an tashi kuma saita mayar,haka dai take gudanar da rayuwarta cikin tsananin kamun kai da kuma nutsuwa,sai dai wani abu ga Maryam shine,ko kadan bata daukar kaniya,Sam batason rainin wayau,keta,cin fuska da kuma wulaqanci.kawarta daya itace 'Hauwa',kuma unguwarsu daya.ѕнeĸarυn Maryam goma sha bakwai,ayanxu haka tana gaba da rubuta Ssce wa'ec dinta ne
Maryam ta tsani mashaya arayuwarta,k'yamarsu take sosai shiyasa su Hayat basu taba burgeta ba dake su Hayatun ne ke haya awannan karamin gidan nasu.Toh dayake Hayat ma baya shiga sabgar mata shiyasa baima san da zamanta ah unguwar ba,shidai barshi da shaye-shayensa amma babu ruwansa da 'yan mata,roughcoin ne dai dan kwashe kwashe.
Akodayaushe idan yamma ta kunno kai,sai kaga Tsoho ya fita kofar gida da kujerarsa ya zauna akarkashin wata bishiyar mangwaro yana dan shan iska,toh wasu lokuttan idan har Hayat na gida tofa yakan fito waje shan iska don sosai wannan bishiyar ke bada wata irin ni'imtacciyar iska,toh sai su hade da tsoho anan,toh har takai sai kaga su zauna suna hira,har Tsoho yayi ta masa fada kan yabar shaye-shaye,idan har ya amsa masa awurin akan cewa ya daina,tofa kuwa yana barin wajen zai cigaba,Tsoho na son Hayat sosai da sosai,don wasu lokuttan ma tare zuwa masallaci kuma su dawo atare,sai dai Hayat bai taba bashi labarin komai agame da kansa ba,haka ma Tsoho bai taba neman jin wani abu agame dashi ba,nashi kawai yana masu fatar shiriyace.
Bayan saida kayan electronics,Mal.Rilwan na kiwon kaji da kuma tantabaru acikin gidansa,matarsa kuma Ummi Aisha sana'arta itace saƙa,agefe daya kuma tana saida su minerals,kunun aya,zobo,pure water da dai saraunsu,kuma alhamdulillah tana samun kasuwa sosai.Ya'yansu uku kuma duk maza ne.
___________________________________
*°•мυ ĸoмo ĸan laвarι•°* Mal.Rilwan na fita waje ya soma dube dube yana mai son ganin bakon da Maryam tace yana nemansu Hayat,ai kuwa charaf! Idanuwansa suka sauka kan Faruq wanda ke zaune ya saddar dakai kasa yana tunane-tunane.Sannu ahankali ya taka har xuwa inda yake zaune tare da dan taboshi,adan firgice ya dago kai yana dubansa.
"Yi hakuri na baka tsoro ko?" acewar Mal.Rilwan,murmushi kawai Faruq yayi abinsa,sukai musabaha.
Mal.Rilwan yace"Kaine wanda ke tambaya akansu Hayatu samarin dake zaune acikin wannan gidan?" ya fadi hakan tare da nuni da gidansu Hayatun.
Murmushin takaici Faruq ya saki tare da fesar da wani iska daga bakinsa kana yace"Ta fada muku kenan?amma shine ita bata iya tsayawa ta saurareni ba tayi shigewarta ciki,wannan sam ba dabi'a mai kyau bace.... "
Da sauri Mal.Rilwan ya tari numfashinsa"Gaskiya ne bata kyauta ba kuma nayi mata fada akan hakan,amma kasan dai tambayar da tayi maka ko kadan batayi laifi bako?dole ne tasan alakarka dasu sannan abinda ke tafe dakai kafin ta fada maka komai akansu,don haka da fatar zaka mata k'yakkyawar fahimta da kuma yi mata uzuri akan hakan?"
Sai ayanxu Faruq yaga rashin dacewar daukar zafi da yayi,da gaskiyarta kam dole ne tasan alakarta dashi kafin ta gaya masa wani abin kai tsaye,atake anan kawai yaji yarinyar tayi mugun birgeshi.(Kalubale gareku,wen you first meet a stranger,kuma ya tambayeku abu,karku kuskura ku bashi amsa kai tsaye becuz some are evil,Allah yasa mu dace).
Bayanin kanshi yayi masa azuwan ai shi din dan'uwa ne ga Hayat,kuma yazo ne don tafiya dashi gida,Cike da farin ciki Mal.Rilwan yace"Allahu Akbar! yau Allah ya karbi adduarmu nida tsoho,akullum bakunanmu basa gajiya da rokarwa 'ya'yan nan addu'ar shiriya da kuma komawa gaban wani nasu,musamman ma Hayatu wanda ga dukkan alamu ya nuna rinjayarsa akayi xuwa cikin wannan kazamar rayuwar,bismillah Mal.Faruq shigo muje ciki tsoho ya ganka."
"Assalamu alaykum ya jama'atul muminin.... " Shine abinda Faruq ya furta ah sa'ilin da suka kutsa kai cikin gidan sosai,tsoho ne ya amsa masa don shi kadai ne ke zaune atsakar gida,yau bai fita shan iska ba.Tabarma Mal.Rilwan ya karbo wajen uwargidansa ya shimfida akusa da Tsoho,yace"Bismillah! Mal.Faruq zauna... "
Ya amsa tayinsa ya zauna,suka shiga gaisawa da kyau sosai,shi kuwa Mal.Rilwan yaje ya karbo lemun da Ummi Aysha ke saidawa da kuma ruwa asaman tray ya kawo ma Faruq.Ruwan kawai Faruq ya iya dan tabawa,Mal.Rilwan yayiwa Tsoho bayanin Faruq din da kuma abinda ke tafe dashi.
Shima tsoho kabbara yayi kamar yadda Rilwan yayi,cike da farin ciki Tsoho yace"Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Haqiqa bazan iya misalta maka tsananin farin cikin dana shiga ba ayau,wato yau watarana ce da bazan iya mantata ba harna kare rayuwata adoron kasa,Hayatu mutumi na ne sosai,kai na daukeshi ne tamkar dan cikina,tarayyarsa da wannan katon arnen yana min ciwo sosai donna tabbata shine ya rudeshi suka bar gida,sai dai kuma bayan shaye-shaye sam bashi da wani mugun hali don ko budurwa ma ni ban taba ganinsa da ita ba,sallar nan kuwa bata taba wuceshi,wasu lokuttan ma tare muke jerawa muje masallaci,kuma duk inda yake muddin yamma ta kawo kai,ma'ana ana gab da kiran sallar magrib tofa zaka ganshi ah unguwa ya dawo,har gida zai shigo idan bai ganni awaje ba yace tsoho na dawo taso muje masallaci,bayan mun idar kuma kafin ayi kiran sallar isha'i zaka ga ya hau karatun Qur'ani,bazai dakata ba har sai anyi kiran isha'in.Ayau Ina mai Farin ciki da har wani nashi ya nemi inda yake ya kuma taso har yazo nan don tafiya dashi,ubangiji Allah yayi maka albarqa Umaru,Allah yasa ka wanye da duniya lfy.. "
Cikin muryar kuka Faruq yace"Amin amin baba,kuma dalilin barinsa gida shine..... "
Da hanzari Tsoho ya katseshi yace"Kai Umaru kul bana son jin komai,banda tonon silili ka koyi boye sirrin gida,kai bama gida kadai ba,ka koyi boye sirrin wani,Sam babu kyau tone-tone... ". Sai kuma Faruq yaji haushin kansa da abinda yayi niyyar fada ada,subutar baki ce.
Tsoho ya umarci Rilwan daya kirawo masa Maryam tazo ta baiwa Faruq haquri,dakyar ta fito sanye da dogon hijabinta da kuma nikab,ta tsugunna tana baiwa Faruq haquri,acikin nikab dinta kuwa murguda masa baki take tayi,shi kuwa bawan Allah ahankali yace"Tashi kije komai ya wuce,nima don Allah ki yafemin... "
"Bakomai nima komai ya wuce" ta fada tare da mikewa at once tayi gaba.
Adaidai lokacin kuma aka soma kiraye-kirayen sallah,tsoho ya dubi Rilwan yace"Maza Rilwanu tashi ka debo mana ruwa abutoci mu daura alwala kila ma mu hade dashi acan masallaci donna tabbata sun dawo.. "
Da sauri sauri Mal.Rilwan yaje ya debo musu ruwa abutoci ya kawo musu,duk suka daura alwala,jakar Faruq kuwa Mal.Rilwan ne ya karba yakai dakinsa,kana suka fito suka nufi masallaci wanda bashi da wani nesa da gidan.
** Su Hayat kuwa sai wuraren karfe shidda suka samu mai siyar bus dinsu,kuma awulaqance aka siyeta don anga suna tsananin buqatar kudi,90thousand aka siye wannan katuwar bus din kuma dakyar aka siyeta ahakan don bus din tana da dan matsala,tun acan suka ware dubu hamsin wanda zasu baiwa Mal.Rilwan sauran kudin gidan da ake binsu,dubu biyu kuma na Mal.Miskala kudin sigarin da ake binsu kenan.Wuraren shidda da rabi suka shigo cikin unguwar akan dan acab'a wanda sukai two pack,adaidai shagon Mal.Miskala suka sauka suka biyashi kudinsa,kana suka siyi biredi da kosai akusa da shagon,sannan suka nufi gida wanda tuni har an tada kabbarar sallah,akofar gida suka rabe,Shi Hayat ya nufi masallaci da gudu-gudu don kada ya rasa jam'i ayayin da Roughcoin ya shige gidansu Tsoho don siyar musu lemun kwalba gun Anty Ummi kamar yadda ake kiranta.koda ya shiga,ta siyar masa da komai ba tare da ta labarta masa komai ba,don Ummi Aysha macece wacce babu ruwanta da gulmace-gulmace ko kuma shiga sabgar daba tata ba.
Hahaha! acan masallaci kuwa,Hayat adaidai bayan Faruq ya tsaya yayi sallarsa,raka'a daya kawai ya samu,don haka adaidai lokacin daya kai sujjadar karshe,alokacin su Tsoho suka fito daga masallacin suka nufi gida,tsoho sai cewa yake"wai yau Hayatu lafiya bai dawo da wuri ba?basu taba kaiwa warhaka bafa agari?"
Suna isowa kofar gida,tsoho ya haskawa kofar gidansu toci yaga kofar abude take don babu wannan kwadon kuma,da mamaki ya dubisu Faruq wanda suma kallonsu akan kofar take yace"Laaah!kunga ashe sun dawo ina nan inata kumfar baki,amma meya hana Hayatu xuwa masallaci yau?ku jira bari na duboshi.. "
Kafin suyi wata magana tuni ya shige ciki,Roughcoin kadai ya sama acikin dakin ya baje akasa sai cin biredinsa da kosai yake,agefe daya kuma lemun kwalbarsa ce wacce time to time yake dan kurba,ya dume gida da wakar *'Do me Do me'*.
Yana ganin tsoho yayi saurin rage volume don yasan halinsa sarai yanzu zai iya hawansa da fada."Tsoho yane?meh kakeso ne?idan kuma kudinku ne ka biyo toh kasha kuruminka har gida zamu kawo muku shi cikakke anjima... "
Tsoho yace"Dalla rufemin baki mutumin banza kawai,Hayatu nazo nema ina yake?"
"Mosque.... " shine kawai abinda ya iya cewa,shi kuwa Tsoho bai sake cewa komai ba ya fito abinsa,ya gayawa su Faruq din yadda sukai da Roughcoin.
Tsoho yace"Amma abin da mamaki don ko mai kama dashi ban gani ba amasallacin,kodayake ina jin daga baya yazo,kuma nasan sai bayan isha'i zai dawo,Kumu koma masallacin.... "
Suka sake komawa masallacin,koda suka koma sun hangoshi ne can gaba yana karatun Qur'ani cikin zazzakar muryarsa,basu dakatar dashi ba sukayi zamansu awaje,saida aka kira sallar isha'i sannan ya dakata,bayan mutane sun taru aka tada sallar,sai asannan ne su Tsoho suka shige ciki don basu san Hayat yaga Faruq yanzu sai sun kai gida.
Ana idarwa su suka soma fitowa suka nufi gida,daga can wani gefe akusa da gidan suka tsaya,wajen duhu duhu ne,can sai ga Hayat yana tahowa,sai da suka bari ya shige cikin gida kana suka take masa baya.
_*тoн мy ғιғυl ya ĸυĸe ganιn нadυwar prιnce ғarυq da ĸυмa prιnce нayaт zaι ĸaѕance?*_
ĸυ вιyo
*тaĸυ*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα°•*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ __________________________________ 💥
_*°•wαnnαn pαgє dín mαllαkínkí nє mч lσvlч ukhtí 'rαmlєrh',ínα ѕσ kí ѕαní cєwα ѕíѕ hαfѕαt dínkí tαnα míkí ѕσ mαrα íчαkα wαndα вαвu αlguѕ αcíkí,uвαngíjí Allαh чαвαr qαunα dα хumuncí mαí dσrєwα,αmєєn°•*_
*Թɑցҽ 1⃣8⃣*
_*°αddu'αr nєmαr tѕαrí dαgα αzzαlumαí kσ kumα mαhαѕѕαdα👇°*_ _*°•Allαhummα rαввαѕ-ѕαmααwααtíѕ-ѕαв'í,wαh rαввαl-αrѕhíl-αzєєm,kun lєє jααrαn mín(ѕαíkα αmвαcí ѕunαnѕα),wα'αhzααвíhí mín khαlαα'íqíkα 'αn чαfrutα 'αlαччα 'αhαdun mínhum 'αw чαtghαα 'αzzα jααrukα,wαjαllα thαnαα'ukα,wα lαα'ílαhα 'íllα αntα•°*_
💥💥
---------Har Hayat ya daga yalalon labulen dakinsu zai shige,sai kuma ya jiyo sallama daga bayansa,muryoyi fiye da biyu ne suka daki dodon kunnuwansa amma yafi saurin shaida muryar Tsoho,don shi da karfinsa ya doka sallamar.Cike da fara'a Hayat ya saki labulen ya juyo yana mai fuskantarsu dakyau,yace"Ayyah baba tsoho abokina kaine tafe?Don Allah kayi haquri yau banzo kiranka muje masallaci ba wallahi yau ban dawo da wuri bane,hasalima yau sallah raka'a daya ce kawai na samu ta magrib,ina can har isha'i amma ko mai kama dakai ban gani ba,nace toh yau Tsoho lafiya kuwa ban gansa amasallaci ba?yanzu haka ma so nake naci abinci sannan na shigo dubiyarka sannan na damkawa Yah Rilwan raguwar kudin gidansa.. "
Shi kwata-kwata hankalinsa ma baya ga mutane biyun dake tsaye agefen tsoho,kuma ko kadan yaki baiwa Tsoho damar magana,yacigaba"Tsoho albishirinka?gobe Zan koma....... "
Wutar da nepa suka kawo ne ya katse masa maganarsa,kuma wutar lantarkin dake can sama ah bangon kofar dakinsu ya matuqar taimaka wajen haskaka masa fuskokin duka halittun dake tsaye agabansa.Ido cikin ido suke kallon juna da prince Faruq.
Akalla sun kwashi kusan daƙiƙu hamsin suna kallo-kallon junansu,Hayat shine wanda ya soma kawar da dogon silent din ta hanyar furta" *'YAYA PRINCE......... '* Ya fadi hakan cikin ƙaryewar murya,sannu ahankali wasu hawaye masu dumi suka soma gangaro masa saman cheeks.Jaa da baya ya soma yi kadan da kadan fuskar nan tasa shimfide take da tsansar mamakin ganin Faruq agarin Lagos kuma wai acikin gidansu,cikin rashin sani yaci karo da wata 'yar karamar kujera dake bayansa,ai kuwa kiris ya rage ya fadi,amma kafin yakai kasa sai yayi saurin sanya hannu ya dafe Bango.
"Hayatu kabi ahankali karka fadi don Allah... " acewar Tsoho.
Tsoho ya maida kallonsa kan Faruq wanda yayi mutuwar tsaye,ruwan hawaye ne kawai keta bulbulowa saman kuncinsa,kuma har yanxu bai dauke kallonsa akan Hayat ba.Duk da cewa dare ne amma wutar lantarki ta taimaka wajen hasko masa yadda kamannin Hayat ya sauya,ya mugun tara sumar kai,haka ma kasumbarsa ta cika fuskarsa,abu dai kamar ba Hayatudden Bahago dan Qayun daya sani ba.
Maganar tsoho ce ta maido da hankalinsa daga duniyar nazarin daya shiga akan Hayat,cewa yayi"Mal.Faruq mu zamu koma gida,zamu baku wuri ku sulhunta,idan har kun daidaita saiku samemu acan... "
"Toh Baba" shine kawai abinda ya iya furtawa cikin dauriya.
"Kai Rilwanu muje.. " acewar Tsoho,har sun juya zasu fice sai kuma Tsoho ya tuna da wani abu,ai kuwa da hanzari ya koma da baya,ya nufi kofar dakinsu Hayat,daga labulen sama yayi,can ya hango Roughcoin raƙube abango,jikin nan nasa sai aikin maƙyarƙyata yake don duk yana ta jin conversation dinsu dake ta wakana atsakar gidan,wato dai *'PRINCE UMAR FARUQ BAHAGO'* is here kenan,lol yasan kashinsa ya bushe shiyasa ya shiga cikin tsantsar tashin hankalin nan.
Dariyar mugunta Tsoho yayi kana yace"Shege katon arne ashe dai kaji komai,dan'iska mayaudari kawai,don wallahi ba'a gaya min ba amma nasan dasa hannunka acikin lamarin bawan Allah Hayatu,wallhi karshenka baza tayi k'yau ba,ni wallahi harna hango mazauninka acikin gidan wuta,zaka fito ne ko kuwa saina shigo na sameka anan?" hahah! Tsoho ya sami opportunity don ko dama can shida Roughcoin ko kadan basa shiri,Roughcoin sam baya daraja Tsohon,har ce masa yake Tsohon banza.
"Baba hadda son zuciyar shi Hayatun aciki don haka karka gama dora laifin akan abokinsa.... " haka yaji Faruq ya fada cikin wata kakkausar murya.Jikin Tsoho ne yayi sanyi qalau,ahankali ya juya yaja hannun Rilwan wanda nashi kawai kallo ne yake tayi,har sun kai kofar fita sukaji Faruq yace"Baba ina fatar ba fushi kayi da kalamaina bako?idan kalaman nawa sunyi tsauri ne da yawa toh don Allah ina nemar yafiyarka.. "
Harga Allah ba fushi Tsoho yayi ba,jikinsa ne kawai ya soma tsinkewa da lamarin Hayat,ya tabbata akwai magana akasa sosai akanshi,wai ma don bai san cewa mahaifiyarsa ta rasu akanshi ba kenan.
"Dana wallahi ba fushi nayi ba,nidai idan kun gama ina jiranku agida... " yasa kai ya fice ayayin da Rilwan ya take masa baya.
Roughcoin ne yayi shahada ya fito aguje saura kiris suci karo da Faruq,yayi kofar fita daga gidan ah 180 kai kace ko wani babur ne😂.
Hakan kuwa da yayi ba karamin dariya ya baiwa Faruq ba,harda kwallansa kuwa,ya rakashi da"Bloody monster daka bi ahankali donni bata kai nake ba,infact bani da deal dakai don hadda son xuciyar kanin nawa aciki,kadai je ka gyara rayuwarka if not kana iya karewa agidan wuta,asararre kawai.... "
Yana gama fadar hakan ya dauke dariyarsa,alokaci daya kuma ya juya yana fuskantar Hayat.
Ahankali ya furta"Hayatudden Bahago...... "
Cikin rawar murya yace"Ya... yah princeeeee waya gaya maka inda nake?"
"Ibrahim spanzy.. " Faruq ya bashi amsa atakaice ah sa'ilin daya watsa hannayensa cikin aljihun wandonsa.
Kafin Hayat ya gama shanye mamakinsa kawai yaji Faruq ya cigaba"Spanzy shine wanda ya gayan komai,garin da kake da kuma unguwar da kake zaune,da kuma sana'ar da kake yi,u hav completely turned into an enormous drunker,what an outrageous and shameful thing?the whole prince of sarkin minna has turned his life into a mess!!! Shame on you Hayatudden freaking Muhammad Khamis Bahago.. "
Hayat ya karya gwiwowinsa zuwa kasa tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka tamkar wani karamin yaro,sosai yayi nadamar biyewa zugar aboki kamar Roughcoin.
"Wai duk akan 'ya macece kabar gida?'ya macen ma da bata san kana yi ba?'ya macen da ayanxu hankalinta nacan wani wuri ne daban ba'a kanka ba?macen da take can tana rayuwarta hankalinta kwance kai kuma kana nan kana fuskantar kalubalen rayuwa akanta?bayan bata San kana yi ba?akanka mahaifiyarka ta kamu da congestive heart failure har yayi sanadiyyar barinta duniya,kuma abin mamaki da haushi wai duk kana da information akan hakan amma don toshewar kwakwalwa da kuma rashin imani ka kasa dawowa gida.... "
Matsawa yayi kusa da inda Hayatun ke zaune,shima ya karya gwiwowi zuwa kasa kamar yadda yaga Hayatun yayi,in otherwords,kneels down nake nufi,kana ya cigaba"Hayatu mahaifiyace fa?wacce ta dauki cikinka for good 9months,alokacin da zata haifoka kuwa kafarta daya aduniya dayan kuma alahira ne,alokacin ta fidda rai ne ga rayuwa,tayi nakudarka cikin radadi da kuma azaba,ta raineka cikin tsananin sonka da qaunarka kasancewarka dan data haifa kwara daya tak aduniya,taci kashinka,tasha fistarinka,ta tsotse majinar hancinka don kawai kayi looking good,dede da minti daya bata qaunar taji kukanka,da sauransu dai,shine kai kuma Hayatu ta hanyar da zaka saka mata kenan?ta hanyar kasheta da bakin cikinka?ta hanyar banzantar da mutuwarta?Brother u surely need prayers and deliverance.... "
"Akanka kuma mahaifinmu ke can kwance ciwon stroke ta kamashi,wai duk akanka kai daya Hayatu?kai ne kawai dan da suka Haifa?ta hanyar da zaka saka musu kenan ta kashesu da bakin cikinka?well,ni inason iyayena idan kai baka sansu,nazo nan ne ba don komai ba sai don na rokeka ka bini mu koma gida don kaine maganin lalurar Abba mai martaba,pls pls Hayatu bana son na rasa mahaifina don Allah ka biyoni mu koma gida... "
Da sauri Hayat ya rungumo dan'uwan nasa tare da bude wani sabon shafin kukan,kana yace"Yayah prince I hate myself for the cause of all this,dan'uwa nayi nadama sosai don Allah ku yafeni,bin son xuciya bai kareni da komai ba illa jefani cikin bala'i,nayi sanadin barin mahaifiyata duniya,haka kuma nayi sanadin da mahaifina ya kamu da ciwon shanyewar barin jiki,infact na jefa duk wani masoyina cikin kuncin rayuwa akaina,tirr! da haihuwata Yayah prince,nasan da'ace Haj.karama na raye,watakila zatace, _*'Hayatu dana san haka zakazo ka zama arayuwa harka samu kuka akanka,toh kuwa dana dade da barar da cikinka tun kana gudan jini'*_.... "
Da karfi faruq yace"Shut up! Hayat,zaka soma sakin layi ko?kodayake I won't blame you becuz I can see dat harwa yau bakasan meye kaddara ba,haka kuma baka san meh kalmar *'HAKURI'* da kuma *'DANGANA'* suke nufi ba,amma nevertheless,ina maka addu'a Allah yasa nan gaba ka sansu duka,sannan kuma kasan lokacin daya dace kayi amfani dasu... "
Tsagaitar da kukansa yayi,ya koma 'yar shessheka kana yace"Dan'uwa kayi haquri dama ina da niyyar komowa gida gobe don gabaki daya rayuwa ta juyan baya,haqiqa nayi nadama sosai Yayah prince,don Allah ka tashi mu wuce ma yanxu,inason naje ga Abba mai martaba na nemi yafiyarsa... " kan Faruq yayi magana tuni ya mike,har zai shige daki yaji kawai Faruq ya ruƙo hannunsa.
"Ina zaka?" acewar Faruq.
Ya juyo yana dan dubansa kafin yace"Hado kayana zanyi nazo mu tafi.. "
Murmushin takaici Faruq yayi,yace"Lallai Hayat na yadda baka da hankali,yanxu fisabilillahi sai mu dau hanyar doguwar tafiya acikin wannan daren?mu sami motar ma ah ina?ko azatonka amotar gida nazo?toh don ka sani amotar gwamnati nazo,kuma yasin bazaka bini da kayan kwarmasanka ba,jeka ciki ka kwaso important documents dinka kazo kawai mu tafi,sannan ka rufe gidan muje ka damkawa landlord makullin gida,nawa ne ma suke binku don kamar dazu naji ka ambaci cewa zaku basu sauran kudin gida da ake binku?"
Ahankali yace"Dubu hamsin ne. " Jinjina masa Faruq yayi kana yace"kuma kana dasu?don gashi dai abokin cin mushen naka ya gudu ya barka aciki."
"Eh gasu acikin aljihuna cikakke don yau muka saida bus don mu samu mu biyasu kudinsu,sauran daya rage kuma muyi kudin motar komawa gida.. " ya fadi hakan tare da fiddo kudaden ya nunawa Faruq.
Murmushi kawai Faruq yayi kana yace"Hayatudden Bahago kaga rayuwa,fatana ayanxu shine Allah yasa hakan ya zamo babban darasi agareka da kuma duk masu bin son xuciya kamarka.. "
"Ameen amin,Yayah kayayyakin ciki fa su kuma ya za'ai dasu?"
Faruq yace"Masu gidan sa rabawa almajirai don wallahi bayan documents dinka ko tsinke bazaka bini dashi ba,kuma kamin sauri don ahotel zamu kwana,washeqari kuma mu Kama hanya... " Da sauri-sauri Faruq ya shiga ciki ya kwaso credentials dinsa,ya dudduba dakin da kyau yaga ashe Roughcoin ya kwashe nashi,ko bin takan kosai da biredin da Rough ya rage masa beyi ba ya fito ya sami Faruq,suka fito Hayatu ya kulle gidan,kana suka shige gidansu Tsoho,alokacin agogo ya nuna 9:35pm.
Tsoho na ganinsu ya shiga kabbara da nuna tsantsar farin cikinsa afilli,yace"Masha Allah abu yayi kyau sosai,naji dadi sosai da kuka daidaita kanku,ubangiji Allah yayi muku albarqa,Allah yasa kufi karfin xukatanku akodayaushe,haqiqa Mal.Faruq ka cika dan'uwa na gari daka ceto rayuwar dan'uwanka daga halaka,Allah yayi maka sakayya da gidan aljanna,kai kuma Hayatu ba karatu ba,ba komai ba,ka bi rudin abokin banza,kun shigo cikin rayuwar kashe wando,yanxu ba don 'yar sana'ar tukin nan da kukeyi kuke dan samun kudi ba da kuwa rayuwarku ta zamo kalar tausayi,don Allah abinda nakeso dakai shine kabi dan'uwanka ku koma gida,kuma koman rintsi koman wuya karka taba mantawa da irin halaccin da Umar Faruq yayi maka arayuwa,Faruq masoyinka ne na gaskiya,karka kuskura ka butulce masa nan gaba,Hayatu ina mai gargadinka da kakkausar murya daka guji bin son xuciya da kuma hulda da abokanan banza wanda gashi ayanxu sun kaika sun baro,dadin abin ma ka rike addini shiyasa abin yaso da dan sauki,kudin gida kuma mun yafe muku harga Allah,ubangiji Al-gafur Al-rahim ya yafe mana duka gabaki daya.... "
Babu wanda jikinsa beyi sanyi ba da kalaman Tsoho musamman ma shi Hayatun wanda yake feeling guilty sosai,duk suka amsa da "Ameen amin Baba muna godia sosai."
Ashe Mal.Rilwan ya yankawa Faruq kaza daya yasa Anty Ummi ta masa ferfesu dinsa,sai kuma tuwon masara da miyan kubewa danye wanda yasha man rago sosai,aka kawo musu,ai kuwa Faruq yayi farin ciki sosai da irin wannan karramawar da aka musu,kuma daga shi har Hayat sun sake jiki sun kwashi girki,yau itace karon farko da Hayat yaci abincin gidansu Tsoho,don koya shigo gidan aka masa tayi baci yake ba amma ayau yaci.
Bayan sun kare Faruq yacewa Tsoho zasu wuce Hotel inda ya kama musu daki sannan kuma gobe zasu wuce Minna don nan ne garinsu kuma su din 'ya'yan sarkin minna ne.
Daga Tsoho har Mal.Rilwan saida wuta ya dauke musu na wani dan wucin gadi,mamaki ne shimfide karara asaman fuskokinsu,Tsoho yace"'ya'yan sarkin minna?ashe da manyan mutane muke tare da shine bamu sani ba?sannuku Faruq ai mahaifinku sanannan mutum ne,ina da labarinsa,mutumin talakawa,mai taimako da kuma daukar kowa nasa ne,kai Hayatu ni bansan dalilin daya saka ka baro gida ba,amma kamar yadda na fada afarko bana son tonon silili,ku koyi boye sirrin gida,madallah Allah yayi muku albarqa,ina son na roqi wata 'yar alfarma idan har zan samu.... "
"Baba fadi buqatarka kawai don kafi karfin nemar alfarma awajenmu... "acewar Faruq.
Saida Tsoho ya fesar da wata iska daga bakinsa kafin yace"Idan babu wata matsala ko ince takura,idan komai ya daidaita zanso na baiwa Hayatudden auren 'yar wajena wato *'MARYAM SANI FALALU'* 'yar autata.... "
Dif! Wuta ya daukewa Hayat,sai bin tsohon yake da kallon mamaki don bai taba tunanin jin hakan daga gareshi ba,Faruq kuwa ba karamin dadi zancen ta masa ba,haka ma Rilwan,cike da farin ciki Faruq yace"Allah sarki Baba wannan babbar kyauta haka?baka duba cewa Hayatu ba mutumin kwarai bane ka dauki nutsastsiyar yarinya zaka bashi,toh mun karbi wannan tsadaddiyar kyautar,Allah ya saka da alheri. "
Tsoho yace"Ai d'a na kowa ne,idan ka guji dan wani ko kayi tir! da halayyarsa ai bakasan ya rayuwar naka dan zai kasance nan gaba ba,kuma ni na yaba da hankalin 'Hayatu ne shiyasa naji shaawar bashi 'yata Maryam,ga kuma addinin daya rike,nidai shawarata agareshi ko kuma nace addu'ata agareshi shine Allah yasa yabar shaye-shaye da kuma bin son xuciya... "
"Nagode sosai Tsoho da wannan kyauta,insha Allah idan na koma gida bada jimawa ba Zan turo magabatana ayi maganar aure." haka sukaji Hayat ya fada wanda hakan kuwa ba karamin baiwa Faruq mamaki yayi ba.
"Masha Allah" shine abinda Tsoho ya fada,daga haka Mal.Rilwan ya rufe taron da addu'a,Hayat ya damkawa Mal.Rilwan makullin gida tare dace masa kayan ciki arabawa almajirai.Aka daukowa Faruq jakarsa,Ummi Aysha ce kawai ta fito sukayi sallama,sai kuma 'ya'yanta amma ita uwar gayyar wato Maryam tuni har tayi bacci abinta.Har can Titi su Tsoho suka rako su Faruq.
Bayan tafiyarsu Faruq ya dubi Hayat yace"Kai nifa bazan iya tafiya da mahaukaci ba don haka ka nuna mana shagon aski muje kayi donna tabbata basu tashi ba... "
Hayat ya shaka wannan cin fuskar da Hayat ya masa amma ai baya data cewa tunda duk shine silar komai.Suka dunguma zuwa wani shagon aski aka kwashe sumar kansa,aka bar masa low cut,kana aka masa gyaran kasumba,ai kuwa ya fito shar! dashi,daga nan wani boutique suka shiga,Faruq ya zabo masa kaya kala daya wanda zai saka gobe.Daga haka suka nufi hotel tare da directives din Hayat don yasan hotel din sosai.
Saida Faruq ya nuna musu evidence of payment da kuma room number din da suka bashi sannan wani ya jagorancesu zuwa dakin.Wanka Faruq ya soma yi kafin ya latso Hajiyarsa wacce ya tarar da missed calls dinta da yawa dana spanzy.Bayan sun gaisa yayi mata bayanin komai,tayi murna ba kadan ba har tace abata Hayat din suyi magana,shi kuwa Hayat kunyarta yakeji sosai shiyasa yaki karba.
Bayan sun gama waya ya kira Spanzy ya sanar dashi komai tare da yi masa godia,daga haka kuma ya kashe wayar,yaso kiran Habib Albinsa amma kuma bayason yayi waya da ita agaban Hayat.Basuyi ordering komai ba don akoshe suke,its exactly 15mins to 12am.Faruq ya nemi lafiyar gado,nan da nan kuwa bacci yayi awon gaba dashi.
Shi kuwa Hayat yadda yaga rana haka kuma yaga dare,kwana yayi yana ibada da kuma nemar gafarar ubangiji da kuma yiwa mahaifiyarsa addu'ar samun rahamar ubangiji.
***
Washeqari misalin karfe biyar da rabi ta yamma suka iso garin Minna,Faruq ya kira Hajiyarsa yace ah turo musu direba,ai kuwa babu bata lokaci direba yaje ya daukosu,suna sakkowa acikin mota,cike da mamaki dogarawa suka soma bin Hayat da kallo don basu taba tunanin cewa fitar da Faruq yayi yaje nemo Hayatun ne ba.
Sai zubewa ake akasa ana cewa"Barka da dawowa Yarima karami,muna farin ciki da dawowarka..... "
Bebi ta tankasu ba ya nufi Haj.Babba wacce take can tsaye sai washe haqora take tana jiran ya karaso inda take,ta jagoranceshi xuwa turakar mai martaba........
_*ĸaѕн! ѕorry gυyѕ alĸalaмιn rυвυтυna ne ya ĸare don нaĸa ѕaιna ѕιye wanι*_
_*тoн ya ĸυĸe ganιn нadυwar нayaт da мaι мarтaвa zaι ĸaѕance?*_
_*нayaт ya dawo wнaт neхт now?*_
_*#тeaмнayaт# ĸυ ғιтo ayι ѕнarнι*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα°•*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ __________________________________ 💥
_*°•wαnnαn pαgє dín mαllαkínkí nє mαrчαm chuввч hαчαt,kαmαr чαddα kíkє ѕσn hαчαt αzαhírí,tσh kí ѕαní ѕhímα чαcє nα gαчα míkí cєwα чαnα mutuwαr ѕσnkí kumα zαí kσkαrtα чα αurєkí tundα αn mαѕα kwαcєn nαjmíч😉•°*_
_*°•mαmαn αmírα tαwα ínα míkα gαíѕuwαr вαn gírmα αgαrєkí,nαgσdє ѕσѕαí dα qαunαrkí dα kumα kulαwαrkí αkαínα,hαfnαn ítαmα tαnα míkí ѕαn ѕσ fíѕαвílíllαhí💕•°*
*Թɑցҽ 1⃣9⃣*
""""Haj.Babba ta kasa haquri yama karaso gareta,don haka da dan gudu-gudunta ta soma kokarin isa zuwa gareshi,ganin ta nufoshi da gudunta,yasa shima ya kara sauri ya isa gareta tare da rungumeta tsam! tamkar wata babynsa.Hawaye na gangarowa mata saman kunci tace cikin sanyin murya"Hayatudden Bahago kai ne haka?ashe dama zamu sake sanyaka ah ido kafin mu kwanta hannun dama?Hayatu why?meyasa ka gujemu my son?"
Rushewa yayi da wani uban kuka wanda har hakan ya saka jijiyon kansa mimmiƙewa,yace"Mother pls forgive me wallahi bin son zuciya beyi ba arayuwa,gashi na kashe mahaifiyata da bakin cikina,Abbana kuma yana kwance ba lafiya,na haddasa masa damuwa wanda hakan ya haifar masa da ciwon shanyewar barin jiki,sannan ace ni Hayat zan gama da duniya lafiya bayan na sab'awa mutanen da sukayi sanadiyyar zuwana duniya?na kuntata musu sannan ace naga haske acikin lamuran rayuwata?sannan kuma ace na samu rahamar ubangiji gobe kiyama?Gaskiya ni ba dan albarqa bane,am a cursed child..... "
Ji kake tasss!Haj.Babba ta daukeshi da wani mahaukacin mari,cikin tsananin bacin rai tace"Hayatu menene kake fada ne haka?anya kanka daya ne kuwa?haba d'ana meh zai saka har kayi irin wannan furucin?ko shin bakayi imani da Allah bane?inason ka dauka cewa duk wani abinda ya faru dakai jarabawa ne daga ubangiji,don haka Allah yasa kaci wannan jarabawar,taho muje ga mai martaba yaga farin cikinsa,na tabbata insha Allahu daga yau ciwonsa ya kare,zaya mike akan kafafuwansa sannan kuma bakinsa zai bude insha Allah... "
Ta kamo hannunsa suka nufi turakar mai martaba,suna dab! da isa sai ganin su Abida sukayi sunsha gabansu(Dake aranar Abida tazo don Haj.Babba ta mata waya cewa ai su Hayat na tafe shine tazo).
Sun fito gani ne koda gaske dinne Hayat ya dawo,Abida tace cikin muryar kuka"Yayah prince karami is diz you?kai such is life,Allah ya kyauta... " ta juya tayi ciki da gudu,ita kuwa Hidaya cewa tayi"Barka da dawowa Yayah prince... " itama tayi gaba,jikinsa duk ya mutu da kalaman Abida,ya dago kansa ya sauke kallonsa kan Najmiy wacce take tsaye tana zubda ruwan hawaye,jira yake tace masa wani abin amma ga dukkan alamu ya nuna cewa bata da niyyar magana.
Ahankali yace"Najmiy kiyi magana pls,ko 'yar zagice kimin don naji dadi araina... " da sauri ta kalli Faruq wanda yake tsaye ya cika yayi fam dashi,alamu yayi mata da ido,ai tuni tayi cikin gida tare da fashewa da kuka.
"Ni muje don Allah tunda har yanxu baka hankalta ba... " Haj.Babba ta fadi hakan tare da sake masa hannu tayi ciki abunta.Cike da kasala ya soma takawa,da sauri Faruq yasha gabansa yace"Mal.dakata bazaka shiga ganin mahaifina haka kai tsaye ba,ka bari na nemo maka izininsa tukunna... " kan yayi magana tuni Faruq ya juya ya shige turakar mai martaba ya barshi nan tsaye,shi kuwa kallon mamaki ya bishi dashi,wai shi da mahaifinsa ayau aka hana masa ganinsa kai tsaye wai har sai anje an nemo masa izini,lallai son xuciya bata kareshi da komai ba illa jefashi cikin bala'i da kuma kuncin rayuwa.
Cak! ya tsaya wuri guda tare da harde hannayensa abaya,shike nema asulhunta tsakaninshi da mahaifinsa don haka bai kamata ya haifar da wata rigima ba,shiyasa ya kwantar da kai.
______________****_______________
Haj.Babba na shiga dakin mai martaba,cak! ta tsaya abakin kofa ayayin data shiga wulla masa wani irin tattausan murmushi daga inda take tsaye,shi kuwa mai martaba dake kishingide asaman gado ya bita da kallon rashin fahimta,can ta soma takawa xuwa inda yake tana fadin"Ranka shi dade Ina tafe maka da wani babban albishiri... "
Ta dan dakata tare da tsura masa ido tana mai son tantance irin yanayin daya shiga,gyad'a mata kai kawai yayi alamun yana jinta,da sauri ta waiga don azatonta Hayat ne ke biye da ita,sai kuma taga sab'anin hakan,Faruq ne ta gani ya sawo kai cikin dakin shi kadai,ahankali ta furta"Kai ina Hayatun yake ne?"
"Hajiyata kibar komai ahannuna,naki kawai shine kallo... " ya bata amsa cike da ladabi.
Yana gama fadar hakan ya nufi Abbansa,shi kuwa mai martaba wani irin farin ciki ne ya ziyarcesa alokaci guda na ganin Faruq,sai yayi tunanin kila albishirin da Gimbiya Hadizarsa ke shirin fada masa kenan,wato dawowar shi Faruq din.
Faruq na isa gareshi yayi saurin karya gwiwowinsa zuwa kasa,da sauri ya kamo hannun mai martaba mai lafiyar,babu bata lokaci hawaye ya soma sakko masa,Cikin raunin murya ya soma magana"Abbana Allah yayi na dawo lafiya,kuma nayi nasarar taho maka da maganin lalurarka,yanxu kai nake jira kawai kaban izini sannan naje na shigo maka dashi"
Dakatawa yayi yana kallon mahaifin nasa wanda ya kura masa idanuwa cike da so da kuma qaunar dan nasa,nisawa yayi yace"Abbana naje na shigo maka dashi... "
Gyad'a kai mai martaba ya shiga yi babu gaggautawa wanda hakan ke nuni da cewa lallai yana maraba da koma meye ne dari bisa dari.
"Thank you Abbana,u the best.. " Faruq ya fada tare dakai masa wani kyakkyawan sumba asaman hannun,kana ya mayar da hannun ya ajje ahankali akan filon dake gefen mai martaba,da sauri ya mike ya fice ayayin da Abbansa ya bishi da kallon qauna,ita kuwa Haj.Babba wani sassanyar ajiyar xuciya ta sauke kana ta sami wani sofa ta zauna,sosai take yabawa da halin kirki irinna danta Faruq,babu abinda ya baro na daga cikin halayyar mahaifinsa,he's just like a photocopy of his Abba.
** "Hey!you my dear naughty brother.. " Faruq ya fada ah sa'ilin daya sauke kallonsa kan Hayat,shi kuwa Hayat bema san yanayi ba don gabaki daya hankalinsa ya tafi can duniyar tunanin mutane uku ne,na daya gamuwarsa da Abbansa,abu na biyu kuma rasuwar mahaifiyarsa wanda ke dukansa sosai aynxu,abu na k'arshe kuma shine 'Najmiy Gaddafi',he still loves her,babu abinda ya ragu daga cikin irin son da yake mata,hasalima ji yake kamar wutar soyayyarta ta sake ruruwa ne acikin xuciyarsa na ganin daya mata ayanxu,kai Najmiy she's juz older than her age,yarinya 'yar 17 amma kamar 'yar 20,dama yawancin labarawan nan akwai girman jiki,gashi kuma education dinta is moving very very fast kuma kokarinta ne ya haifar da hakan,she's in her year two now ah midwifery,ita da Hidayah.
"Wai ko bakaji abinda na fada bane?" Faruq ya sake fada cikin fusata.Sai asannan ne Hayat ya dawo cikin hankalinsa,yace"Yayah prince wai magana kake ne?"
Kallon rainin wayau Faruq ya wurgeshi dashi kana yace"Eh! cewa nayi ka shigo Abbana ya baka izini.. " yana gama fadar hakan ya juya ya shige ciki,shi kuwa Hayat sosai kalaman Faruq din ya daki xuciyarsa da kuma yadda yake nuna masa isa da gadara sai kace shima ba mahaifinsa bane,don kawai ya aikata ba dede ba shine Faruq ke masa irin wannan cin fuskar?
Ahankali yaja jikinsa ya soma takawa ciki,xuciyar nan tasa kamar zata faso waje don tsananin tsoro da kuma fargaba.
** Faruq na shiga dakin ya sami waje ya zauna,Haj.Babba kuwa da Mai martaba wanda baisan inda aka dosa ba suka xubawa kofar shigowa ido,sai da Hayat ya kwashi kusan mintuna biyar kafin yayi shahada ya doka sallama ya shigo,idanuwan mai martaba ƙyam akansa.
Acikin seconds biyar kawai,Abba mai martaba ya shiga vibrating sabida wani gagarumin shock daya kai masa attack alokaci guda na ganin Hayat,bai taba mafarkin sake ganin Hayat ba arayuwarsa,atunaninsa ma Hayat din baya ma araye ne.
Wani abin mamaki da kuma ikon Allah shine,bakinsa daya rufe,wato maganarsa da tayi ceasing ada sai gashi ayau Allah ya bude masa shi,cewa yayi"Hayatu dana kai ne?"
Da sauri yace"Abba mai martaba wallahi Hayatunka ne" ya fada tare da karasawa inda yake da sauri.
Haj.Babba kuwa alokaci daya suka mike ita da Faruq har suna rige-rigen cewa"Alhamdulillah Allah mun gode maka bakin Abba mai martaba ya budu" suka fada cike da farin ciki,amma sai dai basu matsa kusa dashi ba,so suke ya gama ganawa da Hayat tukun.
Hayat ya zube asaman kafafun Mai martaba,axuciye Faruq yace"Kai wai so kake ne ka karashe mana shi?ko kuwa bakasan cewa akan kafafuwansa da basu da lafiya bane ka zub'e?"maza ka dagashi don da'ace da gaske kake kana sonsa toh kuwa da baka bar gida ba...... " wani wawan kallo haj.Babba ta wurgeshi dashi ta wutsiyar ido wanda hakan ne ya sashi saurin yin shiru.
"Am sorry Yayah prince mantuwa ce nayi... "Hayat ya fada cikin sanyin murya kana ya daga daga jikin mai martaba,kasa hada idanuwa dashi yayi don sosai yake jin kunyarsa,cikin kuka ya soma magana"Abbana haka ka koma wai duk akaina?wallahi ni har kunyar hada idanuwa dakai nake don ko kadan ban kyauta maka ba,nabi son xuciyata da kuma zugar abokai wanda gashi ya kaini ya baro acikin kogin danasani mara amfani,Abbana ko ahakan ma idan ka barni yayi don naga darussa da yawa na rashin bin maganar iyaye,Nayi sanadin barin mahaifiyata duniya,gashi kai kuma na janyo maka wani mugun ciwo,Abbana don Allah karka juya min baya,don Allah ka gafarta min,Hajiyata kema ki yafemin kuma Allah yakai rahama da haske kabarinki.... "
Kuka yaci karfinsa,hawaye yadan zubowa Mai martaba saman kunci,hannunsa mai lafiyar ya daga,hannun na rawa amma saida ya kokarta yakaishi saman kan Hayat ya dire,ahankali ya soma magana"Allah yayi maka albarka Hayatu,ko bakomai nayi farin ciki da dawowarka gida kuma nafi kowa farin ciki daka furta da bakinka cewa kaga darussa da yawa arayuwarka daka tsallake maganar iyaye,alhamdulillah! hakan yayi kyau sosai kuma naji dadin hakan,kuma sannan wacce ka bar gida dominta kamar yadda na fada tun farko,'A' dina 'A' ne,na aurar da Najmiy ga Yarima Umar Faruq,don haka sai ka sake komawa inda ka fito idan kaga bazaka iya rungumar kaddararka ba............ "
_*тoғa мy jaмa'areѕ wнo aмong yoυ can deѕcrιвe ιrιn yanayιn da нayaт ya ѕнιga yanхυ?*_
_*нммм! aввa мaι мarтaвa aм ѕorry тo ѕay ka ĸυnno rιĸιcι aн ғaмιly dιnĸa,нow ι wιѕн daĸa нana ĸowa najмιy,daĸa вaιwa wanι can awaje ne aυrenтa da ĸoмaι вaι ғarυ вa,мυje хυwa #тeaмнaғnanFans#*_
_*ĸυyι мana нaqυrι da raѕнιn jιnмυ ĸwana вιyυ wlнy вaмυ dan jιndadι gaвaĸι dayanмυ мυ тrιpleтѕ,nι,мy ѕιѕ nerja'arт da ĸυмa ѕιѕ janaғ*_
_*σчα lєt'ѕ kíndlч nσvє tσ thє nєхt lєvєl👇*_
_*mσm híввαh💕*_ ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*•°(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°•ιnιqυιтy,eмpaтнy,нυмιlιaтιon & roмanтιc love💑°•*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATPADD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα°•*
*°•ιитєℓℓιgєит ωяιтєя'ѕ αѕѕσ✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ ____________________________________ 💥
_*°•ѕσ much lσvє чσu mч dєαr mσmmα hαj.hαdízαtσuh muhαmmαd kαkαkí,mαmmα u gαvє lífє tσ mє,turnєd thє вαвч íntσ α lαdч,mαmmα αll u hαd tσ σffєr wαѕ thє prσmíѕє σf α lífєtímє σf lσvє,thєrє íѕ nσ σthєr lσvє thαn α mσthєr'ѕ lσvє fσr hєr chíld👉---cєlín díσn•°*_
*Թɑցҽ 2⃣0⃣*
_______jin zancen Mai martaba yayi tamkar saukar aradu,Najmiy dinsa tayi aure sannan wai kuma dan'uwansa Faruq ta aura?yaushe ma akayi auren?acikin shekaru biyun da baya gida?yanxu kuma duk guduwar da yayi agida da nufin idan ya dawo yasan za'a bashi ita don kada ya sake guduwa,yanxu plan dinsa ya tashi abanza kenan?God!!!! shikenan dan'uwansa Faruq yayi masa kwacen *'Adorable'* dinsa kamar yadda yake kiranta kenan.
Ji yayi kamar ya fasa wani uban ihun da zai iya tada zaune tsaye,ihun da zai iya hargitsa kwakwalwar duk wani halittar daya ji wannan ihun.Baya jin rayuwarsa zata iya cigaba da tafiya normal ba tare da *'Adorable Najmiy'* dinsa ba,sai dai kuma bazai iya raba auranta da dan'uwansa ba amma kuma alqawari ya dauka sai ya sanya Faruq tsiyayar da hawaye akan *'SO'*,sai ya gwada masa yadda akeji idan aka rasa *'Masoyi'*,wannan alqawari ne saiya dauki *'FANSA'* akan *'UMAR FARUQ'*,infact! har ita kanta *'NAJMIY'* din sai ta gane kuranta.
"Yayah prince ka cuceni,ashe son Najmiy kake shiyasa kasan yadda kayi kabi duk wata hanya ka rabani da ita?toh Ina son ka sani cewa *'KA TAFKA BABBAN KUSKURE'* don ba'a taba *'HAYATUDDEN'* kuma azauna lafiya,wallahi wallahi koda zanyi yawo tsirara ne nayi alqawarin maida rayuwarku abar tausayi daga kai har Najmiy din,sai na firgita rayuwarku fiye da zato da kuma tsammaninku.... " duk acikin xuci yake wannan maganganun.
Mai martaba ya katse masa zancen xucin da yake tayi ta hanyar fadin "Hayatuna yana ji kayi shiru?kodai shawarace kake da xuciyarka kan matakin da zaka dauka kuma akaro na biyu?"
Murmushin ƙarfin hali ya saki wanda zamu iya fassarashi da murmushin daya fi wani kukan ciwo,kana yace"A'ah Abba Mai martaba ni tuni ma na dade da cire Najmiy acikin raina kawai lokacin dawowata gida ne beyi ba sai yanzu,dama ina da niyyar dawowa ayau sai kuma naga Yayah prince yazo nemana jiya,wallahi harga Allah nina haqura da Najmiy,ubangiji Allah ya sanyawa auransu albarqa,Allah kuma ya basu zaman lafiya,ni ayanxu fatana shine Allah yasa Hajiyata ta yafeni,kuma Allah ya gafarta min bakanta muku dana yi,kai kuma Abbana kayi haquri ka yafeni sannan kuma Allah ya baka lafiya.... "
"Allah ya yafemu duka,naji dadi daka hankalta Hayatu,na kuma ji dadi da ayanxu kasan yadda ake daukar *'DANGANA DA KUMA 'HAQURI'*,koda yake ko baka haqura ba dama babu yadda zakayi tunda dai an riga da an daura auran,kai kuma Umaru Allah yayi maka albarqa,hakika ka cika dan'uwa na gari wanda ya fita yaje ya nemo dan'uwansa don kawai ya dawo kan hanya madaidaiciya,ubangiji Allah yasa ka wanye da duniya lafiya Umaru.... "
"Amin amin Abbana,bara na latso likitanka na kora masa good news... " acewar Faruq kenan,murmusawa akayi gabaki daya har Hayatun.Haj.Babba kuma ta mike tana cewa Hayat yazo yaje yaci abinci,yace mata taje gashi nan tafe,so yake Faruq ya kare wayarsa sannan yayi masa magana.
Bayan ya kare,ya kalleshi yace"Congratulations Yayah prince,ashe an zama babban mutum ban sani ba?anyway ina tayaku murna,Allah ya bada zaman lafiya sannan kuma Allah ya kawo kazantar daki..... "
Dam!! Faruq yaji gabansa ya yanke ya fadi amma kuma sai ya waske yace "Amin tanks bro,muna ma cikin watanmu na shidda kenan da auran... "
Kan Hayat yayi magana,Faruq yayi saurin kallon mai Martaba yace"Abbana likitanka yace yana nan tafe ya dubaka bayan sallar magrib.... "
"Toh " shine kawai abinda ya iya furtawa.Hayat kuwa bai sake cewa komai ba ya mike ya fice,Faruq ma ya mike yabi bayanshi,suna fita suka ci karo dasu Abida sunzo ganin Abba mai martaba don tuni Haj.Babba ta karas musu da daddadar labarin.
"Habib Albi kibi ahankali karki fadi.... " Faruq ya fadiwa Najmiy haka cike da shaukin sonta,sosai abin ya daki xuciyar Hayat,bakin ciki ya turnukeshi,ji yayi kamar ya shako Faruq din ya aika dashi har lahira.
_*"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajurni fi musibati wa'akhlifni khairan minha "*_,wannan itace addu'ar daya yita nanatawa acikin xuciyarsa har ya isa b'angaren Haj.Babba.
*🐾AGURGUJE PLEASE🐾*
Kan kuce meye wannan tuni gida ya soma rudewa da jama'a 'yan xuwa yin barkar dawowar Hayat dake acikin kankanin lokaci har Faruq ya sanya an baza agidajen radio cewa Yarima karami ya dawo gida,abinka da dan babban mutum kowa so yake ace ai yazo shiyasa akayita tururun xuwa,shi kuwa uban gayyar makalewa yayi adakinsa yaki fitowa don sosai yake jin kunyar hada idanuwa da mutane,tsanar Faruq ya dadu aransa don acewarsa meyasa Faruq din zai bazawa duniya cewa ya dawo?aganinsa wani salon cin fuskar ne ya sake yi masa daga dawowarsa,dangin mahaifiyarsa suma sunzo don su aka ma soma sanarwa kafin kowa,mai martaba yace"Ga dan yar'uwarku nan dan'uwansa Faruq ya fita yaje ya nemosa don haka yau saiku shafa min lafiya,ayau zanyi bacci mai dadi wanda na jima ban sake yin kwatankwacinsa ba..... " suma din dakyar Hayat ya bari suka ganshi.
Kowa saida yayi mamakin budewar bakin mai martaba wai kuma akan Hayat,nan suka sake tabbatar da tsananin qaunar da yake yiwa Hayatun tunda akansa ya kwanta wannan ciwon sannan kuma akansa bakin nashi ya budu har ya soma magana.
___________________ Likitocinsa sunzo sun dubashi kuma sunce da akwai improvement sosai,dama Hayat ne makasudin rashin lafiyar kuma tunda ya dawo insha Allahu zaya mike.
Awannan ranar Hayat yasha fira da mahaifinsa kamar babu abinda ya faru,fira hadda ƙyaƙyatar dariya,hannayensu sarke cikin na juna har bacci ya kwashesu,Hayat na zaune saman wata kujera wanda ke kusa da gado ayayin da mai martaba kuma ke kwance saman gadon,kafin baccin ya kwashesu sai da suka sake nemar gafarar juna,shi kuwa Faruq nacan kan wata doguwar kujera,shima wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi.
Can mai martaba ya farka,yana jin wani sabon al'amari ajikinsa,ya kalli Hayat da Faruq wa'enda ke kwasar baccinsu hankali kwance,murmushi yayi ya furta ahankali"Ubangiji Allah ya dada hada min kawunanku,Allah yayi muku albarka,naso ace mun rayu da juna na wani dan tsawan lokaci amma ga dukkan alamu lokacin da aka dibar min ya kare..... "
Yadan ja numfashi,can ya cigaba cikin muryar da bata fita sosai yace"Hayatu komin rintsi koman wuya karka taba juyawa dan'uwanka Faruq baya ko kuma ka zalunceshi don yayi maka gata arayuwa,sannan kuma ku rike min Najmiy amana...... "
Allahu Akbar!!! his royal highness *'MAI MARTABA MUHAMMAD KHAMIS BAHAGO'*,mutumin talakawa ya cika yana mai dauke da murmushi asaman fuskarsa,ya koma ga mahaliccinsa cikin haske da kuma annuri ah fuska (Allah yasa muyi irin wannan cikawar,amin).
Sai wuraren biyar saura na asubahi sannan Hayat ya farka,yaji hannun mai martaba dake sarke cikin nashi yayi sanyi qalau,tashiwa yayi ya kunna wutar lanta,kana ya dawo wajensa,fuskarsa dauke da murmushi kamar ka kirashi ya amsa.
"Abbana kodai jikin ne naji hannunka yayi sanyi da yawa.. " Hayat ya fada tare da dan taboshi,shiru bai amsashi ba,Hayat ya soma tsorata da wannan al'amarin,don haka ya shiga girgizashi continuously yana fadin "Abbana meya faru?don Allah ka tashi mana Hayatunka ne fa"
Faruq ya taso agigice sakamakon muryar Hayat daya tasar dashi.
"Hayat meke faruwa ne?" ya nufo wurinsu.
"Yayah prince nima wlhy ban sani ba,inata kiran sunansa amma yaki tankani,don Allah kazo ka duba mana shi karya mutum ya barmu.... " ya fada already in tears..........
_*wayyo Allaн мaι мarтaвa ya rιgaмυ gιdan gaѕĸιa,wa'adι ya cιĸa,wanι aвιn вιrgewa da ĸυмa ғarιn cιĸι ѕнιne an ѕaмυ ya yaғewa нayaт ѕannan ĸυмa aнannυn нayaтυn ya raѕυ,нaĸan yayι*_
_*тoғa!wнaт ιѕ нayaт υpтo?мeн yaĸe ѕнιrιn aιĸaтawa ĸan ғarυq da ĸυмa najмιy?ĸυ вιyo*_
_*αlвíѕhírínku?fαtαlwαr míjínα nαnαn tαfє muku gσвє ínѕhα Allαh*_
*TAKU*
*mσm híввαh💕* ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°•ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑•°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ __________________________________ 💥
*NOT EDITED*
*Թɑցҽ 21*
Faruq shima karan kansa bai gane komai agame da mai martaba ba,don haka arude ya kira likitansa,dakyar aka samu ya daga wayar sabida baccin dake idonsa,jin abinda Faruq ke gaya masa ya saka baccin wartsekewa daga idanuwansa,at once ya tashi,ya shirya agurguje ya kamo hanyar gidan mai martaba.
Babu b'ata lokaci Faruq ya latso Haj.Babba ya kora mata bayani,hankali tashe ta taso su Najmiy suka nufi turakar mai martaba.Tunda Haj.Babba ta sauke idanuwanta kan mai martaba ta gane cewa inaaa! rai yayi halinsa,kota fadawa su Faruq ba yadda zasuyi ba don haka zata barsu suji hakan daga bakin likita.Fita waje tayi ta sami wani gu ta zauna,ta hau cizgar kuka ahankali yana furta"O'ooh mai martaba ashe korarmu kake tayi adaren jiya?kana ta cewa mu tafi mu kwanta ashe dai bakaso ka cika ne agabanmu?Allah sarki my dearest husband Allah yayi maka aikin gafara,Allah yasa kaje asa'a don wallahi kayi mugun kyautata mu'amalarka da mutane,don haka bani da fargabar komai akanka,Allah ya jikanka Muhammadu... " kuka yaci karfinta,su dogarawa da ƙuyangi suka cika kofar turakarsa cike da jimami,kowa jira yake yaji sakamakon likita wanda xuwansa kenan.
Can suka jiyo ihun Faruq yana fadin"Noooooo!!!! Not again!!!! Hayat ka sake kashe min wani nawa,kayi sanadin barin someone so dear to me,my hero,my everything,tsakanina dakai babu yafiya,kotun Allah ce kawai zata rabani dakai...... " sam baya ma cikin hayyacinsa yake fadin wa'ennan maganganun.Haj.Babba tayi wani irin zabura ta shige ciki tana mai rushewa da wani sabon kukan,ƙuyangi kuka,dogarawa kuka,kowa da kowa kuka yake,babu zancen jarumtaka acikin wannan al'amarin mai tab'a xuciya wato mutuwar mutumin talakawa.
Dakyar Haj.Babba ta iya b'anbare hannun Faruq daga makurar daya yiwa Hayat,cikin muryar kuka tace"Haba Faruq menene kakeyi haka kamar wani jahili?ko kuwa ka manta cewa rayukanmu duka ahannun Allah yake?ka sani fa wani baya iya kashe wani sai dai ace ta sanadin mutum wannan din yabar duniya,kuma ni inason ku dauka cewa wa'adin mai martaba ne kawai ya cika,kuyi masa addu'ar samun rahamar ubangiji,maza ku hanzarta ah shiryashi don mamaci baya son jinkiri....... "
Kuka yaci karfinta ta juya ta fice da gudu,acan waje taga kowa sai kuka yake,wani murmushin karfin hali ne ya sub'uce mata tace"Allahu Akbar!! Muhammdu mutumin mutane,sarkin sarakuna,kabar mutanenka da kewarka da kuma kewar kirkinka agaresu,ubangiji Allah yayi maka aikin gafara,don Allah kubar yi masa kuka babu kyau,gatar da yake nema agareku itace addu'a...... "
Tayi bangarenta tana mai kokarin danne kukanta cuz she has to be strong for her children,Najmiy har suma sai datayi,yo! ai dole tayi,mutumin daya taimaketa ayau bashi kuma ai dole ta kusan haukacewa ma.
Kan kuce meye wannan har mutane sun soma taruwa,Faruq ya kira abokanan aikinsa yace abada sanarwa agidan radio,zuwa tara na safiya za'ai sallacesa kana asadashi da gidansa na gaskia.Ya kira Mal.Rilwan ya sanar dashi zancen rasuwar dake sunyi exchanging numbers kafin ya taho.Jama'a na nesa dana kusa,manya da kuma kananan mutane duk sai zuwa ake tayi,kafin 9am har gida ya cike babu masaka tsinke.'Yan kungiyar *'intelligent writers'* suma ba'a barsu abaya ba,su *'My sahiba'*, *'my najatee'*,*'my leemah'*,*'My blood Sainah'*,*'Mom afra'*,*Aufana Ukhti'*,*'Mummy Zill'*,*'My anty hauwa'*,kai kuna da yawa,duk sun samu kawo ta'aziyyar Mai martaba M.K bahago.
Su my qanwa Ramlerh suma ba'a barsu abaya ba,my Kakus Hafsat duk da tana fama ne da kanta don tsufa amma don shegen karfin hali irin nata sai datazo😀,su chubby,su Yaseera,mugirat,lashminzy,Ameenah Abdul,Hafsat kanty,maman Amira,Juwairiyya Adam,kai kuna da yawa kuma,duk sunzo,ni kaina Hafnan sai dana je dake nima 'yar wajen aikinsu Prince Faruq Bahago ne. 😉,mune 'yan video coverage.
Hayat sai fadi yake yana dada nanatawa"Allah sarki ashe da rabon zan gana da Abbana kafin ya kwanta hannun dama,ashe da rabon zai yafemin kurakuraina sannan da sanya min albarqarsa kafin ya tafi..... " kuka sosai Hayat keyi mai cike da nadama har baya jin lallashi.
Mai martaba m.k bahago yayi jama'a sosai ba kadan ba,kowa sai fadin abubuwan alkhairi yake akansa,Mal.Rilwan ya samu xuwa amma aranar sadakar uku,ya mika sakon gaisuwar Tsoho don shi bazai iya juran dogon tafiya ba sabida tsufa.Haqiqa su Faruq sunji dadin zuwansa sosai,washeqari ya koma bayan Faruq ya dada jaddada masa cewa suna nan xuwa akan batun Hayat da maryam.
_______________________________
Bayan an kare zaman makoki akayi rabon gado kuma itama Najmiy ba'a banbantata da sauran ba,an bata kasonta daidai dana sauran matan don ya taba barin wasiyya kan cewa idan yau ya fadi ya mutu,toh itama Najmiy tana da gadonsa don tamkar 'yar cikinsa ya dauketa,kuma abata daidai da irin kason da za'a baiwa matan.kuma sun aikata hakan.
Bayan wata daya aka nada Faruq as the next emir of Niger state kasancewarsa Yarima mai jiran gado,ayanxu Prince Faruq ya koma *'MAI MARTABA UMAR FARUQ BAHAGO'*,ya watsar da aikin jaridarsa,ranar da aka nadashi sarkin kuwa sai daya zubda hawaye na tunawa da mahaifinsa.ba'ayi wani bikin shagali ba don Faruq ya hana,yace har yanxu ana cikin zaman makoki ne.Aka nada *'JABIR AWWAL'* amatsayin wazirinsa,Jabir ya baiwa shekaru arba'in baya,ayayin da Mai martaba Umar yake da shekaru 30 kacal aduniya,a very very young king,haka kowa keta cewa,wasu kuma suce"Kodayake ba shekarun za'a duba ba,Allah dai yasa yayi koyi da halayyar kirkin mahaifinsa.... "
Haj.Babba ta sake hada kan 'ya'yanta ta musu nasiha mai ratsa xukatu musamman Faruq da Hayat,tace musu su manta da duk wani abinda ya faru abaya,ayafi juna and let dem focus on the present,suka nuna mata cewa ai komai ya wuce har Faruq ya dauki alqawarin samawa Hayat aikin yi tunda result dinsa nada k'yau,shi kuwa Hayat har yanxu yana nan kan bakansa kamar yadda ya alqawaranta na daukar fansa kan Umar Faruq.
Cikin kankanin lokaci Faruq ya samo masa aiki based on the field he studied *'Chemical engineering'*,ya samo masa aikin awani company ta engineers, *'Biomedical engineering'* shine bangaren da aka baiwa Hayat,aikinsu shine suyi creating equipments,computer systems da dai sauran devices na healthcare.
Saida aka samu watanni uku da soma aikin Hayat sannan Faruq ya tunkareshi da maganar Maryam,yace"Hayat tunda ka soma aiki,why not muje ayi maganar auranka da Maryam din Tsoho?naga kai baka ma maganarta ko tambayarta sai dai nine naketa kafa maka gwamnati awajen mutanenta,shekaranjiya mukayi waya da Rilwan yake gayamin cewa satinta daya kenan dayin candy,kaga kuwa ya kamata mu yunkuro ko kuwa meka ce?"
"Tabdi! Lallai Yayah ni wallahi harna manta da zancen wata maryam,nifa idan za'a bi ta tawa kawai akyaleni nayi rayuwata ni kadai basai nayi auran ba....... "
Axuciye Faruq yace"Kaga malam karka sake ka maidani mutumin banza ah idanuwan bayin Allahn nan,karka sa suyi tunanin kila mun hada kai ne tare muci mutuncinsu,toh wallahi baka isa ba nadai gaya maka don da bakinka ka daukar musu alqawari,kaga kuwa aure kamar an riga an gamashi ne....... "
** Babu yadda Faruq ya iya illa bada kai bori ya hau tunda yaga yayan nasa ya zage,sai hidimar bikinsa yake gadan gadan don tuni har ankai gaisuwa an saka rana.Ita kanta Maryam bata da iko ne da kanta da kuwa bata bari an bada ita ga Hayat ba,don ta tsaneshi sosai ba kadan ba sabida shaye-shayensa(Allah sarki maryama ai tuni Hayat yayi hannun riga da shaye-shaye).
Anyi shagalin biki lafiya qalau,maryam amarya ta tare da angonta Hayat acikin dayan sabon flat din daya rage wanda dama can na Hayatun ne,flat din akusa dana su Faruq yake.Zama suke kamar ba ma'aurata ba,kai kace ko makiyan juna ne,daga gaisuwa dake shiga tsakaninsu shikenan,idan kuma wani abin yake da buqata zakaji yace "Ke!!! dauko min kaza" ko kuma "Ke! 'yarinya kira min wani ko wance... " ita kuma bata iyawa sai kaga ta maida masa da zagi,shi kuwa mara haqura sai kaga ya taso zai daketa,da gudu zakaga ta shige daki tasa key don kar ya samu damar shigowa.wani abin birgewa dasu shine,duk rashin zaman lafiyar nan tasu babu wanda ya taba sani don dukansu akwai boye sirrin juna,awaje zasu nunawa duniya kamar sunfi kowa zaman lafiya,alhalin abin ba haka yake ba,na ciki na ciki,Koda wasa Maryam bata taba kaiwa wani nata kukanta akan Hayat ba,kuma harwa yau yaki hada shimfida daya da ita na auratayya,itama Maryam din bata wani damu ba,shifa har yanxun matar wani yakeso wato 'Najmiy',ya gama deciding kan irin fansar da zai dauka akansu,lokaci kurum yake jira tayi sannan ya aiwatar da kudiransa akansu.
Har kusan shekara daya babu abinda ya canza daga irin zaman da Hayat da Maryam keyi,abin nasu ma ya ninka nada don har dambe sukeyi kuma ita maryam din tafi cutuwa don dukanta yakeyi sosai amma ba irin wanda zataji rauni ba,dan'iskan kafin ya soma bugunta sai ya rufe ko'ina don karta samu ta tsere sannan kuma ya kara volume din TV har karshe don kar ajiyo ihunta.Kuma harwa yau babu wanda yasan abinda ke gudana azamtakewarsu sai su biyu din.
Maryam da Najmiy kuwa sunyi wani irin mugun sabo ne da juna,duk da cewar Maryam din tadan girmema Najmiy amma still tana bata girmanta amatsayinta na matar wan mijinta,haka ma surukar tasu Haj.Babba har competition suke wajen faranta mata.
Acikin shekarar nan ne kuma Najmiy da Hidaya suka kare karatunsu na unguwanzumanci,ayanzu sun zama cikakakkun *'Midwives'*,suna gamawa suka sami aikin yi ah general hospital minna,dakyar Faruq ya yadda zatayi aiki,shima din saida ta hada masa da kukan shagwabarta.An tsaida lokacin bikin Hidaya nan da watanni biyar masu zuwa.
Ayanxu Najmiy tana da shekaru goma sha takwas aduniya,tayi wani irin ciccikowa kamar ba yar 18 ba,hakan kuma ya sake daga hankalin Hayat akanta,sai dai kuma babu yadda ya iya tunda ta riga ta masa nisa amma fa sai ya dau fansa babu fashi.
Awannan lokacin ne kuma Mai martaba Umar Faruq yaji shaawar hada shimfida da matarsa Gimbiya Najmiyya akaron farko tunda sukayi aure,ada can suna dai matsayin mata da miji ne amma ko kadan baya taba ko 'yar yatsarta ne sabida bayaso ya zarce,don ya daukarwa kansa alqawarin bazai taba kusantar Najmiy ba har sai takai shekaru goma sha takwas,alokacin ta soma sanin kanta.Ita kanta abin na damunta cuz suna yawan yin firar ma'aurata da kawayenta,yadda mata da miji keyi amma taga ita da mijinta ba hakan yake ba,toh tun asannan ne ta soma sha'awar mijinta amma kunya ya hanata tunkarensa ta masa magana,kuma bata taba gayawa kowa wannan sirrin ba,tabarwa cikinta,sannan kuma tana yawan addu'ar Allah ya karkato da hankalin mijinta xuwa gareta.
Bayan ya kammala komai na al'adarsa,sai ya tunkari dakin gimbiyar tasa yana mai jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ziyartarsa..........
_*wαít σσσh!!wαí duk αtunαnínku dα cαn fαruq dα nαjmíч ѕunчí fírѕt níght nє?tσh gαѕhínαn чαnхu kun gαní*_
_*mσm híввαh cє💕* ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιнєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°* https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ __________________________________ 💥
_*°•hαhαhα! ѕσrrч guчѕ í dєcídєd gívє αn updαtє σn híввαtullαh cuz ít'ѕ вєíng α whílє,fαtαlwαrku wαtσ lєσnα lukαѕ tαnα nαn tαfє αnjímα kαdαn kσ kumα gσвє dα ѕαfє ínѕhα Allαh•°*
_*°•wαnnαn ѕhαfín nα mαllαkα muku ѕhí hαlαk mαlαk dσn hαkα kuчí чαddα kukєѕσ dαѕhí👇
_*°•ѕíѕ mugírαt muѕα(mαruвucíчαr 'kíѕhín jαhílcí)•°*_
_*°•ѕíѕ ѕαfíччα Alíчu wαkílí(mαruвucíчαr 'mαѕαukín ѕσn)•°*_ ____________________________________
*Թɑցҽ 22*
Har Najmiy ta gyara filonta zata kwanta,sai taji kawai an turo kofar dakin an shigo,ahankali takai hannu ta kunna dim light din dake gefen gadon,hasken ya taimaka wajen bayyana mata wanda ya shigon,ajiyar xuciya ta saukar kana tace"Ooh Ya hayati ashe kaine?"
Murmushi ya sakar kasa kasa yace"Ada wa kike tunanin zai iya shigowa dakin baccinki acikin wannan daran face mijinki my habib albi?uhm gayamin?" ya fada tare da zaunawa agefen gadon,ya jawota ta fado jikinsa,daga shi har ita wani irin bakon yanayi ne suka tsinci kansu ciki wanda basu taba jinsa ba kuwa.
Ta soma kokarin raba jikinta daga nashi,kara janyota yayi ta shige jikinsa dakyau,ya shiga shinshina gashin kanta yana mai yamutsa fuskarsa aciki,numfashinsa yaji kawai ya soma haurawa sama sama,cikin wata dasasshiyar murya yace"Habib albi ina son kamshin nan sosai.... "
Kukan shagwab'a ta sakar masa ganin abin nasa na kokarin soma wuce gona da iri amma aranta farin cikine fal acikinsa na ganin yau mijinta ya kusanto inda take har yana mata wasa irinta ma'aurata ba kallon qanwarsa kuma ba.Shagwab'ar tata ta taimaka wajen kara masa kaimin abinda yakeyi,romance dinta ya shiga yi sosai babu gaggautawa,itama ta cire kunya da shakku ta shiga maida masa da martani,can ya dakata yana maida numfashi,idanuwansa ƙyam akanta,ita kuma rausayar dakai tayi gefe don bazata juri kallon ƙwayar idanuwansa ba.
Cikin wani salon Jan hankali yace"Najmiiiiiiyya kalli cikin ƙwayar idanuwana.... "
Dakyar ta kalleshi,amma tana yi tana dan rufe idanuwan lokaci xuwa lokaci,sauka yayi daga samanta ta hanyar mirginawa gefenta,ya sanya hannu ya tallafo fuskarta gareshi,fuskokinsu tamkar su manne da juna tsabar kusanci,murmushi yayi kana yace"Najmiy na mace akan sonki,don haka inason ayau dinnan ki bani dama na gwada miki irin kalar son da nake miki,inason ayau ki karbeni amatsayin mijinki ba dan'uwa kuma ba,pls Najmita can I move on?"
Sanya hannu tayi ta rufe fuskarta dashi alamun kunya,kuma alokaci guda taji gabanta ya hau dukan chalugude,hakan da tayi kuwa ba karamin birgeshi yayi ba don arayuwarsa yana mugun son mace mai alkunya.
"Toh shikenan tunda baki yarda ba nina tafi,aduk lokacin da kika yanke shawara da xuciyarki ta kuma amince miki dani toh sai kiyi gaggawar sanar dani..... " yayi yunkurin mikewa don barin dakin,da sauri ta ruƙo hannunsa tace cikin sanyin murya"Na amince Ya hayati.... " cike da tsantsar farin ciki ya rungumota yana fadin"Masha Allah thank you my lovely wife Allah yayi miki albarqa matata... "
Ahankali ya rad'a mata akunne"Akwai wata alfarma da nake nema kuma awurinki,shin zaki iya daurewa ki min ita?"
"Ka wuce gaban ayi maka alfarma awurina,bada umarni kawai Ya Hayatina... " acewarta cikin shagwab'a,sosai yaji dadin kalaman nata wanda hakan yasa kawai yaji sonta ya mugun karun masa acikin xuciya.
Ahankali ya soma magana"Najmiy dama so nake kiyi just 2month awajen aikinki don kici moriyar karatunki,bayan wannan watanni biyun kuma sun cika na sanya araina cewa zansa kiyi resigning don tun ina karamina bani da burin wai ace matata tayi aiki,all I want her to be is to become a full house wife,nata kawai ta dunga kula dani da kuma 'ya'yanmu,Najmiy jiya watannin naki biyu ya cika da soma aikin,so pls can u kindly show some love to ur lovely husband by resigning?"
Jikinta ne yayi sanyi qalau da maganganun nasa,tana matukar son aikinta amma ya zame mata dole ta ajjeshi tunda mijinta ya nuna bayaso,bata ankara ba kawai taji hawaye ya soma kwaranyo mata saman kunci,takai bayan hannu zata sanya ta goge,sai taga ya rigata saukar da harshensa saman kuncin nata,ya shiga lashewa,sai daya gama lashewa tass kana yace"Hakan ba zata samu bako?"
Cikin raunin murya tace"Tunda mijina ya bada umarni kuma yace haka yakeso ai dole nabi,na maka alqawari daga yau na ijje aikina.... "
Beyi wata wata ba ya rungumota tsam jikinsa ya shiga shi mata albarqa mara iyaka,daga bisani sukaje suka dauro alwala sukayi sallah raka'a uku,ya dade yana musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma zuria dayyaba,can ya shafa,ya juyo ya kinkimeta sai gado,saida ya soma ciyar dasu da gasasshiyar namar daya shigo da ita da kuma fresh milk,kana suka bi lafiyar gado,daga nan kuma labarin ya soma sauya zani.
Faruq ya rikice akan Najmiy,dama gashi akullum cikin gyarata Haj.Babba take,don haka ni'ima ya gama ratsata ta ko'ina shiyasa gogan naku ya rikicen,ita kuwa tasha kuka don azaba abinka da sabuwar shiga,Faruq yasha yakushi dasu cizo amma duk abanza don bema san duniyar da yake ba,awannan daran sun rayashi,sun gurzashi don samun albarqar ubangiji da kuma ladarsa duk da cewa Faruq dinne kawai yayi ta fama shi daya.
*** Tun daga wannan ranar kuwa ita da Faruq suka dinke da juna,wani irin mugun shaquwa da qaunar junansu ya dada yin karfi atsakaninsu,kuma adaran farkon nasu ne Allah ya azurta Najmiy da samun shigar ciki,sai da yayi watanni uku kafin su gane sabida batayi wani laulayi ba,wannan cikin kowa yayi murna da samuwarsa musamman Hayat wanda dama can plan dinsa na akan dansu ne,duk da cewa ya danji zafin samun cikin da Najmiy tayi da waninsa amma murnar ya dara bakin cikin.Tattalin cikin ake sosai bana wasa ba,sai tanadi ake tayi na tarar babyn har Haj.Babba,wani abin bakin ciki da tausayi,duk yadda wannan family din suka ci buri sosai akan wannan cikin na Najmiy sai d'an baizo da rai ba,haqiqa abin beyi musu dadi ba amma sai suka rungumi kaddararsu suka kuma lallashi Najmiy wacce har kuka tayi akan hakan,Hayat yafi kowa jin haushin wannan abin sabida plan dinsa ya ruguje.
Cikin hukuncin ubangiji kuma Najmiy bayan watanni biyar ta sake samun wani cikin,wannan karon tayi laulayi sosai akansa tamkar bazata rayu ba.Samuwar wannan cikin Na Najmiy yasa Maryam ta tadawa Hayat da rigima don haqurinta ya soma karewa,ce masa tayi kiri-kiri "Hayat nima inason naga gudan jinina,wallahi kaji tsoron Allah Hayat kana daukar alhakina da yawa,shekaru kusan biyu muna tare amma ko hannuna baka tab'a tabawa ba da sunan jindadi,idan kuwa har anga ka rikenin toh zalina zakaci......"
Kwance belt dinsa yayi,ya soma kokarin saukar da wandonsa kasa yana fadin"Don ubanki kwanta na miki cikin tunda ke 'yar iska ce,so kike na kusanceki,toh maza kwanta shegiya jarababbiya kawai....."
"Tunda agidan mijina nayi iskancin ai da sauki,kuma badai ubana ba.... "
Zaro belt din yayi daga jikin wandon ya matso kusa da ita yana fadin"Sai uban waye?"
Kan ta ankara har ya soma shaud'a mata belt din ajiki,kasa ihu tayi don xuwa yanxu ta riga ta saba da bugun da takesha daga hannunsa,kuma harwa yau taki gayawa kowa don harga Allah tana masifar son mijinta.Kowa na zaton suna zaune lafiya qalau ne musamman ma Faruq,don har zama suke suyi hira agaban jama'a amma na ciki na ciki,kowa na tunanin kila lokacin samun rabon maryam dinne beyi ba,alhalin basu san cewa akwai gagarumar badakala akasa ba.
Cikin Najmiy nada 2months ya bare,wannan karon har kuka saida Hayat yayi aboye,koda yaje gaisheta kasa haquri yayi yace"Don Allah asarar ya isa hakanan,kiyi kokari idan kin dauka next time kar wata matsalar ta sameshi idan ba haka ba xansa dan'uwana ya karo aure don muna da buqatar samun *'YARIMA MAI JIRAN GADO'*..... " fuuuu! ya tashi ya fice,angode babu kowa afalon sai ita,ta dade tana mamakin wannan furucin na Hayat wanda hakan har kuka ya sanyata amma taki gayawa kowa.
Tun asannan kuma Najmiy bata sake daukar wani cikin ba,Hayat ya shiga cikin tashin hankali sabida gabaki daya ta ruguza masa plan din da suka shirya da Rougcoin don Hayat ya sake nemoshi awaya,kuma har sau biyu yaje garinsu Ibadan.Haka dai ya haqura tare da xubawa sarautar Allah ido don yayi yayi da Faruq ya kara aure amma yace shi sam bayada ra'ayin ajje mace fiye da daya.
Sai bayan shekaru biyu Najmiy ta samu wani cikin,wannan karon ta haifeshi lafiya qalau,Hayat ji yayi tamkar ya xuba ruwa akasa yasha don murnar wannan haihuwar,kai kace ko shi akai wa haihuwar don yadda ya kasa tsaye haka kuma ya kasa zaune,abin ma har mamaki yaketa baiwa sauran yan'uwansa,aganinsu qaunar d'an yake ba tare da sanin cewa yana da wani mugun nufi akasan ranshi akan yaron ba.
Najmiy ta roki alfarman asanyawa yaro sunan dan'uwanta daya bata kuma bataso asakaye sunan wato *'ARYAAN'* sunan da yaro yaci kenan.Aryaan ya taso cikin so da kuma kulawar iyayensa,kakarsa Haj.Babba da kuma anties nasa,Abida 'ya'yanta biyu ayanxu,hidaya ma tana da 'ya.Hayat sai ya dunga nan da nan da yaron,shima Aryaan ya saba dαshi don duk wani motsi ídαn чαji zakaji yace"Uncle ne?".
Wata rana Maryam ta tashi da wani irin matsanancin ciwon ciki wanda har saida aka kaita asibiti,iya binciken likita an gano cewa muguwar sha'awa ce ta taru tayi mata yawa,ya kira Hayat office ya gargadesa akan ya dunga kula da buqatunta don ciwon sha'awa nada illa sosai,toh tun asannan ya danji tausayinta ya soma hada shimfida da ita ba don yaso ba,kota gamsu ko bata gamsu ba dagawa yake abinsa ya kyaleta,Aryaan nada shekaru uku aduniya Maryam ta haifi 'yarta kyakkyawa mai kama da ubanta Hayat,ranar suna akayiwa Haj.Babba kara aka sanyawa yarinya sunanta wato *'KHADEEJAH'*,za ana kiranta da *'ILHAM'*.
Akwai wani aminin Mai martaba Umar Faruq mai suna *'DR.ABUBAKAR SADIQ BATURE'* (kun tunashi ah first page?likitan Aryaan).
Aminai ne sosai,tare sukai karatu ah Udus,ah inda Faruq ya karanci *'POLITICAL SCIENCE'* shi kuma Bature kamar yadda ake kiransa sabida mamarsa baturiyace,da baban zai aureta sai ta musulunta,toh shi baturen ya karanci *'MEDICINE'* ne,bayan ya hada degree dinsa sai iyayensa suka turashi masters ah qasar india,toh bayan ya kare sai babban asibitin india suka rikeshi don ya kasance mai gwazo da kokari,ya zama shahararran likitan kwakwalwa ah inda kasashe daban daban har gayyatarsa yin surgery suke.
Dakyar yazo ya dawo Nigeria ya auri wata Nabila wacce dama akwai alqawarin aure atsakaninsu,koda ya aureta ya ijjeta gaban iyayensa ne yace daga baya idan komai yayi masa daidai zai taho ya dauketa xuwa India da zama.bayan watanni uku uku yake squeezing lokaci yazo yaga gida,yakan yi musu a week kafin ya koma,Allah yazo ya azurta Nabila da haihuwar twins mace da namiji (My dream😀). *'NADEEM'* da *'NADEEMAH'*, shekara daya kacal Aryaan ya basu.
Akan kai twins gidansu Mai martaba don sada xumunci,haka zalika akan kai shi Aryaan din gidansu suma,wata irin muguwar shaquwace ta shiga tsakanin yaran musamman Aryaan da Nadeemah.Aryaan nada shekaru biyar Najmiy ta sake haihuwar 'ya mace wacce taci sunan Haj.Karama wato *'MAYMUNERH'* sai suna kiranta da *'ZAITON'*,ba Aryaan kadai aka haifawa wannan 'yar ba hatta su twins da kuma Ilham sunyi farin ciki sosai,acewarsu sun sami qanwa don suma twins mamarsu bata sake haihuwa ba bayan su,haka ma Maryam shiru kake ji tun bayan haihuwar Ilham.
Acikin wannan lokacin ne kuma Dr.Bature ya dawo ya dauke iyalinsa suka koma qasar india inda yake aiki,Aryaan da Nadeemah har zazzabi sukai na rabuwa da juna.Tunda suka wuce sau daya sukazo ganin gida.
Bayan shekara daya,Aryaan ya soma experiencing some strange symptoms atare dashi,abin takai har suma yakanyi,awannan lokacin kuma su Dr.Bature suka sake xuwa ganin gida shine Mai martaba ya labarta masa lalurar Aryaan,bayan wasu yan gwaje-gwaje ya tabbatar musu da cewa ya kamu ne da cutar *'MEDULLOBLASTOMA CANCEROUS BRAIN TUMOR'*,yace dole za'a fita dashi waje aje ayi masa surgery.ba tare da wani b'ata lokaci ba aka fita dashi xuwa qasar India.
Anyi aiki cikin nasara,amma wani abin mamaki aduk lokacin da yayi yunkurin dawowa cikin rayuwa sai wani gagarumin shock from no where yakai masa attack ah kwakwalwa kuma iya binciken likitocin sun kasa gano wannan shock din,kamfutocinsu sai nuna musu suke *'NOT DETECTED'* harna tsawon shekara daya babu magana mai dadi.
Wannan kuwa aikin Hayat ne,akwai wata bayerabiya wacce Roughcoin ya amsowa Hayat wani abu haka da already an riga anyi programming dinsa,wani babyn roba ne karami mai suffar mutum sak!,toh aduk lokacin da Aryaan yayi yunkurin dawowa cikin rayuwa sai kaga Hayat ya dauki wannan babyn robar ya shiga caccaka mata allura aka,toh allurar nan da ake caccakawa wannan babyn shine ya zamo shock din dake kaiwa Aryaan attack,zakaji Hayat yana kuka yana fadin"Dana kayi haquri iyayenka ne suka jawo maka,na tabbata yanxu Faruq da Najmiy suna matukar jin radadi da kuma zafin halin da kake ciki,kadan kenan daga cikin irin abinda ni nake ji agame da mamarka..... "
Xuwan Hayat sau biyar India tunda Aryaan ya kwanta rashin lafiya,agidan Dr.Bature su mai martaba suka sauka,lokaci xuwa lokaci mai martaba yake xuwa ganin gida sabida mutanensa.
Ayau kuma Haj.Babba itama lokaci yayi,kwananta ya kare aduniya,ciwon siga ya zamo ajalinta shine mai martaba ke kokarin komawa gida kamar yadda kuka gani ah first page.Sai ya bar Najmiy donta tsaya da Aryaan.
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_*Masha Allah am xoxo happy da yau muka kawo karshen wannan tuna baya din,yanxu sai mu koma kan ainihin labarin *_
_*ku biyoni don jin tsintuwar da mai martaba umar Faruq zai yi🏃,amma kafin nan bari mu hanzarta mu dubo wani ƙauye mai suna 'TEWI' wanda ke cikin garin minna*_
_*Masu son Hayat yanxu ina fatar zaku dan rage 😂*_
_*Abinda kuma nakeson ku gane shine,ciwon brain tumor ba Hayat ne ya haddasa masa ba,ciwonsa daga Allah ne,nashi dai wannan shock dinne yake bashi.*_
*íntєrmíѕѕíσn (tѕαkíчαr lαвαrí)💘💘*
*tαku*
*mσm híввαh💕* ❄️❄️❄️❄️❄️ *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤* ❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°•ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑•°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/ __________________________________ 💥
*NOT EDITED*
*Թɑցҽ 23-25*
_________*'TEWI'* wani dan karamin ƙauye ne dake ƙarkashin *'BOSSO lOCAL GOVERNMENT'* wanda ke ah jihar *'MINNA'* .Tewi ƙauye ne sosai wanda wutar lantarki ta Nepa ma basu dashi,ƙauye ne wanda beyi wani suna ba sabida Karancin mutanen ciki,mutanen wannan kauyen ko dari shidda basu kai ba,Allah ya albarqaci ƙauyen Tewi da kasar noma,shukunansu nan da nan suke girma,hakanan zaka gan ganyayyakin fresh dasu abin gwanin ban sha'awa dai.Yaren da akafi yi shine *'GWARANCI'* kasancewarsu gwarawa.Sunan mai unguwar wannan ƙauyen *'MAL.MUHAMMADU NAZIRU'*.Shugaba ne mai kirkin gaske da kuma taimako saidai kuma beyi sa'an matan aure ba.
*°•GIDAN MAL.MUHAMMADU NASIRU•°*
Uwale wacce ta kasance amaryar Mal.Muhammadu ce ta bada himma wajen dakar dawa dake acikin wani katoton turmi ayayin da uwargida ran gida mai mulki wato Mariya take zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e wanda Uwale ta riga ta daka,sai taga yayi lukwi dashi kafin ta juye awani kafcecen kwano mai dan zurfi da kuma fadi.
Can Uwale ta dakata tare da sanya hannu daya ta rike ƙwanƙwasonta,dayan kuma rike da tabarya,yamutsa fuska tayi wanda ya nuna alamun gajiya atattare da ita.
Mariya ta dago kai ta kalleta jin tayi shiru da dakar,ganin yanayinta yasa ta dan murmusa tace"Yadai Uwale kin gaji koh?"
Uwale tace"washhh! Yayah Mariya wallahi ƙwanƙwasona kamar zai karye,Allah na gaji don Allah zoki karashe ni kuma na cigaba da tankad'en ko kuma aƙira Fulani ta ƙarashe......"
Saurin dafe ƙirji Mariya tayi,cikin daga murya tace"Wah zai kira Fulani anan?ke tunda ma ta soma yoyon fitsarinta kin sake ganin na bata aiki ta min?Ni Mariya bazan ci kazanta ma don haka ni bani tabarya na karashe idan da gaske kin gajin ne...." Ta mike ta kwace tabaryar ahannun Uwale wacce tunda Mariya ta soma maganarta take ta tikar dariya son ranta.
Tace"Kai Yayah baki da sauki in har akan Fulani ce...."
Ko kala Mariya bata ce mata ba illa maida hankali da tayi akan dakarta.Jan jiki tayi xuwa ga kujerar da Mariyar ta tashi,ta cigaba da tankad'en.
Fulani kuwa dake can dakinta taji duka hirarsu akanta,wani hawaye masu dumi suka gangaro mata saman kunci,da sauri ta sanya bayan hannunta ta daukesu,cikin rawar murya ta daga hannunta sama tace"Yah Allah! na rokeka ka kubutar dani daga hannun wa'ennan azzaluman matan,nasan da nawa laifin aciki amma Yah Allah ka karkato da hankalin Muhammadu gareni ya maidani gaban iyayena...." Kuka yaci ƙarfinta,takai hannu tana shafa fuskar 'yar 3days old baby dinta,ahankali tace"'Yata don Allah ki yafemin don duk nice silar shigowarki cikin wannan kuncin rayuwar,baki san komai ba amma har kin soma dandanar dacin rayuwa....."
'Yar kuwa kamar taji abinda uwar ke fada don wani uban ihun jirajirai ta fasa abin gwanin ban tausayi,da sauri Fulani takai hannu ta ciccib'ota ta mannata saman kirjinta,kana ta shiga jijjigata alamun rarrashi,tana kuka itama Fulanin tana yi.
Mariya taji koke-kokensu na shigar mata kunnuwa,abin ya soma isarta don haka ta jefar da tabarya kana ta nufi dakin Fulani tana masifa"Wai Fulani wannan wani irin iskancin banza ne haka zaku bi ku dami mutane da koke-koken iskanci daga ke har shegiyar aljanar 'yarki?iyyeh magana nake miki?"
Ta daga labulen dakin ta hango Fulani ta sanyawa 'yarta nono abaki,ita kuwa 'yar ta hau tsotsa da sauri da sauri don dama yunwa takeji sosai.
Ahankali Fulani tace"Yayah don Allah kiyi haquri tayi shiru ma...."
Dariyar sheƙiyanci Mariya ta sakar,sai datayi mai isarta kana ta daure fuska tace"Malam na dawowa wallahi zaki bar gidan nan,zaman dadironcin ya isa hakanan,gashi har nema kike ki shafa mana muguwar cuta,toh wallahi yau zaki bar gidan nan kinji dai na gaya miki,Allah na tuba ma waya sani ko ke karuwarsa ce bamu sani ba yake mana karya wai taimakonki yayi?"
"A'uzubillahi! A'uzubillah!!! Ni Aishatu ba dadiron kowa bace,sannan kuma 'yar nan tawa ta hanyar raya sunnar ma'aiki na sameta,kaddarace kawai ta rab'ani da mahaifinta,sannan kuma labarin da Malam ya baku ku yadda dani labarin gaskiyace bawai ƙarya ya shimfid'a muku ba.... " ta rushe da kuka,mutumin kirki ne kadai zai iya yadda da cewa iya gaskiyarta ne ta fada,amma mace jahila kamar Mariya ai tayi nisa ah iya kulla makirci iri-iri hadda na siyarwa kuwa.
Kallon uku saura kwata Mariya ta mata kana tace"Ammah malam ce mana yayi kamaki akai da kwarto kuna aikata sab'on Allah adakinki sannan kuma akan gadon aurenki....."
Gaban Fulani ya bada rass!!!! don bata tab'a zato ko tunanin cewa har akwai ranar da Mal.Muhammadu zai iya fallasa sirrinta ga maƙiran matansa ba.koda yake ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin yadda ya sauya mata lokaci guda kuma duk makircin matarsa Mariya ce.
Cikin rawar murya tace"Shi....malaaam.... din...shine....ya...gaya muku hakan?"
"Yayah Mariya nifa naga kokarinki na tsayawa kina tanka maganarta wai ke bakya jin doyi da kuma zarni ne?" Uwale ce tayi wannan maganar daga inda take zaune.
Don iskanci sai gashi Mariya ta sanya hannu tana toshe hancinta wai nan ita zarnin take ji.Ta saki labulen ba tare da ta baiwa Fulani amsar tambayarta ba.Ta nufi inda Uwale take ta mata rad'a akunne,Uwale ta saki sowa da murna tace"Kai Yayah kin kawo shawara mai ƙyau,ai kuwa yana dawowa mu tasashi agaba ya korar mana ita...."
Daga haka suka cigaba da gulmar Fulani suna kyakyatar dariya,suna yi suna aikinsu har suka gaba.
Ita kuwa baiwar Allah Fulani kuka taci sosai da maganganun da Mariya ta sossoka mata,daga baya ta share hawayenta.
***
Bayan awa daya da rabi ta dauki 'yarta ta fito waje don yin wanka dake yanxu lokacin wankanta kenan idan rana tayi sanyi.Sau daya take samu tayi wanka arana tunda ta haihu.Tana fitowa su Mariya suka bita da kallon tsana,taje zata dauki bokitin Mariya,da sauri tace"Karki kuskura ki daukar min bokiti...."
"Nima haka karki daukar min tawa idan ba haka ba ubanki zanci..." acewar Uwale wacce take bakin murhu take tuka tuwon dare,ita kuwa Mariya alayyahu take yankawa.
Fulani ta rasa yadda zatayi don tun jiya bokitinta ya fashe,bata tsaya rokansu ba don tasan ko tana shure-shuren mutuwa ne ba ara mata zasuyi ba,ta aiki almajirin dake musu aikatau xuwa makobta aro mata bokitin awajen wata wacce suke dan shiri da ita.Can sai gashi ya dawo dashi ya mika mata"Wai tace ki basshi ta baki kyauta..."
Dan murmusawa tayi tace"Allah sarki Uwani je kace mata nagode..."
"Toh" shine abinda al'majirin ya fada kana ya fice da gudu,ita kuma taje ta cika ruwa abokiti daga rijiya takai bandaki,su Mariya sai toshe toshen hanci suke tayi,kuma duk tana lure dasu amma sai ta danne ta baiwa banza ajiyarsu.Ta dauki 'yarta data kwantar akan tabarma sukaje sukayi wankansu don duk ita take wankan jegonta babu mai taimakonta,ranar farko Uwani ce tazo ta mata,kuma aranar malam ya tsawatar mata akan karta kuma zuwa duk kuma makircin su Mariya ne,ita kuwa Fulani duk taga yadda Uwanin tayi mata shiyasa ta dan iya wankan,sai ta soma yiwa 'yar wanka sannan takai daki ta kwantar da ita,kana ta koma bandaki tayi nata da sauri da sauri don bata yadda dasu Mariya ba,suna iya iya 'yar wani mugun abu.
*WACECE AISHATU FULANI?*
Aishatu wacce akafi sani da Fulani haifaffen kauyen wudil ne dake ah jihar kano,fulanin usuli ne,mahaifinta Aminu Muntari malami ne sosai don har almajirai yana dasu,akofar gidan yake tarasu ya koyar dasu karatu,matarsa daya mai suna Furera,sannan 'ya'yansu hudu,uku maza sai kuma Fulani wacce ta kasance auta kuma 'ya mace tilo agun iyayenta,Fulani ta taso cikin so kulawa,da kuma gata daga gun iyayenta da kuma yayunta,gata mace ce fara tas da ita mai masifar kyau wacce maza har rushing suke akanta amma itafa mutum daya takeso kuma shine wani mai suna Alu wato Aliyu.Alu kuwa irin yan iskan samarin kauyen nan ne don har fyad'e yakewa yan mata kuma babu wanda ya isa ya tunkareshi kasancewar mahaifinsa yana cikin mutanen da ake tsananin tsoro awannan kauyen.Ita kuwa Fulani bata damu da halayyarsa ba tace itafa shi takeso.Mahaifinta kuma yace bata isa ta b'ata masa suna agari ba,alokacin da ta cika shekaru goma sha tara Mal.Aminu ya hadata aure da daya daga cikin manya-manyan almajiransa wanda ake kira da *'DAN MALAM'* kasancewarsa na hannun damar Mal.Aminu ne.
Dan malam yayi murna sosai da wannan kyautar da Malaminsa yayi masa don dama can ya jima yana fama sa soyayyar Fulani acikin xuciyarsa kawai yadai gagara gaya mata ne ganin ita dai Alu takeso.Bayan auransu Alu ya shiga gwada mata qauna da kuma bata kulawa daidai gwargwado amma ita kuwa rashin mutuncin yau daban haka kuma na gobe daban,sau daya suka tab'a hada shimfid'a shima din cewa tayi kaddarace.Fulani zata haqura amma ina ta kasa cire Alu aranta,ita dashi suka hada plan akan cewa yazo gidanta ya zauna adakin auranta,watakila dan malam na ganinshi zaice kwartonci yazo yi sannan kuma ya sauwake mata,bayan ya sawwake mata sai su gudu.
Sosai Alu yayi na'am da wannan shawarar data kawo masa ranar da suka hade awani wuri asirrance.Ai kuwa ranar da Dan Malam ya fita,sai ga Alu yazo,kuma harga Allah babu abinda ya shiga tsakaninsu,sai akayi rashin sa'a da Dan Malam ya tashi dawowa sai suka taho had'e da sirikinsa wato Mal.Aminu.
Mal.Aminu har kuka yayi da ganin wannan abin kunyar da 'yarsa ta jawo masa agidan auranta,shi kuwa Dan Malam jikinsa ne yayi sanyi qalau harma ya kasa furta komai,kafin sukai ga daukar wani mataki Alu ya tsere,kuma garin ya bari gabaki daya.Malam ya zane Fulani sosai kuma yace dolene Dan Malam ya sawwake mata,dan malam kuma yace shi bazai iya ba ayi haquri yana son matarsa ahakan.Babu yadda suka iya illa barinsa da matar tasa,ita kuwa Fulani taci kuka sosai sanda taji labarin wai an nemi Alu an rasa, bayan watanni biyar saiga ciki ya bullo ajikinta,mahaifinta yace wannan cikin bana Dan malam bane,shima Dan malam ya soma zarginta don tunda sukayi aure sau daya ya kusanceta,sai yayi tunanin kila cikin na Alun ne.
Malam ya matsa masa akan dole saiya saketa kuma saita bar kauyen don bazai bari ta janyo masa abin fada ba agarin.Babu yadda dan malam ya iya illa sawwake matan sabida mutane suna ganin cikin za'ace ai cikin Alu ne.
Babu irin rokan da fulani batayi ba akan mahaifinta yayi haquri karya koreta amma fir! yaki.Yayunta da mamanta ma sukace babu ruwansu da ita ta tafi can ta karata da shegen danta.Bata da kalmar da zata kare kanta dashi don an riga an kama Alu adakinta,don haka komai zata fada akan babu abinda ya shiga tsakaninsu ba yadda zasuyi ba,amma harga Allah cikin jikinta na Dan malam ne.
Haka ta baro kauyen tana kuka,Mal.Muhammadu sarkin taimako alokacin yazo siyen sa ne akauyen,sai yaga yadda take kuka tana tafiya,kiranta yayi ya tambayeta abinda ke damunta ta gaya masa,yace ta masa jagora xuwa gidansu,bayan sunce yayi roko amma fir! Mal.Aminu yace bazai karbeta ba.
Haka dai suka baro gidan rai ba dadi,mal.Muhammadu yace"Toh yarinya idan zaki iya bina garinmu har xuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya asannan kuma mahaifinki ya huce sai mu dawo toh bismillah muje...."
"Ni kowani gari ne muje idan har kana da mata wacce zan zauna agunta...." Fulani ta fada tana mai kuka.
Murmushi yayi yace"Matana biyu saidai babu wacce ta taba haihuwa...." Fulani duk ta rasa abinyi shiyasa kawai ta yanke shawara ta bishi minna.
Acan kuwa rigimace babba ta kaure tsakaninsa da matansa musamman da suka ga Fulani dauke da ciki,sai suke ganin kamar karuwarsa ce,kila cikin da tayi ne yasa aka koreta daga gida shi kuma ya rasa abinyi shiyasa ya kawota nan. Kan kuce meye wannan har magana ya bazu agari cewa ai mai unguwa ya kawo karuwarsa ga iyalinsa.
Shi kuwa ya nuna ikonsa akansu,ya nuna musu cewa ya isa da gidansa,ya baiwa Fulani dakin da zata zauna ta reni cikinta harta haihu.Ya sayo mata wasu en kayaччαkí na amfaninta ya xuba adakin.
_*чαnzu wαccє írín zαmα nє fulαní tαчí αgídαn?*_
_*чα αkαчí mαl.muhαmmαdu чα cαnzα mαtα dαgα вαчα?*_
_*ѕαnnαn kumα чα αkαчí tα kαmu dα cutαr чσчσn fítѕαrí (fíѕtulα)?*_
_*ínα kumα lαвαrín tαfíчαr mαí mαrtαвα umαr fαruwα?*_
*ku вíчσ hαfnαn*